Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya
Published: 18th, September 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Gombe, ta fara aikin gyara da sake duba hanyoyin kiwo 37 tare da filayen kiwo takwas a faɗin jihar.
Wannan aiki na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage rikici da ake samu tsakanin manoma da makiyaya.
HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a NajeriyaAn gudanar da aikin ne ƙarƙashin shirin ‘Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES)’ a matsayin wani ɓangare na gwamnatin jihar don samar da zaman lafiya.
Shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana cewa ana fuskantar matsaloli ne saboda lalacewar hanyoyin kiwo da gonaki.
A baya-bayan nan, tawagar shirin tare da jami’an tsaro, shugabannin gargajiya da jagororin makiyaya, sun kai ziyara ƙauyen Kunji da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba don sauraron ƙorafe-ƙorafen jama’a.
Gwamnatin ta tabbatar da cewa za a ci gaba da tattaunawa da dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa domin samar da mafita mai ɗorewa da kuma hana aukuwar rikici.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja
Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa lokacin da take kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga a ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Hakkin ya fito ne daga bakin Hakimin Bassa, Bagudu Amos, yayin wani taron tattaunawa da mata kan rikici da zaman lafiya mai taken: “Ƙarfafa Matakan Kare Fyade da Cin Zarafin Mata a Jihar Neja”.
Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar FubaraTaron dai wata kungiya mai zaman kanta mai suna Tunani Initiative ce ta shira shi, tare da hadin gwiwar gidauniyar Dorothy Njemanze Foundation da kuma gidauniyar Foundation, domin ƙarfafa gwiwar mata wajen magance cin zarafin jinsi a jihar.
Hakimin ya ce mahaifiyar ta yi tafiya mai nisa domin tserewa daga farmakin ’yan bindigar, ba tare da ta san cewa jaririn da ke bayanta ya riga ya mutu ba.
Ya ce lamarin da ya faru a shekarar 2023 na daga cikin abubuwan da ke ci wa mata ’yan gudun hijira tuwo a ƙwarya a kullum, inda ya ƙara da cewa yawancin matan ba su da gogewar ilimin da zai ba su damar tinkarar cin zarafin jinsi da ke tasowa sakamakon rashin tsaro.
Shugabar ƙungiyar Tunani Initiative, Maryam Mairo Ibrahim, ta ce ana buƙatar a ba mata dama wajen samar da zaman lafiya da warware rikice-rikice a Jihar Neja.
Ta yi kira ga mata da su haɗa kai don karya shingen da ke hana su yin tasiri a rayuwa.
Ta ce, “A Jihar Neja, kamar yadda ake fama da rashin tsaro a wasu wurare, mata su ne suka fi shan wahalar mafi yawan hare-hare da kashe-kashen da ake yi. Idan ’yan bindiga suka kai hari, yawanci maza ne ake kashewa, sai matan da aka bari su ɗauki nauyin sake gina iyali.
“Wadannan rawar da mata ke takawa ba a lura da ita yadda ya kamata. Saboda haka, wannan tattaunawa ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa rawar da mata ke takawa wajen samar da zaman lafiya da kuma magance cin zarafin jinsi a Jihar Neja,” in ji ta.
Daraktan Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Jihar, Nuhu Muhammad, ya jaddada buƙatar ƙara yawan mata a majalisar dokoki ta jiha da ta ƙasa, domin samar da dokoki da manufofi da suka dace da bukatunsu.