Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya
Published: 2nd, October 2025 GMT
Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro.
’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji.
Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a KanoRahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe.
Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba.
Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram suka addaba shekaru da dama.
A wasu yankuna, an buɗe makarantu a sansanonin ’yan gudun hijira domin yara su samu damar ci gaba da karatu, amma a yawancin ƙauyuka makarantu sun daina aiki gaba ɗaya, lamarin da ya tilasta dubban yara daina zuwa makaranta.
Ga yadda jadawalin ya kama a jihohi: Zamfara: An rufe makarantu 20 na firamare da 19 na sakandare, wasu kuma sojoji ne amfani da su. Neja: Makarantu 18 na firamare, guda ɗaya ta sakandare da 11 na Fulani duk an rufe su, da dama sun koma sansanin sojoji. Sakkwato: An rufe Makarantu shida, wasu ’yan gudun hijira ko ’yan bindiga ke amfani da su. Katsina: An rufe makarantu 52 bayan yawaitar hare-hare da satar ɗalibai. Kaduna: Aƙalla makarantu shida suka daina aiki sakamakon mazauna ƙauyukan sun yi hijira. Kebbi: An rufe makarantu bayan satar ɗalibai 96 a Birnin Yauri a 2021. Benuwe: An rufe makarantu 55 a 2024, yanzu ’yan gudun hijira ne ke zaune a cikinsu. Kwara: An rufe wasu makarantu a Ƙaramar Hukumar Patigi bayan yawaitar hare-hare ’yan bindiga. Matsalar da ilimi ke fuskantaNajeriya tana daga cikin ƙasashen da suka fi yawan yara da ba sa zuwa makaranta ba.
UNICEF ta ƙiyasta cewa yara miliyan 10.2 masu shekarun zuwa firamare da miliyan 8.1 masu shekarun zuwa sakandare ne ke zaune a gida ba tare da makaranta ba.
Katsina, Kebbi da Sakkwato sun kowa yawan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta, inda kowace jiha ke da aƙalla yara miliyan ɗaya.
Masana sun ce wannan matsala na haifar da mummunan makoma ga Najeriya.
UNICEF ta yi gargaɗin cewa kowace a duk shekara idan aka samu yaron da baya zuwa makaranta, hakan na ƙara jefa shi cikin hatsarin faɗawa cikin talauci.
Masana tsaro kuma sun ce idan ba a ɗauki mataki ba, samari da ba sa zuwa makaranta na iya shiga ayyukan ta’addanci da aikata munanan laifuka, yayin da ’yan mata za a tilasta musu yin aure da wuri, ko kuma shiga karuwanci da sayar da kaya a titi.
Sun jaddada cewa idan ba a magance wannan matsala ba, ƙasar za ta fuskanci ƙarin jahilai, talauci da tashin hankali.
Iyaye da shugabannin al’umma suna roƙon gwamnati da ta magance matsalar tsaro domin yara su samu damar komawa makarantu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa Ɗalibai makarantu Tsaro yara An rufe makarantu yan gudun hijira zuwa makaranta
এছাড়াও পড়ুন:
An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin
An sanya hannu kan yarjejeniyoyin cinikayya na biliyoyin kudi, a yayin baje kolin hajojin fasahohin zamani na kasar Sin ko CHTF, wanda aka kammala a jiya Lahadi a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin. Wannan ne karo na 27 da aka gudanar da baje kolin na CHTF, inda aka kai ga daddale huldodin cinikayya da ayyukan zuba jari 1,023, wadanda darajarsu ta haura kudin Sin yuan biliyan 170, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 24.
Baje kolin na wannan karo ya gudana ne bisa taken “Fasahohi masu jagorantar ci gaba da dunkulewar masana’antu”. Kazalika, taron na yini uku ya hallara kamfanoni da hukumomi sama da 5,000 daga kasashe da yankuna sama da 100, ya kuma samu halartar baki sama da 450,000.
Yayin baje kolin na CHTF, an nuna sabbin kayayyaki sama da 5,000, da fasahohi da ayyukan kirkire-kirkire da dama. Har ila yau, an samar da manyan yankunan nune-nune 22, ciki har da na muhimman na’urorin gudanar da ayyuka, da na fasahar AI da mutum-mutumin inji, da manyan kayan ayyukan na kasa, da kayan laturoni, da na’urorin sufurin sama dake zirga-zirga kusa da doron kasa, kayayyakin da suka shaida halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkokin binciken kimiyya na duniya, da nasarorin da Sin ta cimma a fannonin kirkire-kirkire. (Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA