An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe
Published: 30th, September 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri na rajistar yara kyauta domin rage adadin waɗanda ke zaune gida ba tare da zuwa makaranta ba.
Bincike ya nuna cewa fiye da yara 787,000 ne ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sanya gwamnatin ta tashi tsaye wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi.
Uwargidan Gwamnan Gombe, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ce ta ƙaddamar da shirin a hukumance, inda ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ganin kowane yaro ya samu damar karatu.
A cewarta, shirin zai taimaka wajen fitar da dubban yara daga zaman ƙangin zaman kashe wando, tare da samar musu da makoma mai kyau ta hanyar ilimi.
An shirya aiwatar da wannan tsari a dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar, inda aka tsara cewa kowacce ƙaramar hukuma za ta yi rajistar aƙalla yara 20,000, tare da raba musu kayan makaranta kyauta kamar jakunkuna, litattafai da kayan rubutu.
Aminiya ta ruwaito cewa shirin wani hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Gombe, SUBEB, UBEC da kuma UNICEF, inda ake sa ran za a rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta kafin shekarar 2030.
Da take jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Uwargidan Gwamna ta buƙaci iyaye da su rungumi wannan dama da hannu biyu-biyu, tana mai cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen bunƙasa ilimi da kyautata rayuwar yara a jihar.
Shugaban hukumar SUBEB, Alhaji Babaji Babadidi, ya bayyana cewa wannan shiri zai taimaka ƙwarai wajen ƙarfafa shigar yara makaranta, tare da tabbatar da cewa ba wai kawai suna shiga ba ne, har ma suna kammala karatunsu cikin nasara.
Ita kuwa Kwamishinar Ilimi ta jihar, Farfesa Aishatu Umar Maigari, ta bayyana cewa wannan mataki babbar dama ce ta rage gibin ilimi da ke tsakanin yara maza da mata, musamman a yankunan karkara.
“Muna sa ran wannan tsari zai canza akalar rayuwar dubban yara, tare da samar da ci gaba mai ɗorewa a ɓangaren ilimi,“ in ji ta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Gombe Makaranta yara zuwa makaranta ƙaddamar da
এছাড়াও পড়ুন:
Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas
Wani mutum da ake zargin yana fama da matsalar tabin hankali ya kai hari tare da kashe wani soja a yankin Imota da ke Ikorodu a jihar Legas.
Lamarin, wanda ya faru a fili da rana tsaka a ranar Lahadi, ya sa makwabtan wurin da dama guduwa don neman tsira.
Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar AlhamisShaidu sun bayyana cewa wanda ya kai harin, wanda ba shi da makami sai sanda ta itace, ya kusanci sojan ya dinga dukan shi da sandar.
Sojan da ya rasu, wanda aka ce yana aiki a karkashin Operation AWASE, rundunar haɗin gwiwa ta musamman da ke yaki da laifuka a jihar, ya mutu sakamakon raunukan da ya samu.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 16 ga Nuwamba, 2025, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, lokacin da aka tura sojan don aikin tsaro na cikin gida.
Rundunar Sojojin Najeriya ta 81 ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da yin ta’aziyya ga iyalan sojan da ya rasu.
Mai rikon mukamin Daraktan Hulɗa da Jama’a na shiyyar, Musa Yahaya, ya bayyana a ranar Talata cewa sojan yana ƙoƙarin kwantar da tarzoma ne lokacin da mai harin ya bugi kansa da sanda mai nauyi, wanda ya jawo masa mummunan rauni.
Ya kuma ce sauran sojoji sun hanzarta shawo kan lamarin, suka kashe mutumin tare da dawo da makamin sojan.
Yahaya ya ƙara da cewa an garzaya da sojan da ya ji rauni zuwa Asibitin Gwamnati da ke Ikorodu, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Ya ce tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin, kuma rundunar sojoji ta yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da kuma bayar da rahoton duk wani abun da ba su yarda da shi ba.