Aminiya:
2025-11-18@08:21:07 GMT

FERMA ta ƙaddamar da aikin gyara tsohuwar hanyar Kano

Published: 29th, September 2025 GMT

Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano.

Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin.

’Yan sanda sun kama kwayoyin N165.

4m da makamai a Kano ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya

Da yake ƙaddamar da shirin a Basawa, Zariya, shugaban FERMA na jihar Kaduna, Injiniya Kabir Iliyasu Danmarke, ya bayyana cewa aikin umurni ne daga shugaban hukumar na ƙasa, Dr. Chuku Emeka Obasi, bisa kudurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na rage haɗurra a hanyoyi.

“Mun ɗauki matasa 50 da za su yi aikin nan cikin wata guda, kuma akwai yiwuwar ƙara wa’adin idan bukata ta taso,” in ji shi.

Danmarke ya ce aikin da aka sanya masa suna “Operation Safeguard of Road” na nufin rage haɗurra da ke faruwa sakamakon tsawon ciyayi a gefen hanya da kuma lalacewar hanya.

Ya ƙara da cewa aikin zai rage kuɗin da direbobi ke kashewa wajen gyaran motoci, tare da samar da aikin yi ga matasa masu shekaru 18 zuwa 45 daga yankin domin inganta rayuwarsu.

Shugaban hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) mai kula da yankin Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya ce aikin ya zo a daidai lokacin “Ember Months” — watannin ƙarshen shekara da ake yawan zirga-zirga.

Ya yaba da shirin FERMA tare da kiran a ci gaba da irin wannan aiki a sauran hanyoyi.

Haka kuma, wakilin rundunar ‘yan sanda na Samaru, Zariya, ya yi alkawarin samar da tsaro ga ma’aikatan da ke gudanar da aikin domin tabbatar da an aiwatar da shi yadda ya kamata.

Aminiya ta ruwaito cewa a wajen ƙaddamarwar, an raba kayayyaki ga ma’aikatan da aka ɗauka domin sauƙaƙa gudanar da aikin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Kaduna Zariya

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Sun Lei, ya gabatar da tsokaci dangane da daftarin da Amurka ta gabatar, game da bukatar tsawaita ayyukan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a yankin Abyei na ko UNISFA a takaice. Sun, wanda ya yi tsokacin a jiya Juma’a, bayan jefa kuri’a a zaman kwamitin tsaron MDD kan daftarin, ya ce kasarsa ta damu game da yadda Amurka ta ingiza daftarin, wanda da ma ita ce ta gabatar da shi.

Ya ce a matsayin kasar dake sahun gaba wajen tallafawa tawagar ta UNISFA, Sin ta shiga an dama da ita a shawarwarin da suka shafi daftarin, to sai dai kuma daftarin ya fitar da wasu ma’aunai masu alaka da yanayin gudanar da harkokin siyasa a yankin na Abyei, tare da hade hakan da makomar tsawaita wa’adin aikin tawagar UNISFA. Kasar Sin ba ta gamsu da hakan ba, don haka ta kauracewa jefa kuri’a kan daftarin.

Sun Lei ya kara da cewa, yayin tattaunawa kan daftarin, da dama daga membobin kwamitin tsaron MDD sun gabatar da shawarwari masu ma’ana domin sake nazari. Kana a yayin shawarwarin ranar Alhamis a zauren kwamitin tsaron, dukkanin sassa sun amince kasar da ta gabatar da daftarin, ta shigar da shawarwarin dukkanin bangarori, maimakon rufe ido da ingiza shi yadda ta ga dama.

ADVERTISEMENT

Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da sauran membobin kwamitin tsaron MDD, wajen wanzar da hadin kai, da kawance tsakanin sassan kwamitin na tsaro, ta yadda za a kai ga tabbatar da tawagar ta musamman ta cimma nasarar sauke alhaki da nauyin dake wuyanta, da ma kara azamar wanzar da zaman lafiya, da tsaro a matakin kasa da kasa da na shiyyoyi. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci November 15, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo November 15, 2025 Daga Birnin Sin An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka November 15, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana
  • An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi
  • Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio
  • An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing
  • ’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro
  • Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa
  • Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 
  • Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso
  • Yadda Za Ku Gyara Kanku