An Rantsar Da Sabuwar Shugabar Kasar Namibia
Published: 22nd, March 2025 GMT
A ranar Juma’a aka rantsar da sabuwar shugabar ƙasar Namibia, Netumbo Nandi-Ndaitwah domin jagorantar ƙasar wadda aka ruwaito na fuskantar ƙalubale na rashin aikin yi da talauci.
Kasancewar Netumbo Nandi-Ndaitwah mace ta biyu da aka taɓa zaɓa a matsayin shugabar ƙasa a nahiyar Afirka, kuma ta farko a Namibia na iya fuskantar ƙalubale.
“Idan komai ya tafi daidai, wannan zai zama kyakkyawan misali,” kamar yadda Netumbo Nandi Ndaitwah ta shaida wa shirin Podcast na BBC Africa. “Amma idan wani abu ya faru, kamar yadda zai iya faruwa ga kowace gwamnati ko da a ƙarƙashin namiji ne, akwai waɗanda za su ce: ‘saboda ni mace ce!’”
Sabuwar shugabar, mai shekara 72 a duniya ta lashe zaɓen qasar ne a watan Nuwamba inda ta lashe kashi 58% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Nandi-Ndaitwah ta kasance daɗaɗɗiyar ƴar jam’iyyar South West Africa People’s Organisation (Swapo) – wadda take kan mulki tun lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai a shekarar 1990, bayan kwashe tsawon lokaci tana fafutukar ƙwatar kanta daga Afirka ta Kudu mai fama da mulkin wariya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Nandi Ndaitwah
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda ta kaya a wasannin kusa da na ƙarshe na Gasar Zakarun Turai
A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana.
An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida.
DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a BornoPSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba.
Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0 a Emirates a cikin watan Oktoba.
Arsenal da Paris Saint-Germain da Inter Milan da Barcelona su ne kungiyoyin da 4 da suka kai matakin zagayen daf da karshe na gasar.
A wannan Larabar ce kuma za a yi karon batta tsakanin Inter Milan da Barcelona, bayan kimanin shekara 15 da aka yi makamancin wannan karawar daf da karshe tsakanin ƙungiyoyin biyu a Gasar Zakarun Turai.
Inter Milan ce ta kai zagayen ƙarshe a 2010, sai dai wannan karon Barcelona na fatan lashe kofin bana da zarar ta fuskanci Arsenal ko Paris St Germain a watan gobe.
Sai dai, Barca da Inter sun fuskanci juna a gasar ta zakarun Turai a 2022/23, inda ta Italiya ta yi nasara 1-0 cikin Oktoban 2022 a wasa na biyu suka tashi 3-3 a Sifaniya.
Wannan shi ne karon farko da Barcelona ke fatan kai wa karawar ƙarshe a Champions League, tun bayan da ta lashe na biyar jimilla a 2015.