Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina
Published: 11th, October 2025 GMT
Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Dokta Aishatu Umar Maigari, ta ce talauci da nuna bambanci na daga cikin manyan dalilan da ke hana yara mata damar samun ilimi a jihar.
Ta bayyana hakan ne a wajen bikin Ranar Yara Mata ’Yan Makaranta ta Duniya ta shekarar 2025, wanda Shirin AGILE tare da Access Initiative Africa da Nudge Initiative suka shirya a Gombe.
A wajen bikin, Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Asma’u Inuwa Yahaya, ta yaba da yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tabbatar da cewa ba a bar wata yarinya a baya wajen samun ilimi.
Ta ce Gwamnan jihar, ya bai wa ilimin yara mata muhimmanci, wanda hakan ya sa ake samu ƙaruwa yara mata da ke zuwa makaranta.
Kwamishiniyar, ta ƙara da cewa ma’aikatar ilimi tana aiki wajen samar da sabbin manufofi da tsare-tsare da za su taimaka wajen rage waɗannan matsaloli da tabbatar da damar ilimi ga kowa cikin adalci.
A nata jawabin, Kodinetan Shirin AGILE, Dokta Amina Haruna Abdul, ta ce bikin na bana an shirya shi ne don ƙarfafa gwiwar yara mata wajen ci gaba da neman ilimi duk da ƙalubalen da suke fuskanta.
Ta gode wa Uwargidan Gwamnan da ma’aikatar ilimi bisa goyon bayansu.
Haka kuma, Akawun Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Barista Rukayyatu Jalo, ta shawarci yara mata da su dage wajen yin karatu, inda ta bayyana cewa ilimi ne hanyar da za ta gina rayuwarsa.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka halarci bikin, sun bayyana farin ciki da godiya kan shirya taron saboda yadda ya ƙara musu ƙwarin gwiwa.
Ɗalibai da dama sun gudanar da muhawara da wasan kwaikwayo a wajen taron.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwamishiniya Yara mata
এছাড়াও পড়ুন:
Masanin Kenya: Taron Kolin Mata Ya Shaida Alkawarin Sin Na Inganta Hakkin Mata
Nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin gida, sun kafa ginshikin jagorancin duniya, wajen samar da ci gaban harkokin mata, musamman ta hanyar fitar da darussa, ta hanyar kyautata mu’amala tsakamnin bangarorin biyu. Babban misali shi ne yadda ake samun bunkasar dangantakar mata tsakanin kasashen Kenya da Sin, wadda aka inganta yayin ziyarar aiki da shugaban Kenya William Ruto ya kai kasar Sin a watan Afrilun bana. Kasashen biyu sun yi alkawarin zurfafa mu’amalar al’adu, ciki har da mu’amalar mata da matasa bisa tsarin dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Wadannan matakai sun kunshi fannoni kamar su tallafin karatu da horar da sana’o’i, kuma dukkansu sun haifar da babban sakamako. (Safiyah Ma)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA