An kama mutum biyu kan zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Kebbi
Published: 9th, September 2025 GMT
A ƙoƙarinta na daƙile matsalar cin zarafin yara, rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta samu nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa ƙananan yara fyaɗe a makon jiya.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, wata yarinya ’yar kimanin shekaru 10 da ke Unguwar Bedi a ƙaramar hukumar Zuru, ta faɗa mummunan tarkon ne a lokacin da mahaifiyarta ta aike ta karɓo saƙo.
Bayanai sun ce wani mai suna Amos Jondo Maliki, wanda ke maƙwabtaka da su, ya kai ta ɗakinsa inda ya samu damar saduwa da ita.
Haka zalika, wata yarinya mai shekara biyar a Unguwar Goribbu, ta shiga shagon wani Mansur Sani mai shekara 48 domin sayen alewa, inda shi ma ya tsugunar da ita ya riƙa sanya yatsansa cikin al’aurarta.
Rundunar ’yan sanda ta ce, da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da waɗannan ababen zargi a gaban kotu.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya jinjina wa Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Junaidu Bello, kan yadda yake ɗaukar lamarin cin zarafin yara da muhimmanci.
CP Bello ya bayyana takaicinsa kan faruwar lamarin, inda ya ba da tabbacin cewa rundunarsa za ta ci gaba da kare jama’a, musamman masu buƙata ta musamman da ƙananan yara.
Ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci cin zarafin yara ta kowace siga ba, inda kuma ya yi kira ga iyaye da su riƙa kula da shige da ficen yaransu, tare da gaggauta miƙa duk wani rahoton cin zarafi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.
Kwamishinan ya ƙara da cewa lamarin fyaɗe na ƙara ta’azzara a cikin al’umma, yana mai kiran gwamnati a matakai daban-daban da su ɗauki tsattsauran matakai domin rage yawaitar wannan danyen aiki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: fyaɗe Jihar Kebbi yarinya
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp