Sojoji sun kashe kasurgumin dan ta’adda da yaransa 5 a Kogi
Published: 8th, September 2025 GMT
Dakarun sojin Najeriya sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda wanda aka fi sani da suna Kachalla Bala da yaransa biyar a Jihar Kogi.
Sojojin Birget ta 12 da ke Lakwaja, hedikwatar jihar sun kuma yi nasarar ceto wasu mutanen da gungun ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi ya ce samamen da sojojin ke kaiwa a sassan jihar domin kakkabe ayyukan ’yan binidga yana samun nasara a yankunan Tunga da Aleke da Ungwan Soni da Ungwan Nyaba da kuma Ankomi.
Yankin gadar Agbede–Adankoo (Mosalanci Boka) da ke yankunan Lokoja, Kabba-Bunu, da kuma Karamar Hukumar Yagba sun yi iyaka da jihohin Kwara da Neja, wanda hakan ya sa suka zama mafaka ga ayyukan ’yan bindiga.
Yiwuwar yajin aikin direbobin tankar mai kan rikicin Matatar Dangote
Yadda dawowar makarantu ta zo mana cikin tsadar rayuwa — Iyayeউৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.