Leadership News Hausa:
2025-09-17@20:30:17 GMT

‘Yansanda Sun Ceto Yara 5 Da Aka Sace A Adamawa

Published: 14th, September 2025 GMT

‘Yansanda Sun Ceto Yara 5 Da Aka Sace A Adamawa

Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa. Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan titin garin Mubi a ɗimauce.

Anan ne, jami’an ‘yansandan suka ceto yaran da suka hada da Adamu Musa, Suleiman Idris, Suleiman Mohammed, Dauda Yahaya da Mohammed Alhassan, dukkansu mazauna garin Gwange, Maiduguri, jihar Borno. Binciken da ‘yansanda suka gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa wani mai suna Aliga Suleiman na Sabon Layi, Gwange, Maiduguri ne ya ɗauko yaran daga Maiduguri ba bisa ƙa’ida ba. ‘Yansandan sun ce ana ci gaba da kokarin cafke wanda ake zargin tare da gurfanar da shi gaban kotu. Kwamishinan ‘yansanda na rundunar, CP Dankombo Morris ya yabawa kwamandan yankin da tawagarsa bisa nasarar ceto yaran, ya kuma umurci sashen binciken manyan laifuka na jihar da ya ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 

Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.

 

Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.

 

Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.

 

Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.

 

Sai dai kasa da wata guda da kulla yarjejeniyar, an tattaro cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a Zamfara inda suka yi awon gaba da masallata da dama.

 

Wata majiya ta cikin garin, ta shaida cewa, harin ya afku ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa masallacin, suka kewaye shi, sannan suka tattara masallatan zuwa daji.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000