Yara 4 da wasu mutum 8 sun rasu a hatsarin mota a Imo
Published: 11th, September 2025 GMT
Aƙalla mutum 12; ciki har da yara huɗu ne suka rasu a wani hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Owerri zuwa Onitsha da ke Jihar Imo.
Hatsarin ya auku ne lokacin da wata tankar gas mai lamba T 16716 LA, mai ɗauke da rubutun NUPENG, ta ƙwace daga kan hannunta ta afka wa wata motar fasinja.
Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinciMotar na ɗauke da mambobin Ikklisin Jehovah’s Witness daga Jihar Anambra zuwa ƙauyen Agwa da ke Jihar Imo.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da mutuwar manyan mutane takwas da wasu yara huɗu, yayin da wasu takwas suka jikkata.
An kai mamatan a ɗakin ajiyar gawarwaki na Ogbaku Mortuary, yayin da aka kwantar da waɗanda suka jikkata a Asibitin Divine Hospital Awo-Omamma.
Okoye, ya ce an fara bincike gano musababbin aukuwar hatsarin.
Ya ce tuni aka buɗe hanyar, yayin da jama’a suka ci gaba da zirga-zirga.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin mota Manya Owerri yara
এছাড়াও পড়ুন:
An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA