Shekara 1 bayan rushewa, har yanzu ba gyara titin Kano–Maiduguri ba
Published: 29th, September 2025 GMT
Shekara guda matafiya da direbobi a ƙauyukan Malori-Guskuri da Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi na ci gaba da fama da wahala bayan da ruwan sama ya karya babban titin Kano–Maiduguri.
A ranar 7 ga Agusta, 2024 ne ruwa ya cinye babbar hanyar a Malori-Guskuri, ya kuma yanke babban ɓangare na hanya.
Shekara guda da wata ɗaya bayan faruwar lamarin, wanda ya mayar wuraren da suka rushe sun koma tarkon mutuwa da ke haddasa haɗurra da suka kashe mutane da raunata wasu da dama.
Wakilinmu da ya kai ziyara ya samu wani kamfanin gine-gine ya dawo Malori da kayan aikinsa. Mazauna sun tabbatar da cewa a makon da ya gabata ne kamfanin ya dawo wurin—fiye da shekara guda bayan lalacewar hanyar.
Yajin aiki: Likitoci sun ba wa gwamnati wa’adin kwana 30 Ana zargin ’yan sanda da kashe limami a KanoDuk da haka ɓangaren Sabon Gari bai samu gyara ba, lamarin da ke ci gaba da jefa direbobi da sauran matafiya da mazauna cikin hatsari.
Wani direban tifa kuma PRO na ƙungiyar direbobin tifa a Katagum, Shehu Muhammad, ya bayyana ɓangaren Sabon Gari a matsayin “tarkon mutuwa.”
“Wannan wurin ya zama tarko. Na shaida lokacin da motoci biyu cike da fasinjoji suka faɗa cikin wurin da ya yanke. Akwai lokaci da ake yi aikin ceto, aka fitar da wata mata ba ta da hayyacinta, sauran kuma sun samu munanan raunuka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa duk da muhimmancin hanyar wajen haɗa manyan cibiyoyin kasuwanci a Arewacin Najeriya, gwamnati ta yi jinkiri wajen ɗaukar mataki.
“Mun gaji da jira. Abin takaici ne, muna da sanata da ’yan mambobin majalisar wakilai da shugaban ƙaramar hukuma, amma kamar ba sa bi ta wannan hanya. Muna roƙon Allah Ya taɓa zukatan shugabanni su kawo ɗauki,” in ji shi.
Shi ma wani direba mai suna Muhammadu Salisu, wanda aka fi sani da Salisu Mai Tifa, ya ce sama da shekara guda ke nan suna fama da wannan lalacewar hanyar, musamman a Sabon Gari.
Ya ce, “Wurin ya zama tarko. A farkon wannan shekara ruwan sama ya cinye hanyar gaba ɗaya. Mutane da dama sun mutu a haɗurra, dukiya kuma ta salwanta,” in ji shi.
Ya bayyana cewa akwai lokacin da hukumomi suka sa manyan injina suka toshe wani ɓangare na hanya don rage hadurra, amma daga bisani kamfanin ya ja da baya ya bar aikin.
A bangaren mazauna kuwa, Safiyanu Garba na Sabon Gari ya ce hadurra sun zama kusan kullum.
“Da wuya kwanaki 10 su wuce ba tare da an samu haɗari ba. Wasu lokutan masu babura da fasinjoji kan rasa rayukansu a wurin,” in ji shi.
Shi ma Muhammadu Dadi na Malori ya ce rushewar ta addabi jama’a musamman a lokacin damina, inda ruwan sama ke taruwa a rami ya toshe hanyar tafiya a ƙafa.
Yahaya Mohammed, wani mazaunin Malori, ya tabbatar da mutuwar mutane da dama a wurin, ya kuma ce sun ji daɗin ganin kamfanin ya dawo da injina don fara aikin gyaran.
Lokacin da aka tuntuɓi PRO na kamfanin Triacta, Ibrahim, ya ce sai ya tattauna da shugabanni kafin ya ba da bayani, amma bai samu damar yin hakan kafin lokacin bugawa ba.
Ƙoƙarin jin ta bakin Kwanturola na Ma’aikatar Ayyuka a Bauchi bai yi nasara ba. Sai dai wani jami’in ma’aikatar ya shaida wa wakilinmu a asirce cewa Gwamnatin Tarayya ta sake ba da kwangilar ne ga kamfanin Triacta.
A cewarsa, kamfanin ya fara da ɓangaren Malori ne saboda tsananin wahalar aikin, kafin ya koma Sabon Gari bayan kammala wannan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hanya Sabon Gari a Sabon Gari kamfanin ya
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Yi Wa Maryam Sanda Afuwa Bayan Shafe Shekaru 6 A Gidan Yari
Baya ga Maryam Sanda, Shugaba Tinubu ya kuma yafe wa wasu mutane da dama, ciki har da Janar Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, da Faruku Lawan, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne daga Jihar Kano.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA