Daga cikin wadannan alkaluman na yara miliyan 1.65 sun kasance suna a jihohin Zamfara, Bauchi, Sokoto, Borno, Kebbi, Kano, da kuma wadanda kuma suke a jihohin da Kungiyar ta MSF ke gudanar da ayyukanta kuma jihohin da ke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro.

Bugu da kari, akasarin kungiyoyi, sun yi ittifakin cewa, batun kula da lafiya, abu ne, da ya kamata matan Gwamatin uku na kasar, su bayyana dokar ta baci a kai.

Wannan rashin ayyana dokar ta bacin a fannin, mussaman a Arewacun Nijeriya, za a iya cewa, babbar gazawar rashin iya gudanar da shugabanci na gari ne, inda a Katsina irin wannan sakacin, mussaman na gazar samar wa yaran abinci mai gina jiki, ya bayyana karar a bangaren Gwamatin Jihar Katsina.

Koda yake dai, kalubalen rashin tsaro ya janyo tarwatsa dubban almumomu daga matsugansu, inda hakan ya haifar da katsewar samun abinci, hakan kuma ya jefa ruwarsu a cikin yunwa da kamuwa da cututtuka, wanda hakan ya kuma nuna rashin daukar kwararan matakai, daga bangaren Gwamnati. Hakazalika, abin damuwa ne na rashin daukar mataki a bangaren kula da kiwon lafiaykasa ‘yan kasa, inda mahukuntan kasar suke ganin yin hakan, tamkar wata taimaka wa ce, ba ta dole ba, wanda hakan ke ci gaba da jefa ‘yan kasar a cikin kangin yunwa, mussaman kananan yara da hakan ke janyo mutuwarsu.

Wasu Gwamnonin Arewacin kasar, maimakon su mayar da hankalansu wajen sauke nauyin alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe, mussaman na kare rayuka alumominsu da inganta rasuwarsu, amma sun buge wajen kawai daga darajar siyasarsu.

Bugu da kari, kudaden da ya kamata Gwamnonin Arewacin kasar, su yi amafni da suyinmin inganta rasuwar alumominsu, ana karkatar da su, wajen yin wasu manyan gine-gine domin kawai Gwamnonin su ce sun yi wani aiki da tarihi zai rinka tunawa da su, bayan sun bar karagar mulki.

Hakazalika, dakunan shan magani da ke a karkara, an bar su Kara zube, ba kayan aiki, tare da kin biyan ma’aikatan kula da kiwon lafiya da ke a yankuna albashinsu, haka suma Malaman Makaranta, inda kuma masu kirkiro da dokoki, suka yi watsi da samar da tsare-tsaren kula da Makarantun Gwamnati.

Abin bakin ciki ne, kan yadda yara ke mutuwa saboda matsalar abinci mai gina jiki, wanda wannan abun, za a iya dakle hakan, inda wasu Gwamnatocin jihohin, da ke Arewa, suka mayar da hankulansu, wajen gina manyan Gadoji, hakan ya nuna azahiri, iri na gazawar Gwamnatocin.

Irin wannan nuna halin na ko in kula, ya nuna yadda ake gudanar da ayyuka, a inda ba su kamata ba.

Nijeriya na samun dimbin kason kudade na shiga daga Gwamnatin Tarayya da wanda masu bayar da tallafi daga kasashen duniya ke bayar wa, musamman a karkashin shiye-shiyen kula da lafiyar jama’a da kuma wanda ake bayar wa ga bangaren ilimin zamani, amma duk da hakan, a jihohin Arewa, ana ci gaba da samun karancin kula da lafiyar yara da karuwar jahilic da mutuwar mata masu juna biyu da kuma rashin samun abinci, mai gina jikin yara.

Duk irin yawon da wadannan kudaden ke yi a zahiri, amma ana ci gaba da samun mutuwar, musamman yaran.

Wannan ya nuna yadda kawai, bangaren shugabanci, ya mayar da hankali wajen biyan ra’ayoyin wasu ‘yan tsiraru, da ake gani sune, dattijan kasa, inda su kuma talakawa kula da ta su rayuwar, ya zama ta jeka na yi ka.

A irin wadannan jihohin, talauci ya yi kakatutu, kuma wasu masu rike da madafun iko a johohin, garkame kawunansu a cikin daki, su dauki matakan da suka ga dama kawai kan alumominsu.

Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen daukar matakin, duk da tallafin da take samu daga kungiyoyin jin kai na ketare.

Bugu da kari, babu wasu kwararan matakai da aka dauka na adana hatsi a Rumbunan Gwamnatin domin shirin ko ta kwana, na yakar yunwa, musamman na samar da abinci, mai gina jiki.

Wannan Jaridar ta yi amanna da cewa, yanzu lokaci ne, da ya wajaba a faraga ba wai kawai batu na fatar baki ba, musamman duba da cewa, annobar ta mutuwar yara a jihar .Katsina abu ne, da ya kamata a dauki matakin gaggawa.

Dole ne, Gwamnatin Tarayya, ta ayyana dokar ta baci kan samar da abinci mai gina jiki, musamman a yakin Arewa Maso Yamma, musamman wajen yin aiki kafada da kafada da Gwamnatocin jihohi, ta hanyar tabbatar da yi gaskiya na samar da dauki.

Kazalika, ya wajaba a rinka binckar kudaden da aka warewa domin kashewa fannin kula da kiwon lafiya da samar da abinci mai gina jiki, kamar a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, da sauransu.

Ya zama wajibi mu kawo karshen yin tumasanci kan kasafin kudaden da jihohi suka warewa fannoninsu, amma daga baya, a karkatar da kasafin, wajen yin wani abu na da ban.

Dole ne shiye-shiyen zuba jari a fannin kula da kiwon lafiyar yara, ya kai ga yaran, musamman yara masu shekaru kasa da biyar da haihuwa.

Kazalika, lokaci ya yi, musamman a Arwa da Sarakuna za su rinka rufe bakunansu su yi gum, kan gudanar da abubuwan da ba su dace ba.

Tabbas, lamarin na Katsina, abu ne, da ke bukatar tausayawa da yin adalaci, domin, ba za sabu mu ci gaba da ganin ana barin ‘ya’yanmu, a cikin yunwa ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yara

এছাড়াও পড়ুন:

Za’a Fara tattaunawar Kasa Dangane Da Talauci da Kuma Rashin Adalci A Rabin Arziki A kasar

Gwamnatin kasar Afirka ta kudu zata fara tattaunawar kasa dangane da talauci da kuma rashin adalci a rabon arziki a kasar.

Gwamnatin kasar ta ware kimani dalar Amurka miliyon 40$ don gudanar da tattaunawar. Inda ake saran dukkan mutanen Afrika ta kudu suna da damar bayyana ra’ayinsu dangane da wadannan matsaloli. Na talauci da rashin adalci a rabon arzikin kasar.

Ana fatan masana daga ciki da wajen kasar zasu gabatar da ra’ayinsu ta shafukan sadarwan da za’a samar a cikin taron.

A halin yanzu fiye da shekaru 30 kenan da fita karkashin mulkin wariya na launin fata tsiraru a kasar, amma har yanzun kasar tana fama da matsalolin talauci, rashin aikin yi aikata laifuka da sauransu.

Mutane da dama suna ganin ba abinda taron zai amfana. Amma shugaba Cyrel Ramamposa ya bayyana shirin taron tun watan yunin da ya gabata. Yana kuma ganin, a cikin ra’ayoyin da za’a tattara mai yuwa a sami mafita daga.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’ August 14, 2025 Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’ August 14, 2025 Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara August 14, 2025 Hizbullahi Ta Yaba Wa Iran Kan Irin Gudumawarta Ga Lebanon Da Gwagwarmaya August 14, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Fatali Da Batun Kafa Gwamnatin Hadaka A Kasar Sudan August 14, 2025 Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon August 14, 2025 Masar ta yi Allawadai da furucin Netanyahu kan shirin kafa Isra’ila Babba August 14, 2025 Hamas ta aike da sakon jinjina ga al’ummar Yemen kan goyon bayan Gaza August 14, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129 August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bayan Gargadi Daga Gwamnatin Tarayya: Jihohin Arewa 15 Sun Fara Daukar Matakan Dakile Ambaliyar Ruwa
  • Za’a Fara tattaunawar Kasa Dangane Da Talauci da Kuma Rashin Adalci A Rabin Arziki A kasar
  • ‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Za Su Gudanar Da Zagaye Na 3 Na Aiki A Wajen Cibiyar Binciken Sararin Samaniya Ta Sin
  • Farfado Da Karkarar Sin: Canjin Gaisuwa Daga “Shin Ka Ci Abinci?” Zuwa “Yaya Rayuwarka A Gari?”
  • Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan
  • Ranar Hausa ta duniya: Za a yi gagarumin biki a fadar Sarkin Daura
  • DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya
  • Ministocin Harkokin Wajen Kasashe 27 Ne Sun Bukaci HKI Ta Kawo Karshen Hana Abinci Shiga Gaza
  • Ministan Harkokin Wajen Iraki Ya Bukaci Zaman Tattaunawa Tsakanin Kungiyar Larabawan Yankin Tekun Gulf Da Iraki Da Kuma Iran