NAJERIYA A YAU: Yadda Ilimi Ke Ƙara Tsada Yayin Komawar Yara Makaranta
Published: 8th, September 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Iyaye na ci gaba da kokawa kan yadda ilimi ke ƙara tsada yayin komawan ’ya’yansu makaranta a sabuwar shekarar karatu.
Makarantu na ƙara ɓullo da sabbin hanyoyin karɓar kuɗi daga hannun yara da sunan koyarwa.
NAJERIYA A YAU: Yadda ake gudanar da bukukuwar Sallar Gani yayin Mauludi DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa HazoShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da ke sa ilimi ƙara tsada yayin da yara ke komawa makaranta.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Makaranta Komawa Makaranta
এছাড়াও পড়ুন:
Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure
Babbar Kotun Kano mai lamba 7 da ke zama a cikin birni ta bayar da umarnin tsare Aminu Ismail, mazaunin Unguwar Bai a Karamar Hukumar Ajingi ta jihar, bisa zarginsa da kashe mahaifinsa, Malam Dahiru Ahmad, ta hanyar caka masa wuƙa har lahira.
Lamarin ya faru ne bayan samun sabani tsakaninsu kan aniyar Aminu ta ƙara aure, wadda mahaifinsa ya ƙi goyon baya saboda abin da ya kira halin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasa.
Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – ZulumA cewar lauyan masu ƙara, Barrista Lamido Abba Sorondinki, wanda ake tuhuma ya shaida wa mahaifinsa niyyarsa ta kara mata ta biyu, amma mahaifinsa ya ba shi shawarar kada ya yi hakan, yana mai danganta matsalar da halin tattalin arzikin ƙasa ke ciki.
Wannan sabani ya rikide zuwa faɗa, inda ake zargin Aminu da caccaka wa mahaifin nasa wuƙa a ƙirji, lamarin da ya jawo masa rauni mai tsanani har ya rasa ransa.
An gurfanar da Aminu da laifin kisan kai, wanda ya saba da Sashe na 221 na kundin penal code.
Ana ci gaba da shari’ar, kuma kotu ta bayar da umarnin tsare shi har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron ƙarar.