Har yanzu ana fama da cutar kwalara a Najeriya – UNICEF
Published: 2nd, August 2025 GMT
Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka.
Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama tamfar alaƙaƙai a Najeriya.
“A cewarsa cutar Kwalara na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya, inda ƙasar ke fama da ɓarkewar cutar a ‘yan shekarun nan.”
“Ya zuwa ƙarshen watan Yuni, Najeriya ta samu adadin mutane 3,109 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara da kuma mutuwar mutane 86 a cikin jihohi 34,” in ji Fagninou.
Jami’in na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙara da cewa, wannan adadi ya sanya Najeriya ta zama ƙasa ta biyu da cutar ta fi ƙamari a yankin yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya kamar yadda aka ambata a baya.
Ya yi nuni da cewa ɓarkewar cutar kwalara a yankin yammaci da Afirka ta Tsakiyar ta haifar da matsala ga yara.
Ya ce, an ƙiyasta kimanin yara 80,000 na fuskantar barazanar kamuwa da cutar kwalara a yammacin Afirka da Afirka ta Tsakiya yayin da aka fara damina a faɗin yankin.
A cewarsa, ruwan sama kamar da bakin kwarya da yawaitar ambaliya da kuma yawan matsugunan su na haifar da haɗarin kamuwa da cutar kwalara da kuma jefa rayuwar yara cikin haɗari.
Ya bayyana cewa cutar kwalara cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar abinci ko ruwan da ke gurɓata da ƙwayoyin cuta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwalara yammacin Afirka da da cutar kwalara cutar kwalara a
এছাড়াও পড়ুন:
Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya
Kungiyar Ma’aikatan jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta mayar wa da gwamnati martanin cewa har yanzu tana ci gaba da gudanar da yajin aikin da take yi.
Ministan Lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ne dai ya bayyana cewa ƙungiyar ta janye yajin aikin gargaɗin.
An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a KebbiDa yake magana da manema labarai bayan wani taron sirri da aka yi a Abuja ranar Juma’a, Pate ya ce matakin ya biyo bayan yarjejeniyoyin da gwamnati da shugabannin Ƙungiyar NANNM suka cimma ne.
Amma da aka tuntuɓi shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Morakinyo Rilwan ya ce ba gaskiya ba ne cewa an janye yajin aikin.
“Idan har Ministan ne ya shirya yajin aikin, to zai iya janye yajin aikin, a ɓangarenmu yajin aikin da ƙungiyar ta shirya yana ci gaba da gudana, Ministan bai shirya yajin aikin ba, don haka ba shi da hurumin janye yajin.
Rilwan ya shaida wa Daily Trust ta wayar tarho cewa, “Akwai hanyoyin da za a bi, idan za a janye yajin aikin gaba ɗaya.
A ranar Laraba ne ma’aikatan jinya suka fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a faɗin ƙasar. Yajin aikin, a cewar shugabancin NANNM zai magance matsalolin da suka haɗa da rashin biyan albashi, ƙarancin ma’aikata, alawus-alawus da ba a biya ba da kuma rashin yanayin aiki mai kyau.
Wannan yajin aikin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun saƙa tsakanin likitoci da gwamnati kan walwala da sauran batutuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yajin aikin ma’aikatan jinya da ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 15 da NNNM ta bai wa gwamnatin tarayya wanda ya kawo cikas ga harkokin kiwon lafiya a faɗin Najeriya.