Sinner da Alcaraz za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu
Published: 3rd, November 2025 GMT
Carlos Alcaraz da Jannik Sinner za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu a watan Janairu, kwanaki takwas kacal kafin fara gasar Australian Open.
’Yan wasan biyu kuma za su hadu a babban wasan Hyundai Card Super Match a Incheon, a ranar 10 ga Janairu, yayin da za a fara babbar gasar Australian Open a Melbourne a ranar 18 ga Janairu.                
      
				
Kafin hakan dai ’yan wasan biyu, wadanda suka hadu a wasanni uku daga cikin hudu na Grand Slam a shekarar 2025, sun lashe kofuna tara cikin manyan gasa 10 da suka gabata a tsakaninsu.
Sinner ya dawo a matsayinsa na lamba daya a duniya bayan doke Alcaraz a ranar Lahadi, bayan nasarar maki 6-4 7-6 da ya samu kan Felix a gasar Paris Masters.
Kawo yanzu dai Alcaraz ne ke kan gaba a fafatawar da suka fuskanci junansu, inda ya samu nasara sau 10, yayin da Sinner ya samu nasara sau biyar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Carlos Alcaraz Koriya ta Kudu
এছাড়াও পড়ুন:
Komai zai iya faruwa a hare-haren da za mu kai Nijeriya — Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na shirin ɗaukar matakan soja da ka iya haɗawa da hare-haren ƙasa da na sama a Nijeriya.
Trump ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai, inda yake amsa tambayar yanayin yadda hare-haren za su kasance ta sama ko ta ƙasa.
NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? Tsagin Damagum da Anyanwu sun shirya mamaye hedikwatar PDP a yauA cewarsa, “komai na iya faruwa, abubuwa da dama za su faru. Ina nufin abubuwa masu yawa,” in ji shi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.
Shugaban ya ƙara da cewa, “Suna kashe Kiristoci, kuma suna kashe su da yawa. Ba za mu bari hakan ta ci gaba da faruwa ba.”
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar, Trump ya bayyana cewa ya umarci Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon da ta tsara yiwuwar kai hari kan Najeriya.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan ya yi gargaɗin cewa Kiristoci na fuskantar kisan kiyashi a ƙasar.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce tana kallon wannan batu a matsayin lamarin da za a iya warwarewa ta hanyar diflomasiyya, tana mai cewa ƙasashen biyu abokan hulɗa ne wajen yaƙi da ta’addanci.
Cikin wani saƙo da mai magana da yawun fadar gwamnatin Nijeriya Daniel Bwala ya wallafa ranar Lahadi, ya ce idan shugabannin ƙasashen biyu suka gana, akwai fatan samun mafita mai kyau.
Barazanar TrumpA wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social da tsakiyar daren ranar Asabar, Donald Trump ya ce Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan take idan har gwamnati ta ci gaba da nuna halin ko in kula kan kisan da ake yi wa mabiya addinin Kirista a kasar.
Hakazalika, Trump ya ce Amurka na iya kutsa wa Nijeriya da ƙarfin soji domin kakkabe ’yan ta’adda masu aikata ta’asa da sunan addinin Islama, sannan ya umurci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka da ta shirya domin yiwuwar kai wa Nijeriya samame.
Wannan furici na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatinsa ta saka Najeriya a jerin ƙasashen da ake yi wa Kirista kisan ƙare dangi, zargin da fadar mulki ta Abuja ta musanta.