Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala gyaran makarantu fiye da 1,200 a kananan hukumomi 44 na jihar a wani yunkuri na farfado da harkar ilimi.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin taron bitar yini guda kan kara kaimi a tsarin duba ingancin karatu, da aka gudanar a dakin taro na Cibiyar Kula da Ilimin Al’umma (CERC).

Ya ce banda gyaran manyan makarantu, gwamnatin ta ware Naira miliyan 484 domin gudanar da karin ayyukan gyare-gyare a gundumomi 484, inda kansilolin mazabu ke kula da gudanarwar ayyukan.

“A karo na farko a tarihin Kano ake aiwatar da manyan ayyukan ilimi a wannan mataki. Mun riga mun gyara makarantu sama da 1,200 kuma an fara ayyuka a matakin gundumomi.” In ji Dr. Makoda.

Kwamishinan ya kara da cewa wannan ci gaba yana cikin matakan aiwatar da dokar ta-baci da aka ayyana kan harkar ilimi a watan Mayun 2024, domin dawo da martabar fannin.

Ya ce gwamnatin ta kuma amince da Naira biliyan 3 domin gyaran makarantun kwana 13 na ’yan mata da gwamnatin da ta shude ta rufe.

Dr. Makoda ya bayyana cewa Kano na da fiye da makarantu 30,000,  adadi mafi yawa a duk fadin Najeriya, kuma gwamnati na da niyyar ganin kowanne yaro ya samu ingantaccen ilimi cikin daidaito.

 

Taron ya horar da daraktoci, shugabannin makarantu da jami’an sa-ido, inda kwararru irin su Farfesa Ahmed Ilyasu da Bashir Sule suka gabatar da jawabai kan hanyoyin tantance darussa da dabarun inganta ilimi.

 

Daga Khadijah Aliyu

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

Idan aka aiwatar da wannan aiki yadda ya kamata, zai iya zama abin koyi a tsarin samar da gidaje a Nijeriya. Amma in aka bar shi ya faɗa cikin halin almubazzaranci da rashin kulawa da ya jima yana faruwa, to zai iya zama wani sabon abin misalin da ba zai amfani talaka.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
  • An Kaddamar da Makon MNCH na 2025, Ya Rarraba Fakitin Bayarwa 6,000, Kayan C/S 500
  • Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF
  • Gwamnatin Sakkwato Ta Sayo Manyan Tan-tan 250 Na Sama Da Naira Biliyan 22
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati
  • Za A Fara Bayar Da Bashin Miliyan 10 Ga Ma’aikatan Manyan Makarantu
  • Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Belin Dillalin Kwaya
  • Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP
  • Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano