Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara
Published: 1st, April 2025 GMT
Sanata Abdul’aziz Yari, mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana shirin tallafa wa marayu 20,000 a faɗin Jihar Zamfara.
Yayin da yake magana bayan cin abincin Sallah tare da marayu 500 a gidansa da ke Talata Mafara, Sanata Yari ya ce an shafe watanni tara ana tantance marayun daga ƙananan hukumomin jihar domin tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta ne za su amfana da shirin.
Ya bayyana cewa shirin tallafin wanda zai fara aiki kafin Idin Babbar Sallah, inda za a ware duk abin da marayun ke buƙata don kyautata rayuwarsu.
“Mun shirya wannan tallafi ne domin amfana da albarkar taimakon marayu, kamar yadda Alƙur’ani da Manzon Allah (SAW) suka hore mu,” in ji Sanata Yari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Marayu Sanata Yari Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, ɗaya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan ƙasar.
Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi — shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ke iya haifarwa a rayuwar talaka?
NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki” DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin ArewaA kan wannan sauyi da dalilansa ne shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan