Kotu ta aike da mutumin da ake zargi da satar yaran Kano yana kaiwa Delta zuwa gidan gyaran hali
Published: 15th, October 2025 GMT
Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya.
Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki.
Hukumar Hana Fatucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce dai da gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harkallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, wadanda su ba su je kotun ba a ranar.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu ce ta bayar da umarnin kullewar yayin fara sauraron shari’ar, bayan sauraron bukatar lauyan masu kara, Salisu Muhammad Tahir da na wanda ake karar, Gideon Uzo.
Daga nan ne kuma kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba inda ake sa ran za a gurfanar da Christpher tare da sauran wadanda ake zargin.
An dai kama Chrispoher ne bayan wani samame da jami’an hukumar ta NAPTIP suka kai gidan nasa da ke jihar Delta sannan suka ceto yara takwas da ake zargin ya sace su daga Kano sannan ya kai su gidan marayun nasa da ke Asaba, babban birnin jihar ta Delta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: satar yara
এছাড়াও পড়ুন:
Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje
Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje
Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta.
Ya kara da cewa: Mutane 170,000 marasa lafiya da kuma wadanda suka jikkata na bukatar tafiya cikin gaggawa zuwa wajen Gaza domin neman magani.
Al-Nasser Medical Complex ya kuma ce: Yara 5,500 na bukatar magani a wajen Gaza. Daraktan asibitin yara na Nasser Medical Complex, Dr. Ahmed Al-Farra, ya bayyana cewa, akwai yara 5,500 a zirin Gaza da ke bukatar agajin gaggawa a wajen yankin saboda tsananin karancin magunguna da kuma ci gaba da tabarbarewar yanayin kiwon lafiya.
A nata bangaren, Nour Al-Saqa, mai kula da harkokin yada labarai na kungiyar likitocin da ke yankin zirin Gaza, ta ce sama da mutane 170,000 da suka jikkata a zirin Gaza na bukatar kulawar gaggawa.
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki tun ranar Juma’a. A matakin farko, yarjejeniyar ta tanadi shigar da kusan tireloli 600 na kayan agajin gaggawa a kowace rana. Sai dai wasu kananan motoci ne kawai aka ba su izinin shiga, kuma har yanzu ba a kai agajin jinya a zirin Gaza ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci