Mazauna Sabon Gero Sun Koka Kan Watsi Da Aikin Gyaran Hanyarsu
Published: 2nd, October 2025 GMT
Mazauna unguwar Sabon Gero, dake bayan Millennium City a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta kammala aikin gyaran titin unguwar, wanda suka ce an bar shi a cikin mawuyacin hali duk da cewa an bai wa wani kamfani aikin kusan shekara guda da ta gabata.
Mazauna yankin sun bayyana cewa halin da hanyar take ciki ya jefa su cikin matsanancin rayuwa, musamman mata masu juna biyu da ke tilasta musu hawa babura domin neman kulawa a wajen unguwar, kasancewar babu asibiti a yankin.
Ɗaya daga cikin mazauna, Rashida Shehu, wadda ke da juna biyu, ta ce ta ji rauni a lokacin da take kokarin bin hanyar zuwa gari domin kula da lafiya, inda ta roƙi gwamnati ta taimaka musu cikin gaggawa.
Haka kuma, rashin makarantar gwamnati a Sabon Gero ya sanya yaran mazauna yankin cikin wahala, saboda da dama daga cikinsu ba sa iya jure tafiyar neman ilimi zuwa waje.
Manoma kuma sun koka kan yadda rashin titin ke hana su kai kayayyakin gona kasuwa.
Mai unguwar Sabon Gero, Mai Anguwa Sunusi, ya bayyana cewa tun shekara guda da ta gabata aka bai wa kamfanin gyaran hanya na Think Lab aikin, amma har yanzu babu wani ci gaba da aka gani a wajen.
Ya roƙi gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da ya sanya wa aikin titin muhimmanci don amfanin al’umma da jihar baki ɗaya.
A nasa bangaren, matasa ƙarƙashin kungiyar cigaban Sabon Gero sun yi barazanar gudanar da zanga-zangar lumana idan aka ci gaba da yin shiru kan aikin, inda suka ce jinkirin kammalawa ya jawo tsaikon ci gaba tare da jefa al’umma cikin haɗari da matsalolin tsaro.
’Yan kasuwa da masu sana’o’i a yankin sun kuma ce lalacewar titin ta rage masu ciniki, tare da hana masu saka jari daga wajen zuwa yin kasuwanci a Sabon Gero.
A cewar su, wannan yanayi ya sabawa alkawuran gwamnati na samar da ci gaban kowa da kowa, abin da ya sa suke jin an nuna musu wariya.
COV: Khadija Kubau
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gyaran Hanyarsu Watsi
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
Kamar ‘yan wasa da masu horarwa, an hana jami’an wasa shiga ayyukan yin caca bisa ga ka’idojin TFF, da kuma na FIFA da hukumar gudanarwa ta Turai (Uefa), masu gabatar da kara na Turkiyya sun bayar da umarnin tsare mutane 21 ciki har da alkalai 17 da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani bangare na babban bincike kan yin caca da kuma shirya yadda sakamakon wasa zai iya fitowa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA