BUK ta ƙaddamar da Sabuwar Manhajar Duba Sakamako Jarabawa
Published: 1st, April 2025 GMT
Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta kaddamar da wani tsari na yanar gizo wanda zai baiwa dalibai damar shiga da duba sakamakon kammala karatunsu ta hanyar lambobi.
Wannan sabon yunkuri shine karo na farko da cibiyar ta samar da sakamako ta hanyar irin wannan dandali.
An sanar da shirin ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakin magatakarda kuma shugaban hukumar kula da harkokin jama’a Lamara Garba Azare.
A cewar sanarwar jami’ar, tsarin da myBUK Team ya kirkira kuma yana bawa ɗalibai damar dawo da sakamako kai tsaye ta hanyar amfani da sashen rajistar dalibai.
Takardun sakamakon za su nuna a sarari na kowane kwasa amma dole ne ɗaliban da suka kammala shekarar ƙarshe su jira amincewar Majalisar Dattawa kafin su sami sakamakonsu.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar dalibai a Jami’ar, Bilal Muhammad Bello, ya yabawa ci gaban da aka dade ana jira tare da bada tabbacin cewa wannan zai rage damuwar dalibai da kuma kawar da jinkiri da aka samu wajen samun sakamakon.”
“Wannan tsarin yana ba ɗalibai damar sanya ido kan ci gaban karatun su tare da kawar da cunkoson da ake samu na jama’a a a allon manna sakamakon jarabawa.”
Da yake tsokaci kan zaman sa a matsayin Sanata na 24 na SUG mai wakiltar Sashen Sadarwa, Bello ya ce. “Na ba da shawarar samun damar samun sakamako ta yanar gizo a lokacin da nake majalisar dalibai, Alhamdulillah, wannan hangen nesa ya zama gaskiya.”
KHADIJAH ALIYU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250 a Jami’ar Ilorin
Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.
An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar samun kuɗin kula da masallacin.
Ana sa ran kuɗaɗen haya da za a samu daga ɗaliban da za su zauna a wurin zai rika shiga asusun kula da masallacin.
Sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya shaida wa manema labarai a Ilorin cewa Ɗangote ya riga ya sanar da su cewa zai ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.
Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar RuwaYa ce an riga an rattaba hannu kan yarjejeniya da Jami’ar Ilorin wadda ta ba wa masallacin damar mallaka da gudanar da ɗakin kwanan ɗaliban na tsawon shekaru 21 kafin a miƙa shi ga jami’ar.
Baya ga aikin ginin, Ɗangote ya kuma yi alƙawarin bayar da tallafin Naira miliyan 5 a kowane wata domin kula da masallacin har sai an kammala aikin.
AbdulGafar ya ce wannan taimako zai rage nauyin kuɗin aikin, tare da tabbatar da ɗorewar ayyukan masallacin.
Ya ƙara da cewa ɗakin kwanan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin wurin kwana ga ɗaliban jami’ar.
Shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki sun yaba wa Ɗangote, sun bayyana wannan mataki a matsayin abin koyi na yadda za a iya haɗa kai tsakanin cibiyoyin addini da ’yan kasuwa wajen ci-gaban al’umma.