Iran Ta Samarda Sabban Hanyoyi Na Fuskantar Barazanar Makiya
Published: 15th, October 2025 GMT
Babban hafsan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin kasar Iran sun samar da sabbin hanyoyin fuskantar makiya wadanda ta daukosu daga abinda ya faru a yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka duka dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Khatami yana fadar haka a jiya a ganawarsa da kwamitin al-amuran tsaro da harkokin waje na majalisar dokokin kasar Iran a ranar Litinin.
Khatami ya fadawa kwamitin yadda al-amura suke dangane da harkokin tsaron kasar da kuma al-amura da suka shafiu siyasa, tsaro da shirin sojojin kasar Iran dangane da abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya.
Khatami ya kara da cewa yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka dorawa kasar, makiya sun yi amfani da dukkan fanninin yakin da suka mallaka, wadanda suka hada fasahar zamani mafi inganci da siyasa da kafafen yada labarai, da lalata tsaron kasa, da kuma amfani da ayyukan leken asiri. Tare da wannan Janar Khatami y ace, mun fidda sabbin tsare-tsare da fuskantar makiya da barazanar da suke wa kasar. Wanda muna fatan wadannan sabbin makatan zasu ladabtar da mikaya su kuma dandana masu radadin wanda ya dace da su. Ya ce abinda ya tabbata a duniya a halin yanzu shi idan kana da karfi za’a iya yin koma, kuma mun gansu a fili a gaza, da nan Iran da Siriya , Qatar da kuma Lebanon. Ya ce mun dauki wadannan sabbin matakan ne dai da umurnin Jagoran juyin juya halin musulunci na cewa ‘Ku kasance masu karfi da Jajircewa’.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta Ce HKI Tana Jinkirta Neman Gawakin Yahudawa A Gaza October 15, 2025 Yansandan Italiya Sun Kara Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa A Garin Udine October 15, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Kalaman Kin Jinin Iran Da Trump Ya Yi A Majalisar Dokokin Isra’ila October 15, 2025 A Lokacin Yaki, Iran Ta Tarwatsa Wata Cibiyar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya Da Ke Yankin Farar Hula October 15, 2025 Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Dirar Mikiya Kan Donald Trump Kan Bai Wa Isra’ila Makamai October 15, 2025 Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Ce; ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa Abu Ne Mai Muhaimmanci October 15, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Cewa: Sake Gina Gaza Zai Ci Dala Biliyan 70 October 15, 2025 Araghchi : Trump bai cancanci mai samar da zaman lafiya ba October 14, 2025 UNDP : An ruguza fiye da kashi 80 cikin 100 na gine-ginen Gaza October 14, 2025 Sojojin Madagaska sun karbe mulkin kasar October 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya
Mai bai wa shugaban kasar Iran shawarar akan harkokin mata da iyali Malama Zahra Beruz Azar ta gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta tausayawa a tsakanin matan duniya domin samar da damar gina rayuwa ta jin kai da ‘yan’adamtaka mai dorewa.
Malama Zahra Behruz Azar ta gabatar da wannan shawarar ne dai a yayin taron kasa da kasa na mata da aka bude a kasar China.
Haka nan ta kuma bayyana cewa; A wannan lokacin muna rayuwa ne a cikin karnin da ci gaba da fasahar kere-kere su ka sauya salon rayuwa, ta yadda kirkirarriyar fasaha ta zama mai matukar tasiri a cikin matakan da ake dauka, kamar kuma yadda Sakandami ( Robot) ya maye gurbin bil’adama a cikin wasu fagage.”
Mai bai wa shugaban kasar Iran din shawara akan harkokin mata da iyali ta ci gaba da cewa; Tare da gagarumin ci gaban da ake da shi a fagen kere-kere sai dai kuma bai zama mai hada zukata ba, da hakan ya sa tazara mai yawa ta karu a tsakanin masu shi da marasa shi,kuma mutane suna kara zama cikin kadaici.
Haka nan kuma ta yi ishara da yadda ake kasuwanci da yake-yake da wasa da kwakwalen mutane da yadda kiyayya da gaba a cikin fagagen sadarwa na jama’a.
Zahra Behruz Azar ta ce jin kai da tausayawa su ne abubuwan da za su dawo da ruhin ‘yan’adamtaka a cikin duniyar da tashe-tashen hankula su ka ci dununta.
Dangane da rawar da mata suke takawa a Iran, Malama Zahra Behruz ta ce; Matan da suke cikin jami’oi a Iran sune kaso 60%, yayin da fagen kirkire-kirkire su ka kai kaso 24%. Lokitocin da ake da su a fadin Iran kuwa, mata ne kaso 40%, sai kuma masu bayar da shawar akan harkar kiwon lafiya da sun kai 30%.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Gagarumar Tarbar Da Aka Yi Wa Fursunonin Falasdinawa Ta Nuna Hakikanin Wanda Ya Sami Nasara October 14, 2025 Hamas Ta Mika Yahudawa 7 Daga Cikin 20 Da ke Hannunta Ga Kungiyar Red Cross October 13, 2025 Iran: Kakabawa Kasa Mai Makwabta 16 Takunkumi Ba Abu Ne Mai Sauki Ba. October 13, 2025 An Gano Gawarwaki 323 Karkashin Burabutsai Bayan Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 13, 2025 Tehran Ta yi Gargadi Game Da Barazanar Yaduwar Fadan Iyakar Afghanisatan Da Pakistan. October 13, 2025 Kungiyar (ASUU) Ta Sanar Da Shiga Yajin Aikin Gargadi A Kasa Baki Daya . October 13, 2025 Aragchi: HKI Ba Zata Mutunta Tsaida Wuta A Gaza Ba October 13, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Masar Saboda Bata Son Haduwa Da Azzaluman Da Suka Kashe Falasdinwa A Gaza October 13, 2025 Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh October 13, 2025 An Fara Musayar Fursinoni Tsakanun Hamas Da HKI A Safiyar Yau Litini October 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci