HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da Sallah
Published: 1st, April 2025 GMT
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar.
Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara.
Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sandaSai dai a sakamakon haramcin gudanar da haye-hayen sallah da rundunar ’yan sandan jihar ta yi, Sarkin bai cika duk tsare-tsaren da al’ada ta tanada ba na gudanar da Hawan Sallah.
Aminiya ta ruwaito cewa, Sarkin wanda ya yi ƙoƙarin kawar da idon jama’a, ya bi ta wasu hanyoyin da ba su aka saba bi wajen kai wa gwamna ziyara a yayin gudanar da hawa cikakke.
Haka kuma, Sarkin ya yi amfani da jerin gwanon motoci ƙalilan maimaiko hawa dawakai
Sai dai an tsananta tsaro a duk hanyoyin da Sarkin ya bi tun daga Fadar Sarki ta Gidan Ƙofar har zuwa Gidan Gwamnatin Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hawan Nasarawa Jihar Kano Sarki Sanusi II
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴansanda Sun Kama Ƴan Daba 33 A Kano
CP Bakori ya gode wa al’ummar Kano saboda goyon bayan da suke ba su a ƙoƙarin su na yaƙar masu aikata laifuka tare da kira ga ci gaba da haɗin kai wajen kai rahoton abubuwan da suke zargi ga Ƴansanda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp