Aminiya:
2025-11-02@19:46:05 GMT

Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara

Published: 15th, September 2025 GMT

Ɗan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, a wani zagayen ganawa da manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027.

Obi, wanda ke ƙoƙarin ƙara yauƙaƙa zumunci da manyan shugabanni a fadin ƙasar, ya bayyana cewa ziyarar na da alaƙa da burinsa na ganin an samu shugabanci na gaskiya da riƙon amana a Najeriya.

An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana cewa ziyararsa ta musamman zuwa Ibadan na da nufin girmama Rashidi Ladoja, wanda aka naɗa a matsayin Olubadan, da kuma jaddada muhimmancin Ibadan a siyasa, zamantakewa, da tattalin arzikin ƙasar.

“Na kai ziyara don girmama sabon Olubadan, Rashidi Ladoja, wanda ƙwarewarsa a matsayin tsohon sanata, gwamna, kuma attajiri za ta taimaka wajen ɗaga martabar Ibadan,” in ji Obi.

Ya ƙara da cewa tattaunawarsa da Obasanjo da Ladoja na da nasaba da ci gaban Najeriya da kuma shugabanci da ke da burin sauya al’umma ta fuskar gaskiya da adalci.

Ziyarar Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda ake hasashen zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Rashidi Ladoja

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu ta dakatar da babban taron PDP

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar babban taronta na ƙasa da aka shirya yi a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, a watan gobe.

Mai shari’a James Omotosho ne, ya bayar da wannan umarni, yayin da yake yanke hukunci kan wata ƙara da aka shigar domin sanin ko jam’iyyar PDP na da ikon ci gaba da shirya taron da aka tsara gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba.

Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Austine Nwachukwu, shugaban PDP na Jihar Imo; Amah Abraham Nnanna, shugaban PDP na Jihar Abiya da Turnah George, sakataren PDP na yankin Kudu maso Kudu.

Waɗanda ake ƙarar sun haɗa da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), PDP, Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Samuel Anyanwu, Sakataren shirya taruka na jam’iyyar, Umar Bature, Kwamitin Ayyuka na jam’iyyar na Ƙasa (NWC) da Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar na Ƙasa (NEC).

Masu shigar da ƙarar sun kasance ’yan tsahin Nyesom Wike ne.

Sun roƙi kotu da ta hana gudanar da taron, inda suka bayyana cewar jam’iyyar ta saɓa wa dokokinta, Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da kuma Dokar Zaɓe wajen shirya taron.

Lauyansu ya shaida wa kotu cewa: “Ba a gudanar da taron wakilai a jihohi 14 ba don haka shirin taron ya saɓa wa doka.”

Sai dai PDP ta kare kanta, inda ta ce lamarin na harkokin cikin gidan jam’iyyar ne, don haka bai kamata kotu ta tsoma baki ba.

Jam’iyyar ta zargi masu ƙarar da ƙoƙarin tayar da rikici domin hana ta gudanar da sabon zaɓen shugabanni.

Aminiya ta ruwaito cewa wannan rikici ya ƙara dagula al’amura a jam’iyyar PDP.

Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, a baya ya yi zargin cewa an yi amfani da hannunsa na bogi a takardun da aka aike wa INEC game da shirya taron.

Amma shugabancin jam’iyyar ya ƙaryata wannan zargi.

A halin yanzu, Kwamitin Shirya Taron na Ƙasa (NCOC) ya ɗage tantance ’yan takara da aka tsara gudanarwa a ranar 28 ga watan Oktoba.

Mutane da dama na ganin ɗage tantance ’yan takarae na da nasaba da jiran sakamakon hukuncin kotu kafin a ci gaba da shirye-shirye.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
  • Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP
  • Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti