Alfanu Da Rashin Alfanun Tallata Shirin Aure Tun Kafin Lokacin Ya Zo
Published: 1st, June 2025 GMT
Sam-sam hakan ba shi da wani alfanu domin yana kawo matsaloli da dama wanda babu lokacin lissafosu. Kalubalen da ka iya afkuwa kuwa shi ne; wadansu ‘yan matan ba sa tan-tance wadanda za su sa da wadanda ba za su saka ba, har da masu saka ‘yan’uwan miji, kawaye da ‘yan’uwa na cikin dangi duk a bi a cakuda su guri guda, kuma ba sa yin komai a lissafance ba sa tunanin a cikin yawan al’umman da ke ciki har da shaidani ciki ba, dan akwai wacce abu ya faru da ita daga bude group na biki (sabe the date) abu ya dawo babbar rigima har ta kai ga ‘police station’ kuma ba komai ya kawo hakan ba sai rarrabuwar ra’ayoyi daya ta zazzagi daya, ita ma dai wannan ya jawo mata babbar mastsala.
Sunana Hassana Tijjani Daga Gombe Najeriya:
Alfanun hakan shi ne yana hada kan juna a zama tsintsiya daya-madaurinki daya. Kuma hakan na nuna kulawa da nuna muhimmancin juna, kowa ya bada tashi gudmmawa da shawara aka ce “hannu da yawa maganin kazamar miya”, kuma a tsara biki mai kyau na gani na fada na bugawa a jarida. Tun da har kimiya da fasaha ta kawo wannan ci gaban me ya sa ba za ayi amani da shi ba Wadansu daga cikin ‘yan’uwa da abokan arzikin ba su da lokaci na samu a hadu guri guda don a tattauna don yanzu kowa ya kama sana’a in baka aikin ofis to, kana siye da siyarwa da haka a samu damar tattaunawa da mutum a duk nisan inda yake, don haka ba na ganin wa kalubale game da hakan, dan akan kanka ma in ka dubi bikin da dana yanzu kai ma ka san akwai babban bambanci. Shawarar da zan bawa su masu yin hakan su yi lokaci ne wataran ba nasu bane na ‘yan’yansu da jikokin sune. To ma idan ba a bude groups din ba ta wacce hanya a ke so a tsara bikin yadda zai tafi yadda ake bukata?, dan nasan akwai masu cewar hakan ka iya kawo rigima, ita ai ta san wanda ta kawo da inda ta nemo su dan haka kuwa duk abin da ya je ya dawo ita ce a ciki.
Sunana Hafsat Sa’eed Daga Naija:
Abin da na fahimta da bude group din da mata ke yi lokacin aurensu shi ne; suna saka masoyansu da ‘yan’uwa da abokan arziki, idan za a yi anko sai a saka ankon da account da duk wanda zai yi ankon ya tura kudin shi a hada wuri daya, in ba haka ba wasu ma ba lallai su sani ba. Ni dai a gare ni yin hakan yanada kyau saboda masoyanka ka tara kuma abun farin ciki ne, duk da cewa wasu na ganin idan mutum ya je ya yada yadda duniyar nan ta zama sai ya zamo matsala yanzu mutane boye aurensu suke yi sabida mugayen da za su kai ga sun raba aurenka. Kalubalen da ake iya samu wasu za sy iya kokarin ganin sun bata ka ko sun bata auren musamman idan aka san wanda za ka aura. Shawarar da zan bayar shi ne mutum ya zauna a yadda yake ya boye auren shi ya fi akan ya rika tallatawa gara a ji ranar daurin aure yadda zamani ya sauya.
Sunana Aisha T. Bello Daga Jihar Kaduna:
Wasu in suka bude group na kawaye ne wanda za su fadi komai na game da bikin ba sai an kira a waya ba suna gani ya fi sauki, gaskiya wasu da an saka su cikin group na kawaye amarya kalubale na farko shi ne turo da wani abu da bai shafi bikin ba da kayi magana kan haka sai abu ya zama fada. Shawara ta in har za ki bude group irin haka ya zama kawar amarya kawai ce za ta iya magana a cikin Allah ya sa mu dace.
Sunana Princess Fatima Mazadu:
Akwai amfanu gaskiya saboda za a yi ‘sharing idea’, sannan kuma za a samu daidaiton ra’ayi. Eh! akwai gaskiya saboda a wani lokacin har akan yi fada ko samun wasu kananun fitintinu, musamman bangare na mata, wadannan za su ga wanda aka yarda da zabinsu sune na gaban goshi wani lokaci gaba ma sai ta kullu. Shawara dai suna yi da taka tsamtsan saboda gujewa fitina da kananan maganganu.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya ni a ganina ba shi da wani amfani ko muhimmancin, domin hasali ma rashin kunya ne, domin kuwa a al’ada ta Hausawa mata suna da kunyar da ba za su iya fadar bikin su. Kwarai kuwa akwai kalubale, domin da farko rashin kunya ne, domin ita al’adar malam bahaushe akwai kunya don haka bai dace ba mace take fadar bikin ta. To shawara ta a nan ita ce; ya kamata gaskiya su daina domin rashin kunya ne, ita kuma kunya tana da matukar muhimmanci a rayuwar ‘ya mace domin ado ce, don haka duk lokacin da mace ta rasa kunya to ta rasa komai a ruyawar ta.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano Rano LGA:
Alfanun hakan zai kara tunasar da duk wanda wannan auren ya shafa domin ayi bikin cikin tsari. A nawa fahimtar babu wani kalubale sai dai ma ya kara bada damar duk wani shiri ayi shi cikin tsari da kuma magance biki ya zo ki ji ana cewa abu kaza da kaza ba a san da shi ba kuma gashi an riga da an makara. Su cigaba da hakan indai domin ayi bikin ciki tsari ne ba ma iya mata ba har da maza hakan zai kara kawo hadin kan al’umma, domin a irin wannan ne ake iya tsara kowa da irin duk wata rawa da mutane za su taka wajen gudanar da tsarin bikin ta inda koda za a yi abin da bai dace ba tun kafin lokacin za a kawo gyara Allah kasa mu dace.
Sunana Muktari Sabo Jahun Jihar Jigawa:
Bude group don tattaunawa akan abin da ya shafi biki tare da ‘yan’uwa da abokai hakan ba laifi bane sai dai idan abin da za a tattauna ya sabawa shari’a da al’ada. Kalubale na iya afkuwa musamman idan group din ya zama ana yin abin da ya sabawa shari’a da al’ada akan koyi abubuwa munana ta irin wannan hanyar kuma ta irin wannan hanya mata ke bayyana sirrin mazajensu da duk wani abu dake faruwa a tsakaninsu da mazajensu wanda hakan ba daidai bane. Shawara ita ce mata su ji tsoron Allah su sani duk abin da suka aikata ta wannan kafa dama kowacce Allah na ji na ganinsu kuma zai musu hisabi akan duk abin da suka aikata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Minista Ya Fice Daga Jam’iyyar APC A Nasarawa
Tsohon Ministan Muhalli, Barrister Mohammed Hassan Abdullahi, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki a Nasarawa.
Abdullahi ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin ƙaramin Minista na Kimiyya da Fasaha, kafin daga bisani ya zama cikakken Ministan Muhalli. Haka kuma, ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa a lokacin Gwamna Tanko Al-Makura.
Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A KanoYa miƙa wasiƙar ficewarsa ga shugaban jam’iyyar APC na mazaɓarsa ta Uke, a ƙaramar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, a ranar Lahadi. Wasikar ta nuna dalilinsa na barin jam’iyyar a matsayin na “ƙashin kai”.
Barrister Abdullahi ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na yi wa ƙasa hidima da kuma goyon bayan da ya samu a lokacin aikinsa, inda ya ce: “Ina yi wa jam’iyya da shugabanninta fatan alheri.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp