Abin da ya sa nake jin daɗin yadda Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa — Buhari
Published: 29th, March 2025 GMT
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana jin daɗin yadda shugaban ƙasar Bola Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa.
Buhari ya ce har yanzu Tinubu bai sauya ba daga tsari da manufofin da jam’iyyar APC ta kafa wanda har ya sanya shi kansa ’yan Nijeriya suka zaɓe shi a 2015.
An ga watan Sallah a Saudiyya Dalilin da Aminu Bayero ba zai iya jagorantar hawan Sallah ba — KurawaBuhari ya bayyana hakan a saƙonsa na taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, wanda ya cika shekaru 73 a doron ƙasa.
Sanarwar da mai magana da yawun Buhari, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ta ce tsohon shugaban yana alfahari da alaƙarsa da shugaban ƙasar na yanzu.
Sanarwar ta ce Buhari da Tinubu sun gana ta wayar tarho a ranar Juma’a, inda a ciki Buhari ya yi Tinubu addu’ar tsawon rai da ingantacciyar lafiya da, sannan ya yi masa fatan samun nasarar a mulkinsa.
“Idan muka yi wa shugabanninmu addu’a, muna yi wa kanmu ne. Ƙasarmu na buƙatar addu’o’inmu,” in ji Buhari a ganawarsa da Tinubu.
Buhari ya ce shi da iyalansa suna godiya ga Tinubu da sauran jagororin jam’iyyar bisa ƙoƙarin da suka yi wajen kafa jam’iyyar APC, inda har ya samu nasarar zama shugaban ƙasa har sau biyu, bayan ya sha gwadawa a baya ba tare da samun nasara ba.
“Lokacin da ’yan Nijeriya suka zaɓi APC a 2023, zaɓi suka yi domin kafa tubalin sabuwar Nijeriya inda talakawa za su samu damarmakin da suke buƙata, kuma ina jin daɗi har yanzu ba a kauce daga tsarin ba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Muhammadu Buhari
এছাড়াও পড়ুন:
ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar.
Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna.
Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a BornoDa yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na ilimi, noma, kiwon lafiya, kasuwanci, da samar da ababen more rayuwa.
“Babu wani sashe a jihar da aka bari a baya a cikin ayyukan ci gaban da Gwamna Mai Mala Buni ke aiwatarwa,” in ji Adamu.
A nasa martanin, Gwamna Buni, wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Barde Gubana, ya wakilta, ya karɓi karramawar a matsayin “hanyar mayar da martani mai ƙarfi” da ke tabbatar da tasirin gwamnatinsa a matakin farko.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin kai Yobe matsayin jiha da za ta iya gogayya da takwarorinta a fagen ci gaban ƙasa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ’yan siyasa daga ciki da wajen jihar, da kuma sarakunan gargajiya.