Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano
Published: 6th, October 2025 GMT
Wata Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin a tura Ashiru Idris, wanda aka fi sani da Mai Wushirya, gidan gyaran hali na tsawon mako biyu saboda wallafa bidiyon batsa da ya shafi budurwa (dwarf) da ba a bayyana sunanta ba, a dandalin sada zumunta.
Mai shari’a Halima Wali ta Kotun Majistare mai lamba 7 ce ta bayar da wannan umarni, tana mai cewa a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali kafin a dawo da ƙarar don ci gaba da sauraro.
Hukumar kula finafinai da ɗab’i ta jihar Kano ce ta kama Mai Wushirya makon da ya gabata bayan da wasu bidiyoyi na rashin kunya suka yaɗu a intanet, inda aka gan shi ba tare da riga ba yana aikata abin da hukumomi suka bayyana a matsayin “abin kunya da rashin mutunci.”
Mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya ce kotu ta umarci a kawo matar da ta fito a cikin bidiyon kafin a ci gaba da shari’ar, yana mai bayyana cewa hukumar ta samu rahoton cewa matar ta gudu zuwa Jihar Zamfara, amma ana ci gaba da ƙoƙarin dawo da ita zuwa Kano domin ta fuskanci shari’a tare da Mai Wushirya.
Tags: 'Yan Matan tiktokMai wushiryaTikTokShareTweetSendShareকীওয়ার্ড: Yan Matan tiktok Mai wushirya
এছাড়াও পড়ুন:
Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
’Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Mata, Super Falcons, sun yi barazanar ƙaurace wa wasannin sada zumunta da Najeriya za ta buga a watan Disamba mai kamawa.
’Yan wasan sun ce za su ƙaurace wa wasannin ne idan har Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ci gaba da jinkirta biyan kuɗaɗen alawus-alawus da suke biyo tun na Gasar Olympics da aka yi a birnin Paris a 2024.
Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaroWasu majiyoyi daga ƙungiyar sun tabbatar cewa ’yan wasan na ci gaba da jiran a biya su haƙƙoƙinsu na wasannin da suka buga, ciki har da alawus na nasarar da suka samu a gasar Olympics, duk da cewa Najeriya ta fice tun a matakin rukuni bayan shan kashi a hannun Brazil da Spain da Japan.
Wani jami’in tawagar, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce ’yan wasan gaba ɗaya sun amince cewa ba za su halarci kowanne wasa ba muddin ba a biya su haƙƙoƙinsu ba.
Ana sa ran Najeriya za ta buga jerin wasannin sada zumunta daga ranar 2 zuwa 10 ga watan Disamba, a wani ɓangare na shirye-shiryen Super Falcons domin tunkarar gasar cin Kofin Afrika ta Mata na 2026.
A halin yanzu, NFF ba ta fitar da jerin sunayen ’yan wasan da za su wakilci Najeriya a wasannin ba.