Shugaban Iran na Shirin fara wata muhimmiyar ziyara a Armenia da Belarus
Published: 17th, August 2025 GMT
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasar shawara Mahdi Sanaei, ya ce Pezeshkian zai bar Tehran zuwa Yerevan a ranar Litinin din nan, sannan ya wuce Minsk.
Ya kara da cewa, a ziyarar ta kwanaki biyu da shugaban zai kai, yana shirin tattaunawa da manyan hukumomin Armeniya da Belarus, kan hanyoyin da za a bi wajen fadada dangantakarsu, musamman a fannin kasuwanci, da kuma sanya hannu a kan takardun yarjeniyoyi a tsakaninsu.
Sanaei ya kara da cewa an shirya kai ziyara a kasashen Armenia da Belarus a karshen watan Yuni, amma aka dage.
Ya kara da cewa, an kuma gayyaci shugaba Pezeshkian don halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) da za a yi a kasar Sin a karshen watan Agusta.
Ziyarar ta Pezeshkian ta zo ne a daidai lokacin da Armeniya da Azabaijan suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta jagoranci kullawa, inda a karkashinta za a kafa wata hanyar sufuri da ta hada Azarbaijan da na Nakhchivan.
A karkashin yarjejeniyar da aka kulla a Washington a ranar 8 ga watan Agusta, Armenia ta bai wa Amurka hakki na musamman don samar da wata hanya a kudancin lardin Syunik, wanda ke kan iyaka da Iran.
Iran ta dade tana adawa da wannan ra’ayin, tana mai cewa za ta sauya tsarin siyasar yankin Kudancin Caucasus kuma zai takaita ikon Iran na amfani da hanyoyin sufuri a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Denmark na nazarin kakaba wa Isra’ila takunkumi kan batun Gaza August 17, 2025 Jakadan Iran a Saudiyya: Kasashen biyu na tuntubar juna a kan muhimman batutuwa na yankin August 17, 2025 Gaza: A cikin sa’o’i 24 Mutane da dama sun yi shahada daruruwa sun jikkata a hare-haren Isra’ila August 17, 2025 An kashe mutane 17 a harin da dakarun RSF suka kai a El Fasher, Sudan August 17, 2025 Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Yi Allah Wadai Da Kalaman Netanyahu Kan Mamaye Yankunan Kasashe August 16, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Furucin Jami’ar Kotun ICJ Na Goyon Bayan Isra’ila August 16, 2025 Araqchi Ya Gode Wa Gwamnatin Iraki Da Al’ummarta Kan Kyakkyawar Tarbar Masu Ziyarar Arba’een August 16, 2025 Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Sanya Ta Cikin Jerin Sunayen Bakin Littafin MDD August 16, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Tafka Muggan Ayyukansu A Yankin Zirin Gaza August 16, 2025 Mataimakiyar Shugaban Kotun ICJ Ta Ce Tana Goyon Bayan HKI August 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar
Yau Lahadi al’ummar Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar.
Masu kada kuri’a miliyan takwas ne aka tantance domin kada kuri’a a zaben zagaye na farko da Shugaban kasar mai ci Paul Biya mai shekara 92 dake neman wa’adi na takwas.
A cikin makonni biyu na yakin neman zaben, Shugaba Biya wanda aka dade ba a gan shi a bayyanar jama’a ba ya gudanar da gangami guda daya kacal, a garin Maroua dake yankin Arewa mai Nisa, daya daga cikin yankuna uku na arewa, inda ya sha alwashin magance matsalar tsaro da rashin aikin yi.
A hukumance dai ‘yan takara goma sha biyu ne ke fafatawa a wannan zaben, amma biyu sun janye.
Manyan masu kalubalantar Paul Biya guda biyu a wannan zaben su ne, Issa Tchiroma Bakary, na jam’iyyar CNSF, da Bello Bouba Maïgari, wanda zai iya dogaro da jam’iyyarsa ta (UNDP).
Batun tattalin arziki da rashin aikin yi da matsalar tsaro su ne suka fi mamaye yakin neman zaben.
Mista Biya na Jam’iyyar (RDPC), ya fara mulkin kasar ne tun shekarar 1982.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter A Kasar Habasha October 12, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci