Sin Da Laberiya Sun Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Ta Fuskar Tattalin Arziki Da Fasaha
Published: 29th, March 2025 GMT
Jakadan kasar Sin a kasar Laberiya Yin Chengwu da ministar harkokin wajen kasar Laberiya Sara Nyanti, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da fasaha, a madadin gwamnatocin kasashensu, jiya Juma’a a Monrovia, babban birnin kasar Laberiya.
Minista Nyanti ta godewa gwamnatin kasar Sin bisa gagarumin goyon bayan da take bai wa kasar Laberiya, ta kuma ce yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da fasaha da bangarorin biyu suka rattabawa hannu, za ta taimaka wa kasar Laberiya wajen cimma muradin raya kasa na ARREST.
A nasa bangare, Ambasada Yin Chengwu ya ce, rattaba hannu kan yarjejeniyar ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin aiwatar da alkawurran da aka dauka a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a shekarar 2024, da kuma gudanar da da manyan tsare-tsaren da shugabannin kasashen Sin da Laberiya suka tabbatar. Ya ce kasar Sin tana son aiwatar da yarjejeniyar tare da kasar Laberiya, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a kasar Laberiya hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun hada da kamfanonin kasuwanci guda biyar, hudu da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma a kasar Turkiyya, wadanda suka sayar da albarkatun man fetur na kasar Iran ga kasashe uku, da kuma wasu kamfanonin jigilar kayayyaki guda biyu.
A cikin sanarwar da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce “Matukar dai Iran na son samar da kudaden shiga na man fetur da sinadarai don samar da kudaden gudanar da ayyukanta na tabarbarewar zaman lafiya, da kungiyoyin da ya bayyana da na ta’addanci to Amurka za ta dauki matakin laftawa Iran da dukkan kawayenta alhakin kaucewa takunkumi.”
Matakin na zuwa ne jim kadan bayan Iran ta sanar da cewa za a sake gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da gwamnatin shugaba Donald Trump a birnin Rome a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a karkashin jagorancin kasra Oman.