Gidauniyar Misilli ta mayar da yara 150 makaranta a Gombe
Published: 15th, September 2025 GMT
A cikin shekaru uku da kafuwarta, gidauniyar Misilli, ta mayar da yara 150 makarantar boko a Jihar Gombe, ciki har da mata 88 da maza 62, tare da ɗaukar nauyin kuɗaɗen karatunsu.
Wannan mataki ya taimaka wajen rage nauyin iyaye marasa hali, inda suka samu ’yancin zaɓar makarantun da ke kusa da su.
Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan kuɗi a Akwa IbomShirin AGILE ya tallafa wa gidauniyar da litattafai domin ƙarfafa wannan yunƙuri, lamarin da shugabar shirin a Gombe, Dokta Amina Haruna Abdul, ta yaba da shi tare da alƙawarin yin haɗin gwiwa.
Ita ma, Dokta Hauwa Yahaya Umar daga SUBEB, ta ce irin wannan haɗin gwiwa yana ƙara wa gwamnati ƙwarin gwiwa bunƙasa ilimi.
A nasa ɓangaren, Daraktan shirye-shirye a Ma’aikatar Ilimi, Dokta Kabir Musa, ya yaba da ƙoƙarin gidauniyar tare da kira da ta ci gaba da tallafa wa al’umma.
Daraktan ayyuka na gidauniyar, Malam Yusuf Hamza, ya bayyana cewa duk da cewa ayyukan sun fi karkata ga Karamar Hukumar Gombe, ana shirin faɗaɗa shi zuwa wasu yankuna.
Ya ce suna tallafawa a fannoni da dama, ciki har da lafiya, ruwan sha, samar da tiransufoma da fitilu, da kuma shirin saka fitilu masu hasken rana guda 20 a unguwanni.
A fannin ilimi kuwa, Yusuf, ya ce suna biyan kuɗin makaranta, samar wa ɗalibai kuɗin karatu a makarantun sakandare 72, da kuma biyan kuɗin JAMB.
Shugaban gidauniyar, Isma’ila Uba Misilli, wanda shi ne babban daraktan yaɗa labarai na gwamnan Gombe, ya gode wa masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suka bayar.
Gidauniyar ta bai wa yara uku da suka fi nuna ƙwazo kekunan hawa, sannan aka bai wa sauran ɗalibai jakunkuna da kayan karatu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gidauniya Kayan Karatu
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk da cewa gwamnati na da dubban kwararrun malamai a makarantunta, har yanzu ana ganin ɗaliban makarantun gwamnati na kasa da na makarantun masu zaman kansu wajen ƙoƙari da kuma sakamakon jarabawa.
Wannan matsala ta daɗe tana jawo muhawara tsakanin iyaye, malamai da hukumomin ilimi.
Wasu na ganin matsaloli ne da ba za su rasa nasaba da rashin kulawa da watsi da harkar ilimi da gwamnati ta yi ba.
Ko wadanne dalilai ne suka daliban makarantun masu zaman kansu suka fi kokari idan aka kwatanta da daliban makarantu na gwamnati?
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyyaWannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan