Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone
Published: 30th, March 2025 GMT
Rahotanni sun ce, wani ɗan kasar China ya kama matarsa tana cin amanarsa da wanda ya ba ta aiki a lokutan aiki ta hanyar amfani da wata na’urar ɗaukar hoto ta jirgi mara matuƙi da ake sarrafa ta daga nesa, tana leƙen asiri daga nesa.
Mutumin mai hazaka da aka fi sani da Jing ya fara zargin cewa, matarsa na yin wata alaƙa ne bayan ta yi nisa sosai da shi kuma ta canza mu’amalarta sosai, ciki har da ziyartar iyayenta fiye da kowane lokaci da kuma kawo uzuri a duk lokacin da ya yi mata rakiya da kuma ƙarin lokaci a wurin aikinta.
Da yake kokawa kan batun, amma yana tsoron kada ya bayyana kansa ga matarsa idan har zarginsa bai tabbatar ba, Jing ya yanke shawarar yin amfani da na’urar ɗaukar hoto ta jirgi mara matuƙin na haya, don yi wa matarsa leƙen asiri daga nesa.
Yana tuƙa motarsa zuwa wurin aikinta sannan ya kunna jirgin mara matuƙi domin ya duba yankin ba tare da fargabar ganin matarsa ko abokan aikinta ba.
Wata rana yana lura da matarsa, sai ya hango ta fito daga ofishinta tare da wani mutum ta shiga mota da shi.
Sun yi tafiya zuwa wani wuri mai nisa a wajen wasu tsaunuka, inda jirgin mara matuki ya kama su suna rike da hannayensu, suna shiga cikin wani gida mara kyau.
Kusan mintuna 20 suna tare, daga nan sun bar gidan, sun koma wurin aikinsu.
Daga baya Jing ya shiga kafafen sada zumunta na zamani, inda ya bayar da rahoton cewa, mutumin da na’urar jirginsa mara matuki ya dauka a faifan bidiyo wanda da gaske ne ubangidan matarsa ne (wanda take yi wa aiki), kwanan nan ya yi mata karin girma.
“Mutumin da matar ke hulɗa dai shi, shi ne ya ɗauke ta aikin,” inda mijin ya rubuta a shafin sada zumunta na Weibo.
“Haka zalika yana aiki a masana’anta guda da matarsa, don haka bai yi musu dadi ba su ware wani wuri daban don yin alaka a can, saboda haka matata ta tilasta musu haduwa da shi a cikin daji.”
Jing ya kuma wallafa hotunan matarsa da masoyinta suna riƙe da hannayensu, ya kuma ce ya shirya yin amfani da bidiyon da na’urar ta ɗauka a matsayin shaida don neman raba aurensu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kwarto
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.