Aminiya:
2025-09-17@20:28:27 GMT

Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano

Published: 17th, September 2025 GMT

Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano.

Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman.

Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono

Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar.

“Mun fara wannan shiri fiye da shekara guda da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai. Yanzu mun zo nan don fara na ɓangaren jarirai. Mu za mu biya kudin kulawar gaggawar yaran sannan mu tabbatar an kula da su har su samu ingantacciyar lafiya,” in ji Dr. Sikiru.

Ya kuma ce a karkashin shirin, yara da ke fama da matsalolin gaggawa kamar rashin numfashi, amosanin jini, cutar shawara da yaran da aka haifa bakwaini da ma cututtukan da ke buƙatar tiyata za su samu kulawa kyauta.

Ya ce asibitoci za su fara ba da kulawa da zarar an kawo yara, sannan su tura adadin kuɗin kula da yaran a kowanne mako ga NHIA don a biya su.

Daraktan ya kara da cewa duk yaran da ya sami kulawar gaggawar kuma, za a saka shi cikin shirin inshorar lafiya na NHIS, inda hukumar za ta ci gaba da biyan kudin inshorar don tabbatar da samun kulawar lafiya mai inganci.

“Kafin yaro ya ci gajiyar shirin, dole ne a tantance shi a a tabbatar yana da rauni da kuma ba zai iya biyan kuɗin asibiti ba. Haka nan dole ne yaro ya mallaki Lambar Shaida ta Kasa (NIN) don tabbatar da gaskiya da shigar da su cikin tsarin,” in ji shi.

Dr. Sikiru ya kuma ce, “Shiri ne kula da marasa lafiya cikin gaggawan. Da zarar sun zo, za a duba su. Asibitin sai ya turo mana jimillar adadin kudin, mu kuma mu biya.”

Ya ce wannan shiri wani bangare ne na kudurin gwamnatin tarayya na rage mace-macen jarirai da tabbatar da cewa babu yaron da ya rasa kulawar asibiti saboda rashin kudi.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo

An garzaya da ita asibiti, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

’Yansanda sun kama Bosede kuma suna bincike a kan lamarin.

Kakakin rundunar, DSP Olusola Ayanlade, ya ce za su tabbatar da adalci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCO
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta
  • KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano
  • Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki