Yadda matasa suka yi aikin gayya don gyara hanyoyi a Kafanchan
Published: 25th, August 2025 GMT
Matasa da dama a garin Kafanchan, da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, sun yi aikin gayya domin gyara hanyar garin.
Sun yi amfani da gatari, fatanya, diga da sauran kayan aiki wajen yi wa hanyar gyara.
Ɗaliba ta haɗu da ajalinta a hatsarin mota a Yobe Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarkiAikin ya haɗa da haƙa da faɗaɗa magudanan ruwa don kaucewa ambaliya da kuma hana hanyar ƙara lalacewa.
Shugaban ƙungiyar Kafanchan Youth Forum, Injiniya Sa’adu Bako, ya ce sun yi aikin ne domin rage wahalar da jama’a ke sha, musamman wajen zuwa jana’iza, musamman a lokacin damina.
Ya kuma yi kira ga gwamnati ta gyara hanyar, kasancewar ba maƙabarta kaɗai take kai wa ba, har da ƙauyukan manoma kamar Zauru da Kurdan.
“Ina kira ga Gwamna Uba Sani ya saurari koke-kokenmu, domin gyaran hanyar don sauƙaƙa rayuwar jama’a kuma ya taimaka wajen harkar kasuwanci da fitar da amfanin gona,” in ji shi.
Ya gode wa matasan da suka fito aikin sa-kan da kuma mutanen da suka tallafa musu da kuɗi da kayan aiki.
Wasu mazauna yankin sun kuma roƙi gwamnati ta kula da hanyoyin cikin garin Kafanchan, kasancewar jama’ar yankin manoma ne da ke buƙatar hanyoyin mota don fitar da amfanin gonakinsu.
Go hotunan yadda matasan suka gudanar da aikin:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aikin Gayya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp