Jakadan dindindin na kasar Sin dake ofishin MDD a birnin Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa a kasar Switzerland, Chen Xu, ya gabatar da jawabi a madadin kungiyar abokantaka ta inganta hakkin bil’adama, da tattaunawa da hadin gwiwa da sauransu, yayin taron MDD karo na 58 da ya gudana a jiya Alhamis.

 

A cikin jawabinsa, jakada Chen ya bayyana damuwa game da mummunan tasirin da ra’ayin nuna bangaranci ya kawo, tare da tabbatar da bukatar aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Kazalika ya kamata a bi ka’idojin adalci, da gaskiya da kaucewa wariya a kwamitin kare hakkin bil’adama, ta yadda kare hakkin bil’adama zai gudana ta hanyar tsaro, da inganta hakkin bil’adama ta hanyar ci gaba, da kuma bunkasa hakkin bil’adama ta hanyar hadin gwiwa.

Dangote Zai Gina Sabuwar Masana’antar Siminti A Jihar Ogun Kasar Sin Ta Bayar Da Rijiyoyin Burtsasai 66 Ga Al’ummomin Zimbabwe Dake Fama Da Karancin Ruwa

Jawabin nasa ya kunshi shawarwari guda uku na inganta ci gaban ayyukan kare hakkin bil’adama na duniya, inda da farko ya bukaci a tabbatar da gaskiya da adalci, sai na biyu dagewa wajen bude kofa, kana na uku shi ne tsayawa tsayin daka wajen samun nasara tare ta hadin gwiwa.

Bugu da kari, jawabin ya samu goyon bayan kasashe sama da 20, da suka hada da Rasha, da Cuba, da Eritrea da kuma Singapore, kuma kasashe masu tasowa sun yi tsokaci sosai a kan sa. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Riza’i: Babu Hannun  Waje A Cikin Hatsarin Da Ya Faru A Tashar Ruwa Ta Shahid Raja’i

Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki.

Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.”

 A ranar Asabar da ta gabata ne dai wasu abubuwa su ka fashe a tashar ruwa ta Shahid Raja’i dake Bandar Abbas a kudancin Iran, wanda ya haddasa asarar rayuka da kuma jikkatar daruruwan mutane.

An bude kwamitin bincike domin gano hakikanin abinda ya faru a tashar da kuma haddas fashewar abubuwan masu karfi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Ta ƙaddamar Da Sabon Shafin Intanet Don Inganta Sayayya A Tsakanin Ma’aikatunta 
  • Iran ta sha alwashin ci gaba da aiwatar da manufofinta na raya dangantakarta da Nijar
  • Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja
  • Saudiya Ta Yi Allawadai Da Kissan Kiyashin Da HKI Take Yi A Gaza A Gaban Kutun ICJ
  • Riza’i: Babu Hannun  Waje A Cikin Hatsarin Da Ya Faru A Tashar Ruwa Ta Shahid Raja’i
  • Rashin tsaro: Gwamnan AbdulRahman Ya Gana Da Sarakuna Masu Daraja Ta Daya A Jihar Kwara 
  • Kungiyar Amnesty International Ta Kafa Hujja Kan Ta’asar’Yan Sahayoniyya A Gaza
  • Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Binciken Yawaitar Haɗurran Tankokin Man Fetur A Nijeriya 
  • Gwamnatin Yobe Na Ƙoƙarin Inganta Tsaro – Hon. Idi Gubana
  • Shugaban Kungiyar Hizbullah Ya Abbaci Abubuwa 3 Wadanda Yakamata Kasar Ta Maida Hankali A Kansu