Yadda bom ya kashe yara 2 ya jikkata wasu 6 a Borno
Published: 19th, August 2025 GMT
Yara 2 sun mutu wasu 6 sun jikkata bayan tashin bom a yankin Ƙofa Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno.
Shaidu a garin sun shaida wa wakilinmu cewa bom ɗin ya tashi ne bayan yaran sun kawo shi gida bisa rashin sani.
Sun shaida wa wakilinmu cewa yaran sun kawo bam ɗin cikin gari ba tare da sanin hatsarinsa ba, suna ɗauka ƙarfe ne da za a sayar.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Lahadi.
’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa An rage kuɗin wankin koda da kashi 76% a asibitocin tarayya NAJERIYA A YAU: Halin Da Muke Ciki Bayan Rasa ‘Yan Uwanmu A Hadarin Kwale-Kwale A Sakkwato“Mun samu rahoton cewa yaran sun tono bam ɗin ne daga ƙasa suka kai gida. Abin takaici, ya fashe, inda ya kashe ɗaya daga cikinsu kuma ya jikkata guda shida,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ’yan sanda sun gaggauta kai waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, inda ake ci gaba da kula da su.
ASP Daso ya bayyana cewa rundunar tana ƙara wayar da kan al’umma don kauce wa irin waɗannan abubuwa. “Wannan lamari ya faru a Konduga, Dikwa, Monguno da Jere duk da dokar hana tattara ƙarfe a jihar,” in ji shi.
Jerin taahin bom a Borno a baya-bayan nan A baya-bayan nan, rundunar ta gano wani bam da bai fashe ba a wata gona a Dikwa. Wannan lamari na zuwa ne bayan wasu fashewar bam da suka faru a jihar. A ranar 27 ga Janairu, 2024, almajirai shida da wani mai sayar da ƙarfe sun mutu a Gubio. A watan Yuli, 2022, ’yan bola-jari 13 sun mutu a Bama sakamakon fashewar bam da suka tono.উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato
KADA ta yi gargaɗi cewa haƙurin jama’a ya ƙare, tana mai jaddada cewa shiru da halin ko-in-kula daga shugabanni ba za a ƙara yarda da shi ba. Sun yi kira da a tabbatar da adalci da kuma mayar da zaman lafiya a yankin, tare da nuna goyon baya ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Garga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp