Aminiya:
2025-07-31@12:34:13 GMT

’Yan bindiga sun hallaka matashi ana sallar Tahajjud a Kaduna

Published: 22nd, March 2025 GMT

Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun kai hari wani masallaci da ke yankin Tudun Wada a Jihar Kaduna, inda suka kashe wani matashi yayin da ake tsaka da sallar Tahajjud.

Sai dai rundunar ’yan sandan jihar, sun kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kai hari masallacin da ke Tudun Wada a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu.

Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia An wawushe motar abinci ta Hukumar WFP a Borno

Kakakin rundunar, Mansir Hassan, ya ce maharan sun fito daga wurare daban-daban kamar Malalin Gabas, Tudun Wada, Rafin Guza, da Unguwar Baduko.

Sun kai farmaki Masallacin Layin Bilya, titin Makwa a Rigasa da misalin ƙarfe 2 na dare yayin da masu mutane ke sallar Tahajjud.

Kafin jami’an tsaro su isa wajen, maharan sun sun daɓa wa wani matashi mai shekara 28, Usman Mohammed, wuƙa har lahira.

Rundunar tare da haɗin gwiwar JTF sun ɗauki mataki cikin gaggawa, inda suka kama mutum 12 kuma ana bincike a kansu.

Haka kuma, an samu makamai a hannu waɗanda aka kama.

An fara bincike domin gano gaskiyar lamarin da tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata laifin.

Sakamakon haka, ’yan sanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a wuraren ibada da sauran wuraren da ake ganin za su iya fuskantar barazana.

Hukumomi sun buƙaci al’umma da su kasance masu sanya ido tare da gaggauta kai rahoto idan sun ga wani abun zargi.

’Yan sanda sun kuma gargaɗi ’yan ta’adda da su daina aikata laifuka ko su fuskanci hukunci mai tsanani.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hari Sallar Tahajjud Tudun Wada

এছাড়াও পড়ুন:

Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina

Sama da mutum 5,000 ne suka tsere daga gidajensu a Jihar Katsina, sakamakon sabbin hare-haren da ’yan bindiga suka kai a Ƙananan Hukumomin Bakori da Faskari.

Mutane daga ƙauyuka sama da 10 sun nemi mafaka a garin Bakori, inda da dama ke zaune wajen ’yan uwansu, yayin da wasu ke kwana a waje ba tare da masauki ko abinci ba.

Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga Tallafin matar Tinubu na N1bn ga ’yan gudun hijirar Binuwai ya bar baya da kura

Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun bayyana cewa, maharan sukan shiga ƙauyuka da yawa, inda suka dinga harbi, ƙone gidaje, sannan suka sace mutane ciki har da mata da ƙananan yara.

Hare-haren sun fi muni a auyuka irin su Guga, Anguwar Danmarka, Gidan Sule, da sauransu.

Wani dattijo mai shekara’u 68 daga ƙauyen Doma ya ce sama da mutum 250 aka kashe a yankinsa cikin shekaru biyar da suka wuce.

Ya ƙara da cewa ’yan bindigar sukan ƙone rumbunan abinci tare da sace dabbobi.

Wata mata da ta kuɓuta daga harin a Anguwar Galadima ta ce iyalinta su 17 sun tsere, inda ta ce an sace sama da mutum 20 a ƙauyen nasu.

Wani saurayi daga Anguwar Dan Marka ya bayyana yadda aka harbe shi sau biyu a ƙafa, kuma yanzu yana amfani da sanda wajen yin tafiya.

Wasu da dama har yanzu suna hannun maharan, yayin da suke neman fansar Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum ɗaya.

Manoma ma na kuka da halin da suka tsinci kansu sakamakon hare-haren.

A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wani manomi daga Ƙaramar Hukumar Sabuwa ya koka da yadda aka lalata gonarsa.

Amma a martanin da suka bayar, shugabannin Ƙaramar Hukumar sun ce an lalata gonakin da ke kusa da manyan tituna ne domin hana ’yan bindiga amfani da su wajen ɓuya da kuma kai wa matafiya hari.

Amma manoman suna kallon wannan a matsayin wata matsala a gare su.

Shugabannin ƙauyuka da hukumomin gwamnati sun tabbatar da cewa mutane suna ƙara zuwa Bakori kowace rana don neman mafaka.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bakori, ya ce akwai sama da mutum 3,500 da ke zaune a Bakori, yayin da wasu sama da 2,000 ke zaune a ƙauyen Guga.

An fara raba wa waɗanda suka rasa matsugunansu abinci da kayan masarufi, amma ana buƙatar samum ƙarin taimako.

Ƙungiya ta buƙaci a ayyana dokar ta-ɓaci a Bakori

An buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da kuma ƙungiyoyin agaji su kai wa waɗanda lamarin ya shafa ɗauki cikin gaggawa.

Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna ‘Grassroots Advocates for Peace’ ta nemi Gwamnatin Tarayya ta ayyana Bakori a matsayin yanki mai hatsari.

Sun buƙaci ƙarin jami’an tsaro, da ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Sun kuma buƙaci a kula da lafiyar kwakwalwar waɗanda suka kuɓuta daga hare-haren da kuma hukunta masu kai hare-haren.

Gwamnatin Katsina na ƙoƙarin magance matsalar

A nata ɓangaren, Gwamnatin Jihar Katsina, ta ce tana ƙoƙarin wajen magance matsalar.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar, Nasir Muazu, ya ce suna ƙoƙarin magance matsalolin da Ƙaramar Hukumar ke fama da su.

Ya ce akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin yada ƙarya a kafafen sada zumunta don haifar da tsoro da ruɗani a zukatan jama’a.

Ya kuma ce an samu sauƙin kai hare-hare a wasu yankuna kamar Jibia da Batsari.

Kwamishinan, ya bayyana cewa an kafa rundunar ‘Katsina Community Watch Corps’ domin taimaka wa sojoji, ’yan sanda da ’yan sa-kai wajen shiga dazuka da ke da wuyar shiga.

Sai dai ya buƙaci jama’a da su ci gaba da jajircewa da kuma bayar da rahoton duk wani abu da su yarda da shi ba.

An samu sauƙin kai hare-hare cikin shekara 2 — Ribadu

A yayin da gwamnati ke cewa ana samun ci gaba, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce Najeriya ta fi samun zaman lafiya a yanzu sama da shekaru biyu da suka wuce.

Ya ce an ceto da mutum sama da 11,000 da aka sace, kuma an kashe wasu daga cikin manyan shugabannin ’yan bindiga.

Ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bisa jagoranci da tsare-tsaren tsaro da suka haifar da wannan sauyi.

Sai dai waɗanda ke zaune a matsuguni na wucin gadi a Bakori da wasu yankuna, rayuwa cikin tsaka mai wuya.

Wasu sun ce har yanzu ba su da ƙwarin gwiwar komawa gidajensu.

Sun tabbatar da cewar sai gwamnati ta samar da tsaro mai ɗorewa, sannan za su koma muhallansu, saɓanin haka za su ci gaba da zama a inda suke a yanzu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya
  • Kwamandan NDA Ya Bukaci Dalibai Su Dage da Karatu a Taron FGC Malali
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • ’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Matashi Ya Kashe Surukarsa Saboda Shigarta Cikin Sha’anin Aurensu
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri
  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
  • Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja