2025-08-08@02:27:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 854
«Tsara Birane»:
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta ce akwai kwamitoci guda 30 da aka daurawa nauyin bibiyar yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Jihar ke sarrafa kudade domin gudanar da harkokin yau da kullum, gami da ayyukan raya kasa. Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana hakan lokacin wata ziyarar aiki...
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin. Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau kuma Sarkin Katsina na Masarautar Gusau. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarwarin da masu zaɓen sarakuna na masarautar Gusau...
Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari. Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Gwamnatin kasar Faransa ta yi kakkausar suka tare da tofin Allah tsine kan harin ta’addancin da aka kai birnin Zahidan na kasar Iran Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin birnin Zahidan na kasar Iran, tare da jaddada adawar kasarta kan duk wani harin ta’addanci da aka kai kan...
An fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa. Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban...
Ya ce rasuwar Dakta Usigbe babban rashi ne ba kawai ga kamfanin jaridar Tribune da fagen aikin jarida ba, har ma da ƙasar nan baki ɗaya. “Nijeriya ta yi rashi matuƙa — mun rasa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan jarida, wanda ilimin sa, jarumtar sa, da himmar sa ta sa kowa yana girmama shi.” A...
Dakarun kasar Yemen sun sanar da sabbin zabukan kara rurutan bude wuta kan makiya a matsayin martani ga abubuwan da suka faru a Gaza Dakarun sojin kasar Yemen sun bayyana a cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin jiya Lahadi cewa: Suna tunanin zafafa yakin da suke yi da ‘yan mamaya dangane da abin...
Ma’aikatar kula da sashen ayyukan jigilar kayayyaki ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, a cikin rabin farkon bana, an samu ci gaba mai yawa a bangaren, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a jiya Lahadi. Hukumar raya ci gaban kasa da gudanar da gyare-gyare, wacce take da alhakin tsara tsare-tsaren tattalin arzikin kasa...
Kungiyar yan tawaye M23 wacce take iko da yanki mai yawa a gabacin Democradiyyar Kongo ta bada sanarwan cewa idan gwamnatinn kasar Kongo bada gaggauta sakin fursinonin kungiyar ba, to tana iya kauracewa tattaunawan da za’a gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a watan mai zuwa. Shafin yanar gizo na Africanews ya nakalto babban...
Duk da alƙawuran sojoji na kama fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji domin hukunta shi kan laifunan ta’addanci, har yanzu ɗan ta’addan bai daddara ba, a yayin da suke ci gaba da farautar sa shi da sauran manyan shugabannin ’yan bindiga da ke addabar ’yan Nijeriya. Dakarun sojin da aka tura ƙarƙashin rundunar Operation Fansan...
Jami’an diblomasiyya na kasashen Iran da kuma na tarayyar Turai 3 wato Faransa da Jamus da kuma burtaniya sun fara tattaunawa gaba da gaba bayan yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka kai mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta kara da cewa wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci don zasu tattauna...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gusau, Dokta Ibrahim Bello na Jihar Zamfara. Sarkin ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 71. An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe HOTUNA: Yadda Kwankwaso ya karɓi ’yan APC zuwa NNPP a Kano Mai bai wa Shugaban Ƙasa...
Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa. Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya. Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: Taro Tsakanin Iran Da Tawagar Kasashen Turai Dama Ce Ta Gyarar Tunanin Tarai
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Taron Istanbul wata dama ce ta gyara matsayar Turai kan shirin makamashin nukiliyar Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i, ya yi la’akari da taron na yau tsakanin Iran da kasashe uku mambobin kungiyar hadin gwiwa ta JCPOA a matsayin wata muhimmiyar dama ta gyara...

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)
Hikimar Rashin Hade Farkon Shekarar Musulunci Da Tarihin Manzancin Annabi (SAW) Masu karatu har yanzu dai muna kan bayani game da abubuwan da suka sa Sahabbai ba su kafa tarihin kirgen shekarar musulunci ba da wasu manyan alherai na Musulunci, sai suka zabi Muharram ta zama farkon shekarar tare da lakaba mata shekarar Hijirah....

Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
Da yammacin yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya shugabanci taron tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da EU karo na 25, tare da shugaban majalisar EU Antonio Costa, da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen a nan birnin Beijing. A yayin taron, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da EU suna da moriya...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ana shirin sayar da makarantar firamare ta Yusuf Dantsoho da ke Unguwar Rimi GRA. Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Maman Lagos, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki makarantar. Makarantar...
Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen dabbobi. Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da nono...

Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
Kwanan nan, darektar zartaswa ta hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD, Anacláudia Rossbach, ta yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a hedkwatar hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD dake Nairobi, babban birnin Kenya. Yayin da aka ambato sakamakon da ya fi jawo hankali...

Ayatullahi Makarem Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kai Da Suka Bayar Lokacin Yakin Kwanaki 12
Ayatullah Makarem Shirazi ya jaddada cewa: An kara samun karfafan hadin kan al’umma Iran bayan wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya da Amurka kan kasarsu Ayatullah Nasser Makarem Shirazi, babban malamin addinin Musulunci a birnin Qum mai tsarki na kasar Iran ya jaddada cewa: An kara samun hadin kan kasa bayan yakin wuce gona da...
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin...
Kayan da aka gano a wajen samamen sun haɗa da wayoyin salula da dama, kwamfutoci, na’urorin haɗa Intanet da mota ƙirar Honda Accord. Sunayen waɗanda aka kama sun haɗa da: Ismaíl Nura, Suuleyman Ayeh, Usman Abdulrazaq, Emmanuel Chigozie, Akabe Seth, Daniel Imoter, Abdulganiyu Jimoh, Jafar Abubakar, Usman Nuraddeen, Mohammad Adnan da Abubakar Abusufyan. Sauran sun...
Gwamnatin Borno ta bayyana yawan ma’aikata a matsayin dalilin da ya sanya ƙananan hukumomin jihar ba za su iya biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata na Naira dubu 70,000 ba. Gwamnatin ta ce ta umarci shugabannin ƙananan hukumomin jihar su samar da tsari mai ɗorewa domin ƙaddamar da fara aikin mafi ƙarancin albashin. WFP zai dakatar...
Alkaluma da aka fitar a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi miliyan 6.95 a rabin farko na bana, inda ta cimma kaso 58 bisa dari na burinta na shekara. Kakakin ma’aikatar kula da ma’aikata da walwalar al’umma ta kasar Sin Cui Pengcheng ne ya bayyana haka yayin wani...
Hukumar Hisbah ta ce ta kama tare da lalata barasa da ta kai kimanin naira miliyan 5.8 a karamar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa. Kwamandan Hisbah a jihar Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga...
Jami’an tsaro sun hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ’yan rakiyarta shiga haramar Majalisar Dokoki ta Kasa, inda ta je da niyyar halartar zaman Majlasiar Dattawa a ranar Talata. Jami’an tsaro a daukacin kofofin shiga harabar majalisar sun hana ta shiga harabar majalisar ne a lokacin da ta yi yunkurin shiga domin halartar zaman ranar Talata,...
An wajabta wa ɗaliban makarantun firamare da Ƙaramar Sakandare mallakar lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) a Jihar Bauchi. Hukumar Kula da Ilimin Bai-ɗaya a Matakin Farko ta jihar (SUBEB) ce ta bayar da umarnin ta hannun shugabanta, Alhaji Adamu Mohammed Duguri. Ya bayyana cewa mallakar lambar NIN ta zama tilas lura da duk hukumomin...
Kungiyar Agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa yunwa na ƙara tsananta a Arewa maso Gabashin Nijeriya, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe. A cewar rahoton, rikicin da ya dauki shekaru 16 ya durƙusar da kasuwanci da hanyoyin samun aiki, wanda hakan ya tilastawa mutane dogaro da ƙananan gonaki don rayuwa. Mutum 16...

Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a yayin gudanar da taron manema labaru na yau da kullum da aka yi yau Litinin cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Tarayyar Turai EU. Kuma taron kolin kasar Sin da EU karo...
– Emmanuel Adegbola Aina – AIG na wucin gadi, sashen leƙen asiri – Omolara Ibidun Oloruntola – Hassan Abdu Yababet – CP, Kwalejin ‘Yan Sanda Jos – Bretet Emmanuel Simon – CP Jihar Taraba – Enyinnaya Inonachi Adiogu – CP, FCID, Gombe – Aminu Baba Raji – CP, FCID Alagbon – Mohammed Mu’azu Usman –...
A wani gagarumin mataki na karfafa yaki da rashin tsaro, gwamnatin jihar Zamfara ta gudanar da wani babban taron masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Gusau, da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma kaddamar da sabbin dabarun yaki da ayyukan ta’addanci da masu aikata laifuka. Taron wanda aka gudanar a...
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zabi Hon. Kamilu Sa’idu (Wamban Kasuwar Daji) a matsayin dan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Kaura Namoda ta Kudu da za a yi ranar 16 ga Agusta, 2025. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce Kamilu...
Ministocin tsaro na kasar Rasha ta JMI sun hadu a birnin Mosco don tattauna batun karfafa dangantakar tsaro a tsakaninsu a dai dai lokacinda al-amuran tsaro suke kara tabarbarewa a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan kasar Iran a Mosco yana fadar haka. Kazem Jalali, ya bayyana cewa...
Sanata Yemi Adaramodu, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, ya ce matsalar tsaro a Najeriya na raguwa, kuma tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa. Ya yaba da ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen yaƙi da ’yan bindiga da ’yan ta’adda. Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila WFP ya dakatar da tallafin abinci...
A bisa umarnin sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ, an yi nasarar gudanar da zaben majalisar jihar Zamfara a ranar Asabar din da ta gabata cikin kwanciyar hankali da lumana, inda aka dawo da dukkan mukamai ba tare da hamayya ba. Mukamin daya tilo da aka fara takaddama a kai ya sa daya...
Shugaba Trump da abokansa sun ce sun gano cewa ana tafka almundahana da zamba a hukumar. Rahoton na zuwa ne yayin da gomman shugabannin duniya ke taro a Birnin Sabeilla na kasar Sifaniya cikin makon nan domin tattauna batun katse tallafin, wanda ya fi kowane bayar da agaji a duniya. Bayan nazarin bayanan alkaluman tallafin...
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da lafta wa Tarayyar Turai da kuma Mexico harajin kashi 30 kan kayayyakin da ake shiga da su da su ƙasar daga ranar 1 ga Agusta. Bayanai sun ce ana ganin wannan matakin zai iya haddasa rikici mai tsanani tsakanin Amurka da biyu daga cikin manyan abokan kasuwancinta. An...

Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kama ‘Yan Leken Asirin Isra’ila A Lardin Mazandaran Na Kasar Iran
Dakarun juyin jaya halin Musulunci ta Iran sun kama wani wakilin hukumar leken asirin Isra’ila Mossad a arewacin kasar Iran Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanar da kame wani jami’in hukumar leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila “Mossad” a lardin Mazandaran (arewacin kasar Iran), wanda ke shirin kai harin ta’addanci a cikin kasar. Sanarwar...
Ali Mohammad Sabeghi, tsohon jami’in bangaren al-adu na ofishin jakadancin kasar Iran a kasar China ya karbi kyautar ‘Jakadan Abota’ na kasar China a wannan shekara ta 2025M. A bikin bada irin wannan kyauta karo na biyu. Labarin ya kara da cewa dangantaka tsakanin JMI ta kuma China yana daga cikin abota mafi kyau tsakanin...
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya ja kunnen shuwagabannin kasashen yammacin Turai kan shiga yaki da kasar Rasha. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Lavrov yana fadar haka, a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, labaran da suke isa kunnensa daga biranen Landan, Paris da kuma Berlin sun tabbatar...
Kididdigar ta nuna cewa maimakon amfani da wannan kudaden shigar don rage basussuka, wasu jihohi suna kara amso bashin. Jihar Ribas ta zama ta farko a jerin jihohin da adadin bashin cikin gida na naira biliyan 364.39 a wata uku na farkon 2025, mafi girma tsakanin jihohi 10. Basukan Jihar Inugu sun tashi daga naira...
Kamfanonin inshora za su kauracewa jiragen ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila saboda tsoron fuskantar hare-haren Yemen Jiragen ruwan da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila za su fuskanci kaurace daga kamfanonin inshora, sakamakon munanan hare-haren baya-bayan nan da sojojin Yemen suka kai kan jiragen Magic Seas da Eternity Sea, wadanda...
An tsara Jirgin zai rinka yin zirga-zirga ne, zuwa daukacin kasashen da ke Afirka ta yamma da kuma sama da haka, musamman yin zirga-zirga daga Nijeriya zuwa kasashen, Jamhiriyar Benin, Togo, Ghana, Kamaru, Sierra Leone, Ibory Coast, Masar, Afirka ta Kudu da sauransu, tare da kuma nuna bukatar yin kasuwanci wadda tuni, aka fara ta....
Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare kan tashar jiragen sama na Bengurion na HKI tare da amfani da makamai masu linzami samfurin Balistic. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin Yemen na cewa, sun kai hare-hare da makamai masu linzami ka tashar jiragen sama na Ben gurion kuma zasu...
Hukumomin tsaron uku su ne, na DIA, DSS da kuma NIA, inda kuma dokar, ta bayar da damar kafa ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro wato ONSA, wadda a baya, ake kiran ofishin da Babban Jami’in Tsaro na Kasa wato CONS. Wannan Jaridar, na nuna matukar damauwarta kan ci gaba da...
Manjo Janar Hatami: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Dakarun tsaron sama na sojojin Iran sun cimma wani gagarumar nasara a yakin da suka yi da makiya yahudawan sahayoniyya. A wata ganawa...
Wani manazarci na Amurka ya bayyana sansanonin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da Iran ta kaiwa hare-hare Wani manazarci Ba’amurke ya tattara jerin sansanonin da Iran ta kai wa hare-harer a wata makala inda ya bayyana cewa: Iran ta samu nasara a yakin da ta yi da ‘yan sahayoniyya. Wani mai sharhi kan harkokin siyasa da...
Sanarwar ta ƙara da cewa mutane 3,824 da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin jiha sun samu N7,960,162,598.64, yayin da 4,833 daga ƙarananan hukumomi aka tantance kuma an biya su N5,983,876,606 a matsayin garatuti. A jimlace, an biya N13,944,039,204.64 a matsayin kuɗaɗen garatuti. Gwamna Lawal bayan ya karbi rahoton ya ce gwamnatinsa ta ba...