Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya.

 

A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.

 

Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan.

 

Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka farfaɗo da su gaba ɗaya za su sauya yanayin yaɗa shirye-shiryen rediyo na ƙasa, tare da sanya VON a matsayin gagarumar alama mai martaba a duniyar yaɗa labarai ta rediyo baki ɗaya.”

 

Ministan ya buƙaci kamfanin Confax Nigeria Limited da ke gudanar da kwangilar da ya tabbatar da inganci da kuma kammalawa a kan lokaci, inda ya ce: “Saboda haka ina kira ga ɗan kwangilar da ya tabbatar da ba wai kawai an kammala aikin a cikin lokacin da aka tsara ba, har ma a tabbatar da cewa an kiyaye mafi girman matakan inganci kuma hakan ya fito fili.”

 

Haka kuma ya umurci ma’aikatan da ke kula da na’urori a VON da su yi aiki da jajircewa da natsuwa wajen kula da wannan aikin.

 

Ya jaddada cewa ana sa ran gidan rediyon VON zai ci gaba da kiyaye manufar sa ta kasancewa gidan rediyo mai goyon bayan Nijeriya da Afrika baki ɗaya, tare da bayar da sahihan labarai na nasarorin da ke fitowa daga Nijeriya da nahiyar baki ɗaya.

 

A ƙarshe, Ministan ya ce: “Yanzu ina farin cikin ƙaddamar da kwangilar gyaran na’urar tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250.”

 

Shi dai VON, shi ne gidan rediyon da Gwamnatin Tarayya ta kafa domin bada labarai daga Nijeriya zuwa ƙasashen ƙetare, kwatankwacin gidan rediyon BBC da na Muryar Amurka.

 

An kafa shi a cikin 1961 a matsayin sashen labaran ƙetare na gidan rediyon NBC, wato wanda ya zama FRCN daga bisani. Firayim Minista na lokacin, Alhaji Sa Abubakar Tafawa Balewa, shi ne ya ƙaddamar da shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: yaɗa labarai

এছাড়াও পড়ুন:

Fursunan da aka yanke wa hukuncin kisa ya tsere daga gidan yari a Yobe

Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe.

Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar.

Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka

A cewar sanarwar, Abba Hassan, wanda asalinsa ɗa  Jihar Borno ne, ya gudu daga gidan yarin a ranar 31 ga watan Oktoba, bayan kotu ta yanke masa hukuncin kisa.

DSP Abdulkarim, ya roƙi jami’an tsaro, direbobi, sarakunan gargajiya, ’yan banga da al’ummomin Jihar Yobe da maƙwabtan jihohi da su taimaka da bayanai da za su taimaka wajen sake kama shi.

Ya kuma gargaɗi jama’a da kada su kusanci fursunan da ya tsere, domin hakan na iya zama hatsari.

“Domin kare lafiyarku, idan kuka ga wani da kuke zargi shi ne, ku sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa ko gidan gyaran hali, ko kuma ku kira lambar 08038452982,” in ji sanarwar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fursunan da aka yanke wa hukuncin kisa ya tsere daga gidan yari a Yobe
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar  Christopher Musa