Yara Kusan Miliyan 3 Za A Yiwa Rigakafin Cutukan Polio Da Kyanda A Jihar Sakkwato
Published: 7th, October 2025 GMT
An yi wa yara miliyan biyu da dubu takwas allura, yayin aikin rigakafin cutar Polio, kyanda, da kuma Gaida a jihar Sakkwato.
Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin da aka gudanar a garin Bodinga da ke karamar hukumar Bodinga.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai na ofishin mataimakin gwamnan jihar, Garba Muhammed, Alhaji Ahmed Aliyu ya raba wa manema labarai, ya bayyana cewa aikin polio din zai gudana ne a daukacin unguwanni 244 dake fadin jihar.
Don haka ya yi kira ga shugabannin al’umma da na addini da kuma abokan ci gaba da masu ruwa da tsaki da su ba da himma wajen tallafa wa wannan aikin ta hanyar hada kai da kuma tabbatar da cewa duk yaran da suka cancanta sun samu alluran rigakafin da ake bukata.
A cewar sa, za a yi allurar rigakafin ga yara ‘yan watanni 9 zuwa 14, kuma za a kwashe kwanaki 10 ana yin wannan aikin.
Ya bayyana cewa Najeriya ce tafi kowacce kasa yawan yara masu kamuwa da cutar kyanda da gaida a duniya.
Ya kara da cewa lamarin ya nuna akwai gagarumin gibi a fannin rigakafi na yaran da ba sa karbar alluran rigakafin a daidai lokacin da ya kamata, wanda ke haifar da munanan sakamako kamar kuramta, makanta, da sauran matsaloli.
Gwamnan wanda mataimakin gwamnan jihar Alhaji Idris Mohammed Gobir ya wakilta, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na gina tsarin kiwon lafiya wanda ba wai kawai ake iya samunsa ba, har ma da samar da ingantacciyar kulawa da tallafawa gano cututtuka da wuri.
A nasa jawabin kwamishinan lafiya na jihar Dr. Faruk Umar Abubakar Wurno ya bayyana cewa an samar da rukunin ma’aikata da zasu ziyarci unguwanni 244, inda kowane rukunin ma’aikatan akwai mutum 11 a cikin su.
Dakta Faruk Umar Wurno ya kara da cewa, jihar ta samu alluran rigakafi guda 3,072,520 daga hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa.
Kwamishinan ya kuma yi amfani da damar wajen mika godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa bada tallafin da takwarorinta ke yi na wannan aikin.
Da yake tsokaci, wakilin mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Hakimin Wurno, Alhaji Kabir Alhassan Cigari, ya bayar da tabbacin cewa sarakunan sun jajirce wajen ganin an cimma nasarar shirin.
MUSTAPHA/Sakkwato
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kyanda
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi
Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya sun bada sanarwan cewa lokacin kafa yansandan jihohi ya yi, har’ila yau dakuma karfafa kula da dazuzzukan kasar saboda magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnonin na fadar haka a jiya Litinin bayan taron gwamnonin shiyar kudu maso yammacin kasar da suka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo. Gwamnonin 6 sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika masu gadin dazuzzuka a shiyar kudu maso yammacin kasar don tabbatar da tsaronsu , sannan gwamnonin jihohin guda shida ne zasu dauki nauyin kula da jami’an tsaron. Labarin ya kara da cewa shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ne ya karanta jawabin bayan taron gwamononin 6. Sauran gwamnonin sun hada da Dapo Abiodun na jihar Ogun, Biodun Oyebanji na jihar Ekiti, Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo, Ademola Adeleke na jihar Osun, wanda mataimakinsa , Yerima Kola Adewusi ya wakilta sai kuma gwamna mai masaukin baki Seyi Makinde na jihar Oyo. Taron gwamnonin ya yabawa gwamnatin tarayyar kan kokarin da take yi na magance matsalolin tsaro a arewacin kasar, suna kuma gabatar da alhininsu gareta saboda abubuwan bakin ciki da suka faru a jihohin Kebbi, Naija da kuma Kwara.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji November 24, 2025 Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta November 24, 2025 Iran Ta Mika Ta’aziyyarta Ta Shahadar Kwamandan Mayakan Hizbullah November 24, 2025 Hizbullah Ta Sanar Da Shahadar Kwamandan Jihadi Haisam al-Tabtabai November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci