Aminiya:
2025-11-04@02:15:43 GMT

Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi

Published: 3rd, November 2025 GMT

Tsohon ɗan takarar Shugaban Najeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce barazanar kawo wa Najeriya hari da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi abin damuwa ne da ke da ɗaga hankalin dukkan ’yan ƙasar.

Tsohon Gwamnan na Jihar Anambra, ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa yammacin wannan Litinin a shafinsa na X.

Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo

Obi ya bayyana cewa, barazanar turo sojojin Amurka su yaƙi ta’addanci da ma sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da Amurkan take da damuwa da su, lamari ne da dole dukkan ɗan Najeriya mai son ƙasar ya ja masa hankali.

“Babu shakka Nijeriya na fama da matsalar tsaro, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da ma asarar dukiya.

“A cewar Ƙungiyar Amnesty, aƙalla mutum 10,000 aka kashe a Nijeriya daga watan Mayun 2023, kuma kamar yadda na sha nanatawa, kashe-kashe a Najeriya abin takaici ne, kuma abin Allah-wadai da ya zama dole a tashi haiƙan wajen magancewa.”

Obi ya ce za a iya magance matsalar ta hanyar samun shugabanci na nagari, “duk da cewa ba a wannan gwamnatin matsalar ta fara ba, amma akwai rashin ƙwarewa da rashin takaɓus daga ɓangaren wannan mulkin na gwamnatin APC wajen tunkarar matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.”

Ya ce Najeriya da Amurka suna da tarihin alaƙa da juna mai kyau, “kuma bai kamata a watsar da wannan alaƙar ba a yanzu.

“Wannan sabuwar dambarwar na buƙatar haɗakar diflomasiyya da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu domin lalubo hanyoyin magance matsalar.”

Barazanar da Trump ya yi wa Nijeriya

A bayan nan ne dai Shugaba Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka ta fara shirye-shiryen yiwuwar kai hari ƙasar, bayan ya yi zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla a ƙasar.

Trump ya bayar da umarnin ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, kwana guda bayan da ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya, ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.

Tinubu ya mayar da martani

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa tun daga lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2023, tana ci gaba da gudanar da tattaunawa da duka shugabannin Kiristoci da Musulmai domin ƙarfafa haɗin-kai da magance matsalolin tsaro da ke shafar ’yan ƙasa daga kowane yanki da addini.

Tinubu ya ƙara da cewa Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya, wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ’yancin yin addini.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru.

A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi.

Ya ce: “Nanpon ya riga ya yanke Peter a kumatunsa yayin da yake rokon a bar shi. Lokacin da muka shiga tsakani muka ce ya daina, sai ya yi barazanar yanka duk wanda ya kusanto shi.

“Da Peter ya ga ba ya sauraron rokonsa, sai ya rungume shi yana rokonsa da kuka.

“Mun fita neman taimako amma babu wanda ya amsa mana. Da Peter ya yi kokarin tserewa sai ya fadi, Nanpon ya kamo shi ya ci gaba da saransa da adda.”

Wani kwararren masanin tsaro da yaki da ta’addanci ya wallafa a dandalin D a ranar Lahadi cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Filato sun kama wanda ake zargin.

Ya kuma ambaci majiyoyi da suka tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar rahoton da aka samu daga Babban Jami’in Tsaro na jami’ar.

Ya rubuta cewa, “Rundunar ‘Yansanda ta Filato ta kama wani dalibi mai shekaru 23 na Jami’ar Jos bisa zargin kashe abokinsa sannan ya binne shi a rami mara zurfi a cikin dakinsa da ke kauyen Rusau a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

“Majiyoyi sun tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi a Jos, inda suka danganta da rahoton da aka samu daga Babban Jami’in Tsaron jami’ar.

“A cewar majiyoyin, wanda ake zargin mai suna Dabid Nanpon Timmap, dalibi a matakin shekara ta uku a jami’ar, ya kai wa Peter Mata Mafurai, mai shekaru 22, hari da adda, ya kashe shi a gidansa.”

Zagazola ya kara da cewa, bayan samun kiran gaggawa da misalin karfe 9:30 na safiya, DPO na sashin Laranto ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa wurin, inda aka kama wanda ake zargin.

“Majiyoyin sun ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya binne mamacin a cikin rami mara zurfi da ya haka a cikin dakinsa. An tono gawar kuma an kai ta dakin ajiye gawarwaki na Asibitin koyarwa na Jami’ar Bingham domin yin binciken gawar (autopsy),” in ji shi.

Ya kara da cewa, an tsare wanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike domin gano hakikanin dalilin kashe abokin nasa.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci November 1, 2025 Manyan Labarai Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NAJERIYA A YAU: Ko Kawo Dakarun Kasar Amurka Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • Trump ya jaddada shirin Amurka na kai hari a Najeriya
  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon ba barazana ba — Kwankwaso
  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami