Shugaban Argentina ya nemi Netanyahu da ya jinkirta kai Ziyara kasar saboda fargabar boren jama’a
Published: 28th, September 2025 GMT
Shugaban kasar Argentina Javier Milei ya bukaci firaminista Benjamin Netanyahu da ya dage ziyarar da ya shirya kaiwa zuwa kasar Argentina gabanin zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, saboda hakan na iya kara cutar da farin jininsa da tuni ya ragu.
A cewar jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila, Netanyahu ya kasance yana shirye-shiryen tafiya zuwa Buenos Aires, amma Milei ya nemi ya jinkirta tafiyar.
Da cewa da cewa Milei sananne ne wajen nuna goyon bayan ido rufe ga “Isra’ila”, an ba da rahoton cewa shugaban na Argentina ya damu da cewa ziyarar Netanyahu za ta yi masa mummunar tasiri a siyasance.
Kasar Argentina dai na daga cikin kasashen da har yanzu suke da damar karbar Netanyahu, wanda kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ke nema ruwa a jallo bisa laifin aikata laifukan yaki a Falasdinu.
An zabi Milei, dan siyasa mai ra’ayin rikau, a matsayin shugaban kasa a shekarar 2023 bayan ya lashe kashi 55% na kuri’un da aka kada. Duk da haka tun daga lokacin farin jininsa ya fuskanci koma baya sakamakon kalubale na cikin gida.
A watan Agusta, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa lauyoyin kare hakkin dan Adam na Argentina sun shigar da kara a gaban kotun tarayya suna neman a kama Netanyahu idan ya shiga kasar.
Karar dai zargin shi da hannu wajen aikata laifin yaki da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da gangan ta hanyar saka su a cikin yunwa, da kuma laifukan cin zarafin bil’adama da suka hada da kisan kai, da kuma wasu ayyukan da ba su dace a kan dan dan adam ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Isra’ila Sun Kashe Sama Da Falasdinawa 77 A Gaza A Yau Kawai. September 27, 2025 An Gudanar Da Taron Cika Shekara 1 Da Shahadar Sayyid Nasrullah September 27, 2025 Yunkurin Jinkirta Dawo Da Takunkumi Kan Kasar Iran Bai Yi Nasara ba. September 27, 2025 Shugaban Hukumar IAEA Ya Ce Shirin Nukiliyar Iran Na Zaman Lafiya Ne September 27, 2025 Shugaban Majalisar Tsaron Kasar Iran Dr Ali Larijani Ya Isa Birnin Berut . September 27, 2025 Iran ta kira jakadunta daga Birtaniya, Faransa, da Jamus domin tuntuba September 27, 2025 MDD : Isra’ila na kai harin bam a Gaza kowane minti 8 ko 9 September 27, 2025 MSF ta dakatar da ayyukan birnin Gaza saboda hare-haren Isra’ila September 27, 2025 Amurka ta soke bizar shugaban Colombia bayan shiga gangamin goyon bayan Falasdinu a New York September 27, 2025 Amurka Tana Shirin Kai Wa Venezuela Hari September 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Byyana
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana dalilin da ya sa Iran ba za ta halarci taron na Sharm el-Sheikh ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana dangane da rashin halartar jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa taron na Sharm el-Sheikh cewa, ba za su iya tunkarar wadanda suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Iran da kuma ci gaba da yi musu barazana da kuma sanya musu takunkumi ba.
Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a dandalin X da sanyin safiyar yau litinin cewa: “Iran ta nuna matukar jin dadin ta ga gayyatar da shugaba Sisi ya yi wa Iran na halartar taron na Sharm el-Sheikh. Duk da Muradin Iran din na tattaunawa ta diflomasiyya, Araqchi ya ce shi ko shugaba Pezeshkian ba za su iya tunkarar wadanda suka kai wa al’ummar Iran hari da kuma ci gaba da yi mata barazana da kuma sanya mata takunkumi.”
Ya kara da cewa: Duk da haka, Iran tana maraba da duk wani shiri da zai kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza da kuma bukatar kai wa ga janye sojojin mamaya daga yankin.
Araqchi ya jaddada cewa: Falasdinawa suna da ‘yancin fahimtar ainihin hakkinsu na cin gashin kansu, kuma dukkan kasashe, fiye da kowane lokaci, suna da alhakin taimaka musu tare da goyon bayan wannan bukata ta doka da ta dace.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta October 13, 2025 Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 13, 2025 Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci