Gwamna AbdulRazaq Ya Amince Da Naira Biliyan 20 Don Gyaran Gine-ginen Makarantu A Kwara
Published: 4th, August 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati.
Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin.
Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko.
Ta kara da cewa gwamnatin ta gyara sama da ajujuwa 1,254 banda wasu muhimman ayyukan gyara da aka gudanar a wurare daban-daban.
Gwamnatin ta bayyana jin dadinta kan aiwatar da ayyukan gyaran makarantu na SUBEB-UBEC tun daga shekarar 2014.
Sanarwar ta ce wannan sabuwar gudummawar za ta hada da dakunan gwaje-gwaje da wuraren tsafta a makarantun da ke sassa daban-daban na jihar, domin cike gibi tare da kara karfafa ayyukan da SUBEB ke yi.
“Duk da irin manyan ayyukan da muka gudanar, muna sane da cewa har yanzu akwai gibin da ake bukatar cikewa, kuma wannan ne dalilin da ya sa Mai Girma Gwamna ya amince da wannan sabon matakin na musamman don rage gibin da ke cikin gine-ginen makarantu,” In ji sanarwar.
Ali Muhammad Rabi’u
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
Fitattun dalibai akalla 12 ne daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF).
A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa.
Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu.
A cewarsa, an zabo daliban 12 ne sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar.
Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya kunshi dukkan kuɗin da ake buƙata a karatun sakandaren daliban.
“Muna kira da jama’a su ba da gudummawa da kuma ɗaukar nauyin ɗalibai. Kada a bar wannan aiki ga gwamnati da iyaye kadai. Ilimantar da ‘ya’yanmu hakki ne da ya rataya a kanmu gaba ɗaya,” in ji Gwamna.
Ya yaba da tsarin zaɓen kuma ya taya waɗanda suka yi nasara murna.
A nata jawabin, Babbar Shugabar Kwara ETF, Oluwadamilola Amolegbe, ta ce daliban 12 sun fito ne daga cikin jerin ɗalibai 640 da aka fara tantancewa bisa cancanta.
Ta bayyana cewa tsarin zaɓen ya fara ne da rubuta jarabawa ga dukkan daliban firamare na aji shida da suka amfana da shirin KwaraLEARN na koyon fasahar zamani, har zuwa lokacin da aka kammala tantancewa.
Ali Muhammad Rabi’u