Matan da yara 95,000 ke mutuwa a sanadin shaƙar hayaƙin girki — UwargidanFubara
Published: 5th, October 2025 GMT
Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki.
Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya.
Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta uku mafi yawa a Najeriya, bayan zazzabin cizon sauro da cuta mai karya garkuwar jiki.
Ta kuma jaddada cewa amfani da itace wajen girki na lalata muhalli, domin hayaƙin yana sakin wani sinadari wanda ke haddasa ɗumamar yanayi.
A yayin taron, an raba tukwanen girki 200 don rage yawaitar hayaƙi, domin ƙarfafa wa mutane guiwa su koma amfani da hanyoyin girki masu tsafta.
Uwargida Otu, ta ce tukwanen suna rage yawan itacen da ake ƙonawa, kuma rage hayaƙin da ke shafar lafiyar mata da yara.
Shi ma Mista Oden Ewa, shugaban Hukumar Green Economy Commission, ya yi magana a taron, inda ya ce miliyoyin gidaje a Najeriya har yanzu sun dogaro da itace wajen girki, wanda hakan ke haddasa cututtuka.
Ya bayyana cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta ce hayaƙin cikin gida na ɗaya daga cikin manyan dalilan mutuwa barkatai musamman a ƙasashe masu tasowa.
Wannan shiri, a cewarsa, na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na kare muhalli, rage hatsarin kamuwa da cuta, da kuma inganta amfani da fasahohin makamashi aNajeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fatakwal Hayaƙi Mutuwa Uwargidan Fubara
এছাড়াও পড়ুন:
Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101.
Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban AmurkaA cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi.
Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito da hikima. A matsayinsa na mai wa’azi kuma babban mai fassarar Alƙur’ani mai tsarki, ya kasance mai kira ga zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.
Ya tuna da albarka da ya samu daga marigayin a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023.
Shugaban Ƙasa ya miƙa ta’aziyya ga almajiran malamin a faɗin Najeriya da wajen ƙasar, yana mai kira da su dawwamar da sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, tsoron Allah da kyautatawa ɗan adam.