2025-07-09@16:27:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2231

«Manajan Darakta»:

    Tsohon jigo a Jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya ce dole ADC ta tsayar da ɗan Arewa takara idan tana son ta kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Okonkwo, ya ce idan ADC ta tsayar da ɗan Kudu takara, Tinubu zai sake lashe zaɓe ba tare da wata tangarɗa ba. Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross Ya ce dole ne ’yan adawa su yi aiki da hikima da dabaru idan suna son yin nasara. “Shirina a wannan karon shi ne zan goyi bayan ɗan Arewa a 2027,”...
    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ta ƙara sanya wa ’yan Najeriya da ke son ziyartar Dubai sabbin sharuɗa. Haka kuma, ta dakatar da bayar da bizar wucin gadi ga ’yan Najeriya. Yara miliyan 5.4 na fama da karancin abinci a jihohin arewa 9 – Red Cross Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista Aminiya ta samu labarin cewa hukumomin shige da fice na Dubai ne suka bayar da umarnin sabbin matakan ga ofishin jakadancin ƙasar da ke Najeriya. Daga cikin sabbin dokokin, duk ɗan Najeriyar da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 45 ba zai samu bizar yawon buɗe ido ba sai idan zai yi tafiya tare da wani. Wannan na nufin cewa yawan ’yan Najeriya...
    Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce akwai yara akalla miliyan biyar da dubu 400 da ke fama da matsalar karancin abinci a jihohi tara na arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro. A cewar kungiyar, jihohin su ne‎ Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, Zamfara, Neja, Binuwai da kuma Kano. Mai rikon mukamin Darktan Lafiya da Kula na kungiyar Dr Aminu Abdullahi, shi ne ya bayyana hakan a yayin taron gangamin neman tallafi kan karancin abinci na kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma da ya gudanar a Kano ranar Talata. Kwanan nan gwamnati za ta sake kara kudin lantarki a Najeriya – Minista Masu ƙwacen waya sun kashe ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ghana a Abuja...
    Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa Iran ta kai hare-hare kan cibiyoyin sojojinta Wani jami’in sojan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci a ranar Talata cewa; Hare-haren da Iran ta kai a watan da ya gabata sun afkawa wuraren sojojin mamayar Isra’ila, matakin da tuni duniya ta amince da kai irin wadannan hare-hare kan cibiyoyin sojin mamaya. Jami’in da ke magana da kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ki bayar da karin bayani, ciki har da gano wuraren da abin ya shafa ko kuma irin barnar da harin ya yi ga kayayyakin aikin soja. Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama  marasa matuka ciki kan haramtacciyar kasar Isra’ila a watan da ya gabata...
    Ministan Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya ce Gwamnatin Tarayya na shirye-shiryen sake kara kudin wutar lantarki domin rage yawan bashin da bangaren lantarkin ke bi. Bayanai dai sun nuna yanzu haka, bashin lantarkin da ake bi a Najeriya ya haura Naira tiriliyan hudu. Amma a cewar ministan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki 300 a Abuja, yunkurin wani bangare ne na tabbatar da cewa bangaren lantarki ya tsaya da kafarsa. Matar tsohon Gwamnan Adamawa ta sauya sheka daga PDP zuwa ADC Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda Idan dai za a iya tunawa, duk da Karin kudin wutar da aka yi wa kwastomomin da ke tsarin Band A,...
    Jam’iyyar ADC ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu shugabanni daga yankin Kudu sun buƙaci Atiku Abubakar, da ka da ya fito takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce wannan labari ƙarya ne, wanda aka ƙirƙira don haddasa rikici , musamman a wannan lokaci da ake ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya. Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense Jam’iyyar ta ce: “Ba mu taɓa zama da wasu wakilai daga Kudu domin yin irin wannan magana ba. “Wannan rahoto ba kawai ƙarya ba ne, yana kuma...
    Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Ilorin ta kai wa daliban makaranta yakin da ta yi da cin hanci da rashawa domin fadakar da su illar cin hanci da rashawa.   Da yake jawabi ga dalibai a makarantar Nursery da Primary School, Tanke, Ilorin, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a, Daraktan Hukumar EFCC, Ayodele Babatunde, ya ilmantar da daliban a kan ma’anar cin hanci da rashawa, daban-daban da illolinsa da yadda kowa da kowa, ciki har da yara, za su iya bayar da tasu gudunmuwar wajen gina Nijeriya mara cin hanci da rashawa.   Ya ce cin hanci da rashawa yana yin abin da bai dace ba ne, musamman idan ya shafi wasu...
    Kungiyar Kano Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (Kano-ACReSAL) ta kaddamar da yakin neman ilimin sauyin yanayi zuwa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta ’Yan Mata da ke Kano a wani bangare na shirinta na “Catch Them Young”. Wato Ilmantar da Matasa.   Gangamin wayar da kan jama’a wani bangare ne na kashi na biyu na yunkurin aikin na jawo dalibai, malamai, da kwararrun muhalli wajen tattaunawa kan sauyin yanayi da kuma shigar da matasa wajen magance shi.   Mukaddashin mai kula da ayyukan, Dr. Abdulhamid Bala, ya sanar da daliban cewa sauyin yanayi ya kasance babban kalubalen da ba za a yi watsi da shi ba.     “Sauyin yanayi ya kasance barazana mai dorewa ga dorewar duniya. Amsarmu dole ne...
    Na Biya Bashin Garatutin Naira Biliyan 13.6 Da ’Yan Fanshon Zamfara Ke Bi Tun 2011, Inji Gwamna Lawal Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana jin daɗinsa na biyan bashin Naira Biliyan 13,944,039,204.64 da aka riƙe wa ’yan fansho a Zamfara tun daga shekarar 2011 zuwa 2023. A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin aiwatar da ayyukan fansho tare da karbar rahoto daga kwamitocin haɗin gwiwa kan biyan bashin kuɗaɗen garatuti da aka yi a gidan gwamnati da ke Gusau. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, warware tarin bashin kuɗaɗen guratuti da fansho da aka tara daga shekarar 2011 zuwa 2023 na ɗaya...
    Mai magana da yawun matatar Dangote, Mista Anthony Chiejina, ya tabbatar da rage farashin a Legas. Ya ce, “Farashin man fetur ya ragu daga Naira 840 zuwa Naira 820 kan kowace lita.” Ya bayyana cewa rage farashin da aka yi a baya zuwa Naira 840 ya faru ne sakamakon hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya sanadiyyar rikicin da ya auku a Gabas ta Tsakiya. Kamfanonin da ke haɗa kai da Dangote irin su MRS, Heyden, Ardova (AP), Hyde, Optima, da Techno Oil za su fara sayar da fetur a sabon farashin. Haka kuma, wasu sabbin kamfanonin da ke dillancin mai sun shiga jerin masu rarraba man Dangote. Kamfanonin sun haɗa da: TotalEnergies, Garima Petroleum, Sunbeth Energies, Sobaz Nigeria Ltd., Virgin...
    Wani babban jami’I a kungiyar Hamas ya bayyana cewa sojojin HKI sun kashe falasdinawa guda 6 a zirin gaza a ci gaba kissan kiyashin da takewa falasdinawa a yankin. Abdul-Karim Hanini, ya kara da cewa wadanda ta kashen tsoffin fursinoni a hannun yahudawan a shekarun da suka gaba 5 daga cikinsu an yi musayarsu ne a shekara 2011 a lokacinda aka yi musayarsu da fursinan yahudawan Galid Shalit a shekarar. Sannan dayan kuma an yi musayarsa ne a shekara ta 2002 wanda yahudawan suka kora daga Cocin Nativity daga birnin Bethlaham a yankin yamma da kogin Jordan. Abdul-Karim Hanini  ya kammala da cewa a dai dai lokacinda muke makokin yan’uwammu da yahudawan suka kai ga shahata, muna rokon All..ya karbi...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mai yiwuwa masu sauraro sun san wani bawan Allah wanda kusan a kullum, kuksan a ko yaushe a cikin nema yake, amma Allah bai kawo ba.. Wasu dai na ganin yawan fadi-tashin da mutum yakan yi ba shi ne zai ba shi kudaden da yake bukata ba, yayin da wasu suke ganin jajircewar mutum tana da nasaba da yawan abin da zai samu. NAJERIYA A YAU: Sarƙaƙiyar da ke gaban Haɗakar ADC: Atiku ko Peter Obi DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan kujiba-kujibar da mutane suke yi don samun arziki da tambayar ko zafin nema yana kawo samu? Domin...
    Idris ya ce: “Ko da yake muna jaddada ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na amfani da ‘yancin sa na shiga ko kafa ƙungiya da faɗar albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, yana da muhimmanci a fayyace cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta bari harkokin siyasa ko hayaniyar ‘yan siyasa su karkatar da ita daga aikin da ta sa a gaba ba.”   Ministan ya ce ko da yake ana ta raɗe-raɗi a kafafen yaɗa labarai game da sabuwar haɗakar siyasar adawa da ke tasowa, Shugaban Ƙasa Tinubu yana ci gaba da maida hankali ne kan Shirin Sabunta Fata domin ciyar da ƙasa gaba.   “Hayaniya a kafafen yaɗa labarai kan fitowar wata sabuwar haɗakar siyasa abin fahimta...
    Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta Nijeriya (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙanƙantar makin da za a bai wa ɗalibai guraben karatu a jami’o’in ƙasar. Hukumar ta ɗauki matakin ne a taronta kan tsarin bayar da guraben karatu na 2025 da ta gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja. An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a Kebbi Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC Haka kuma, ta ce mafi ƙanƙantar maki ga kwalejojin koyon aikin jinya shi ne 140, yayin da ta ƙayyade makin samun gurbin kwalejojin ilimi da na koyon aikin noma a 100. Alƙaluma dai sun tabbatar da cewa an samu gagarumar faɗuwa a jarawabar...
    Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila.   Yana...
    Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta. ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun. Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba. “Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta zargi kasar Amurka da nuna adawa da kungiyar BRICS ta raya tattalin arziki na kasashen kungiyar ta kuma kara da cewa kokarin kare kanta da ga shirye-shiryen BRICS ba zai amfane ta ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar China na cewa kungiyar kungiya ce wacce bata son babakere da Amurka take nunawa a yadda take tafiyar da al-amura a duniya kamar Ita ce, take iko da kowa. Tace kungiyar tana son duniya ta zama mai kudubobi, wadanda su ma za’a iya fada su kuma aikata abinda suke so karkashin dokokin duniya. Don haka mamayar da takardan dalar Amurka ta yiwa mafi yawan...
    ‎Wata ƙungiya mai zaman kanta, Nigeria Health Watch ta ce ta gano har yanzu fiye da rabin matan da ke zaune a yankunan karkarar Jihar Kano sun fi son haihuwa a gida a maimakon zuwa asibiti. ‎Kungiyar ta alaƙanta hakan da al’adun mutanen, waɗanda ta ce an fi samun masu su a ƙauyuka da kuma yankunan karkara fiye da a birane. ‎Daraktar shirye-shirye ta ƙungiyar, Kemisola Agbaoye ce ta bayyana hakan ranar Litinin, yayin gabatar da rahoto a wani taron masu ruwa da tsaki don bayyana abubuwan da suka gano a binciken da suka gudanar a ƙananan hukumomi shida na jihar. Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi...
    (ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu  Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
    (ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu  Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
    Kasar Sin ta gudanar da bikin cika shekaru 88, da dukkan al’ummar kasar ta fara yakin kin jinin harin sojojin Japan a yau Litinin. Inda a wani bangare na bikin aka kaddamar da wani baje koli mai taken “Domin ‘yantar da kasa da zaman lafiyar duniya”. An gudanar da bikin tare da baje kolin ne a babban dakin adana kayayyakin tarihi masu nasaba da yakin, wanda ke kusa da gadar Lugou, wadda kuma ake kira da “Marco Polo Bridge”, wurin da sojojin Japan suka fara kaiwa sojojin kasar Sin hari a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937, lamarin da ya zamo tushen mamayar da sojojin na Japan suka yiwa kasar Sin. Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS,...
    Kamfanin jirgin sama mallakar jihar Enugu, wato Enugu Air, ya fara aiki a hukumance ranar Litinin bayan ƙaddamar da shi a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu. Mutane da dama sun halarci bikin ƙaddamarwar tare da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da sauran manyan baki da suka halarci bikin ƙaddamarwar. APC Ta Tafka Asara, Wani Jigo Ya Fice A Enugu  Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu Enugu Air wani ɓangare ne na hangen nesa da ƙudurin Gwamna Peter Mbah, don inganta harkar sufuri da mayar da Enugu cibiyar jiragen sama a Nijeriya. Kamfanin ya fara aiki da jirage uku na Embraer E170 da E190, wadanda suka dace da zirga-zirgar cikin gida. Jirgin zai fara tashi tsakanin...
    Saboda matsin lamba na doka da kuma la’akari da mahimman batutuwan siyasa, ya zama dole Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da duk wani ci gaba na aikin kwamitin da aka kafa a ranar 4 ga Yuli 2025 domin duba yiwuwar ƙirƙirar sabbin masarautu ko sauye-sauye ga tsarin majalisun gargajiya—musamman a yankunan da har yanzu ke fuskantar shari’a a kotu. Ci gaba da wannan lamari mai sarkakiya alhali wasu muhimman ƙarar shari’a na ci gaba a kotuna, ba wai kawai zai saɓa wa kundin tsarin mulki da ikon shari’a ba, har ila yau, zai iya haddasa tayar da jijiyoyin wuya a cikin al’umma, musamman a yankunan da ke da tarihi na rikice-rikicen ƙabilanci kamar Tafawa Balewa da kewaye. Wannan kira na...
    Rahotanni sun bayyana cewa mazauna wasu jihohin Nijeriya uku na cikin shirin ko-ta-kwana, sakamakon ƙaruwar fargabar samun ambaliya saboda yiyuwar sakin ruwan Madatsar Lagdo ta Kamaru. A cewar wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, jihohin da mazauna ke cikin zaman ɗar-ɗar sun haɗar da Benuwe da Edo da kuma Bayelsa, waɗanda tuni suka fara shiri don kauce wa barazanar ambaliyar. Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos Sai dai Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Nijeriya ta yi watsi da rahotonnin da ke cewa an buɗe madatsar ruwan, a yayin da tuni jihohin suka fara shirya wa barazanar. Gwamnatin Benuwe ta ce ta fara aikin wayar da kan...
    An kashe mutane tara tare da jikkata wasu huɗu a wani da mayakan Boko Haram suka kai yankin a Malam Fatori da ke Jihar Borno. Gwamna Babagana Zulum, wanda baya kasar a halin yanzu, ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Sugun Mai Mele, domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa da kuma tantance halin da ake ciki. Mai Mele ya jaddada aniyar Gwamna Zulum na jajircewa wajen tabbatar da tsaron Malam Fatori saboda muhimmancinsa. Ya sanar da shirin tura manyan injina domin tona ramuka a kusa da hedikwatar ƙaramar hukumar don hana hare-hare nan gaba daga Boko Haram da ISWAP. Turji: Sai ka sako mutanen da ka sace za a yi sulhu — Gwamnatin Sakkwato Sarkin Ibadan ya...
    A taron ƙungiyar BRICS na karo na 17 da aka gudanar a Brazil, ƙasashen mambobi da suka haɗa da China, India, Rasha, Saudi Arabia, Iran da wasu sun soki hauhawar haraji da manufofin kariya ta ciniki da wasu ƙasashe ke aiwatarwa. A sanarwar da suka fitar, sun nuna damuwa kan rikicin Gabas ta Tsakiya, amma sun kaucewa sukar Rasha kai tsaye dangane da rikicin Ukraine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari da safiyar Litinin a unguwar Ogaminana da ke ƙaramar hukumar Adavi a Jihar Kogi, inda suka kashe wani Soja ɗaya da aka tura domin bayar da kariya ga ma’aikatan kamfanin gine-gine. Wata majiya daga yankin ta shaida wa LEADERSHIP cewa maharan sun mamaye wurin aikin ne da safe, inda suka yi awon gaba da wani ɗan ƙasar China da ke aiki a wurin. An bayyana cewa bayan harin, maharan sun ajiye motarsu a kusa da tashar watsa shirye-shiryen Radio Kogi da ke Otite, da nisan ‘yan mitoci kaɗan daga inda suka sace ɗan Chinan. CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa Fursunoni 58 suna rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa NECO ta shekarar 2025. Wannan ci gaba ya samu ne bayan biyan kudin rajista da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Kofar-Nasarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano. Ya ce wannan karamci na gwamnatin jihar Kano shaida ce ta jajircewarta wajen kula da walwalar fursunoni, gyaran dabi’unsu da kuma dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata. “Biyan kudin rajistar jarrabawa da gwamnatin Kano ta yi alama ce ta jajircewarta wajen samar da dama ga fursunoni domin su...
    Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu, yana da shekara 90 a duniya. Kakakin iyalan basaraken ne ya tabbatar da mutuwarsa da safiyar yau Litinin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai. Kwanaki biyu da suka gabata ne basaraken ya gudanar da bikin cikarsa shekara 90 a duniya a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a fadarsa. A shekarar da ta gabata ne aka naɗa Sarki Olakulehin a matsayin Olubadan na Ibadan bayan rasuwar wanda ya gabace shi Sarki Alli Okunmade II.
    An kashe mutane tara tare da jikkata wasu huɗu a wani da mayakan Boko Haram suka kai yankin a Malam Fatori da ke Jihar Borno. Gwamna Babagana Zulum, wanda baya kasar a halin yanzu, ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Sugun Mai Mele, domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa da kuma tantance halin da ake ciki. Mai Mele ya jaddada aniyar Gwamna Zulum na jajircewa wajen tabbatar da tsaron Malam Fatori saboda muhimmancinsa. Ya sanar da shirin tura manyan injina domin tona ramuka a kusa da hedikwatar ƙaramar hukumar don hana hare-hare nan gaba daga Boko Haram da ISWAP. Turji: Sai ka sako mutanen da ka sace za a yi sulhu — Gwamnatin Sakkwato Sarkin Ibadan ya...
    Wani malamin addinin musulunci a jihar Zamfara, Sheikh Mohammed Tukur Sani Jangebe, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara da su gaggauta gudanar da kananan gyare-gyare daga mahadar Maru –Mayanchi – Maradun, da ke kan hanyar zuwa wani yanki na karamar hukumar Talata Mafara.   Ya ce mummunan yanayin hanyar yana ci gaba da haifar da babban kalubale ga matafiya tare da fallasa su ga hare-haren ‘yan bindiga a kan hanyar.   Sheikh Jangebe ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon Najeriya a Gusau babban birnin jihar Zamfara.   Ya bayyana cewa babbar hanyar Maru zuwa Talata Mafara ta samar da ramuka sama da dari, wadanda ke hana zirga-zirgar ababen...
    Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) a jihar Kano ta ce ta samu rahoton laifuka 351 na take hakkin yara daga cikin jimillar kararraki 446 da ta samu daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025.   Kodinetan NHRC na jihar Kano Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a Kano.   Ya bayyana cewa daga cikin jimillar korafe-korafe 446 da aka samu a cikin watanni uku 351 na da alaka da take hakkin yara.   Ko’odinetan jihar ya yi nuni da cewa, sauran shari’o’in sun hada da tashin hankalin gida 19, 18 da suka shafi ‘yancin tattalin arziki da zamantakewa, da kuma biyar da suka shafi ‘yancin rayuwa.     “cikin zarge zargen har na Maita da sauran shari’o’in da...
    A wani yunkuri na bunkasa samar da wutar lantarki da kuma bunkasar tattalin arziki, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kashi na farko na taransfoma 500 ga al’ummomin karkara a fadin kananan hukumomin jihar 44.   Gwamna Abba Yusuf ne ya kaddamar da shi a hukumance a Kano a wani shirin da nufin magance kalubalen rashin samar da wutar lantarki.   Gwamna Yusuf ya ce samar da taransfoma wani shiri ne na bunkasa masana’antu da zaburar da harkokin kasuwanci musamman a yankunan karkara.   “Wannan rabon shi ne kashi na farko na aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara, ba wai kawai wani aikin samar da wutar lantarki ba ne, wani muhimmin mataki ne na inganta samar da...
    Allah Ya yi wa Sarkin Ibadan, waro Olubadan, Oba Owolabi Olakulehin, rasuwa. Shaidu sun bayyana cewa Oba Owolabi Olakulehin ya koma ga Mahaliccinsa ne a safiyar ranar Litinin ɗin, 7 ga watan Yuli, 2025. Ya rasu ne yana da shekaru 90 a duniya.
    Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma da kuma masu sun yenci a ko ina suke. Ya kuma yaba da yadda gikuwan nmalamai na kasar Iran suka sami nasarar kare kasar daga mafi yawan hare-haren  HKI a kan kasar. Ya bayyana cewa Iran ta sami nasara a kan kasashen yamma da makamai wadanda suka fi nasu karfi da inganci, har’ila yau sun sami nasara a kan ma;aikatan yahudawan da suke taimaka masu...
    Miliyoyin yan Najeriya ne suka gudanar da tattakin Ashoora a birne daban daban a kasar a jiya Lahadi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, da farko ya nakalto daruwan da suka fito tattakin na Ashoora a Abuja babban birnin kasar a safiyar jiya Lahadi. A wannan karon dai masu tattakin Ashoora a Abuja sun fito ba tare da sanya bakaken kaya ba saboda kaucewa rikici da kuma kamu daga Jami’an tsaro a birnin, kamar yadda suka sabayi a shekarun da suka gabata. Labarin ya kara da cewa an gudanar da irin wannan tattakin na Ashoora a garurwa kimai 25 a duk fadin kasar, kuma an kammala ba tare da wata matsala ba. An gudanar da tattaki a jihar Bauchi...
    Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba. A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe  kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.
    Zalum ya kuma shawarci gidajen jaridu da su dinga tantance labarai kafin su yaɗa shi domin kaucewa labaran ƙanzon kuregen da wasu suke yaɗawa. A ƙarshe gwamnan ya ce ya duƙufa wajen hidimtawa al’ummar jihar Borno a ƙarƙashin jam’iyar mai albarka ta APC . Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gargaɗi sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar kan zargin hannu a mamaye hanyoyin kiwo da filayen kiwo, abin da ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnan ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu sarakuna na karɓar cin hanci suna kuma ba da damar shiga filayen kiwo ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ke ƙara tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umma. Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka “Duk wanda aka kama yana da hannu a wannan aika-aikar, za mu hukunta shi bisa doka,” in ji Gwamna. Ya kuma roƙi makiyaya da su guji shiga gonaki domin...
    Babban Mufti na masarautar Oman ya yi kakkausar suka kan kasashen da ke neman kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu kasashe ke son kulla                     alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, wata kasa ‘yar mamaya maras tushe. A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmed bin Hamad Al-Khalili ya ce: “Abin mamaki ne yadda wasu kasashe ke son kyautata alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, alhali su kansu suna kallon wannan mahalukiya a matsayin wata kasa mai gushewa ko ba dade ko ba jima, al’ummarta dai suna son ci gaba da yakin ne kawai don ci gaba da wanzuwarta, in ba haka ba,...
    A ranar Asabar, ƙungiyar PSG ta doke Bayer Munich da ci 2-0 a wasan zagayen kusa da na ƙarshe na gasar Kofin Duniya na Kungiyoyi, wanda aka buga a filin wasa na Mercedes Benz, Atlanta, Amurka. Duk da samun katin kora guda biyu, PSG ta nuna kwarewa da jajircewa wajen zura ƙwallaye masu kyau a raga. A wani wasa da aka buga a daren ranar Asabar a filin wasa na MetLife Stadium, New Jersey, Real Madrid ta doke Borussia Dortmund da ci 3-2. Madrid ta fara da ƙwallaye biyu daga Gonzalo Garcia da Fran Garcia, kafin Dortmund ta yi ƙoƙarin dawo da wasan. Kylian Mbappé ya ƙara wa Madrid ƙwallo ta uku da kyakkyawan bugun watsiya, sai dai Dortmund ta...
    Rashford dai ya fi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona domin yana ganin zai iya buga abin a zo a gani a kakar wasa mai zuwa sai dai ita kuma Barcelona ta fi son dan wasa Nico Williams na kungiyar Athletico Bilbao ta kasar Spaniya, wanda shima yake son komawa Bardelona da buga wasa idan har Barcelonan za ta iya biyan kudin da aka yi masa farashi. Kungiya ta kwana-kwanan nan da ta nemi Rashford ita ce kungiyar Bayern Munchen ta Jamus, bayan da Liberpool ta ce ba za ta sayar mata da Luiz Diaz ba, ana ganin yanzu kungiyar za ta karkata akalarta zuwa neman Rashford. Kungiyoyi irinsu Newcastle United da Tottenham da kungiyoyi daga Saudiyya duka sun...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da ci gaba da riki jami’an diblomasiyyar kasar 4 wanda HKI take yi tun shekaru 43 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar tana fadar haka a wata sanarwa da ta fitar shekaru 43 cur da sacewar wadanda Jami’an diblomasiyyar kasar a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ranar 4 ga watan Yuli n shekara 1982. Jami’an diblomasiyyar suna ne Seyed Mohsen Mousavi, Ahmad Motevaselian, Kazem Akhavan, and Taghi Rastegar Moghadam, wadanda wata kungiyar yar ta’adda wacce HKI take goyon bayanta ta kamasu ta kuma mikawa HKI a lokacinda take mamayae da kasar Lebanon. Rahoton ya yabawa gwamnatin kasar Lebanon kan hadin...
      Rukunin farko: Morocco da Zambiya da Senegal da kuma Jamhuriyar Congo Rukuni na biyu: Nijeriya da Tunisia da Algeria da kuma Botswana. Rukuni na uku: Afirka ta Kudu da Ghana da Mali da kuma Tanzania. Bayan karawar bude labulen gasar, akalla za a rika buga wasanni bibiyu kowacce rana a fafatawar cikin rukuni har zuwa ranar Litinin 14 ga watan Yuli. Sannan a lokacin wasannin cikin rukuni za ake buga su daga 13:00 da 16:00 da kuma19:00 daidai da agogon GMT. Za a fara karawar zagaye na biyu daga ranar Juma’a 18 ga watan Yuli. Shekara ukun da ta gabata, Morocco ta gudanar da gasar cin kofin Afirka ta mata, kuma filaye ukun da ta yi amfani da su,...
    Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya tunasar da karamar hukumar Roni game da bukatar gina wani rukuni mai dauke da ajujuwa guda biyu ga makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya domin inganta rayuwar su. Shugaban kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki biyu da kwamatin ya yi a karamar hukumar Roni. Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce tanadin gina ajujuwan ga makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya na kunshe cikin kasafin kudin kananan hukumomi. Ya kuma bayyana gamsuwa da bin kyakkyawan tsarin sadarwa tsakanin bangaren zartaswa da na kamsiloli ta yadda bangaren kamsiloli ya nemi bayani kan jerin ayyukan raya kasa da karamar hukumar ta...
    Wasu ƙungiyoyin mata a ƙauyukan Bendeghe-Ekiem da Abiya da ke Ƙaramar Hukumar Etung, a Jihar Kuros Riba, sun yi  barazanar gudanar da zanga-zangar tsirara idan gwamnati ba ta janye ƙudirin sayar da gonakin koko ba. Matan sun ce wannan shawara da gwamnati ta ɗauka ba su aminta da ita ba, domin gonakin koko su ne tushen rayuwarsu, wanda da su suke cin abinci, suke biya wa ’ya’yansu kuɗin makaranta. Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano Aminiya ta samu rahoton cewa gwamnati na shirin sayar da hannun jarinta a wasu manyan gonakin koko da ke wannan yanki, wanda hakan ya fusata matan da sauran al’ummar ƙauyukan da...
    Jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2023, ba zai tsaya takara a 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dokta Agbo Major, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya mayar da martani kan wata magana da Buba Galadima ya yi. Tinubu ko ɗansa zai naɗa shugaban INEC, APC sai ta faɗi zaɓen 2027 — Dalung Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya na siyan abincin da ya lalace Galadima, ya ce har yanzu Kwankwaso yana cikin NNPP kuma zai tsaya takara a 2027. Galadima ya shaida wa manema labarai cewa: “Babu wani tabbaci da ke nuna cewa Kwankwaso yana shirin komawa APC. Za mu ci gaba da zama a...
    Kungiyar Kananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) reshen Jihar Kaduna, ta mika sakon taya murna ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa lambar karramawa ta CON da shugaban kasa ya yi masa ado da ita, wacce ke matsayin wata alamar girmamawa a Jamhuriyyar Nijeriya ta Hudu. Wannan karramawar, wata alama ce a sarari ga sadaukarwar mai girma gwamna, da gagarumin nasarorin da ya samu a hukumance, da kuma jagoranci mai tsari da yake kai domin ci gaba da tsara tafiyar dimokuradiyyar kasa. Dalilin Kwararru Na Bukatar Kafa Cibiyoyin Bincike Kan Nau’ikan Dabbobi A Nijeriya Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8) Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda dauke da sa hannun sakataren yada labarai...
    “Wannan aiki ne, wanda za a iya cewa; tamkar a yanzu ne muka fara dora damba a kansa”, a cewar shugaban. Haka zalika, shugaban ya kuma sanar da wadanda suka halaccin taron kaddamar da shirin tabbacin cewa; wadannan ayyuka na noman zamani, za su kara taimakawa wajen kara samar da ayyuka a fannin aikin noma sama da 2,000. Ya ci gaba da cewa, kayan za su kuma taimaka wajen kara ayyukan masana’antun kasar da samar da damar gudanar da yin bita da kuma kwararrun kayan aikin noma 9,000. Shugaban ya jaddada muhimmancin yin amfani da kayan aikin noma na zamani, wanda hakan zai taimaka wa manoman wannan kasa. Har ila yau, ya kuma yi nuni da cewa; kaddamar da wannan...
    An fara tuhumar tsohon ɗan ƙwallon Arsenal, Thomas Partey da laifuka biyar da suka haɗa da fyaɗe da kuma cin zarafi, an bayar da rahoton cewa ya aikata laifukan ne a tsakanin shekarar 2021-2022, cewar ‘yansandan Birtaniyya. Daga cikin laifukan akwai fyaɗe akan wasu mata uku waɗanda ake tuhumarsa da cin zarafinsu ta hanyar tursasawa kan mace ta farko da ta biyu sai kuma laifin lalata da mace ta uku. ‘Yansanda a ƙasar Birtaniya sun ce ya kamata Thomas ya bayyana a Kotun Majistare ta Westminster a ranar 5 ga watan Agusta, tuhumar ta biyo bayan binciken da jami’an tsaro suka gudanar, wanda ya fara a watan Fabrairun 2022 bayan da ‘yansanda sun samu rahoton fyaɗen. Partey dai ya bar...
    Miliyoyin Iraniyawa a ranar 8 ga watan muharram sun fito sanye da bakaken kaya da tunawa a bubuwan da suka faru a ranar kwanakin Asoora inda aka kashe Imam Hussain (a) jikan manzon All… Banda wannan raya kwanakin Ashoora ci gaba ne da nuna turjiya da kuma saukar da kai kan azzaluman shuwagabanni ko da ba tare da samun nasara a zahiri ba kuma nan kusa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taturrukan Ashoora a duk fadin Iran, kuma a yau Tasoo’a za’a ci gaba da fitowa har zuwa gobe a Ashoora randa Imam Hussain (a) tare da sahabbansa 72 suka yi shahada a hannun sojojin yazeed a Karbala a ranar 10...
    ‘Yan kasuwa sun yi hasashen cewa za a yi sabon tsarin farashin daga ranar Lahadi. Tun a ranar Talatar da ta gabata, wakilinmu ya lura cewa sauran masu gidajen man da masu shigo da kaya sun daidaita farashinsu domin nuna sabon tsarin farashin da ya biyo bayan tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran. Daga Naira 920, akasarin gidajen sun rage farashin zuwa matsakaicin farashin Naira 845 akan kowace lita. A cewar Petroleumprice.ng, RainOil, Pinnacle, Matrid, Emadeb, Wosbab da First Royal suna sayar da man fetur a kan Naira 845 a Legas ranar Talata. Hakazalika, NIPCO, Aipec sun sayar da mai akan Naira 850 akan kowace lita. A sauran defot da ke wajen Legas, irin su Warri da Fatakwal, ana sayar...
    Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehra mya bayyana cewa: Hukuncin shari’a da ya hau kan Trumpm da Netanyahu shi ne kisa Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a yau ya bayyana cewa: Amurka da karen da suka horar sun yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma wannan wauta ce. Hakika dokar Musulunci ta Trump da Netanyahu ita ce mutuwa. Sun kashe mutane fiye da 55,000 a Gaza. Su suka kai Qasim Sulaimani da yin shahada da sauran abokansa. Su ne masu aiwatar da kisan kai da ayyukan fasadi a duniya. Sun yi wa Jagoran juyin juya halin Musulunci da al’ummar Iran barazana. Abin farin cikin shi ne, dukkanin hukumomin...
    Wani mummunan lamari na kisan gilla ya afku a ƙauyen Galadanchi da ke Ƙaramar hukumar Dutse a Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan jihar ta kama wani tsoho mai shekara 70 bisa zargin kashe ƙanwarsa saboda rikici kan filin gado. Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar y’an sandan jihar, SP Lawan Adam Shi’isu ya fitar ya ce tsohon mai suna Adamu Yakubu – ɗan asalin ƙauyen Galadanchi ne wanda ya samu saɓani da ƙanwarsa mai suna Hannatu Hashimu, mai shekara 45, kan rabon gadon wata gona da suka gada. Bayanan binciken farko da ’yan sanda suka fitar, ya nuna cewa...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwanan baya, wasu kamfanonin samar da kayan shayi masu tamburan kasar Sin sun jawo hankalin sassan kasa da kasa, sakamakon yadda suka fara sayar da hannayen jarinsu a kasuwar hannayen jari ta kasa da kasa. Baya ga haka, wasu kayayyaki masu tamburan kasar Sin na kara samun karbuwa a kasuwannin duniya. Har ma wasu kafofin yada labarai na kasa da kasa sun yi sharhin cewa, kayayyakin kasar Sin sun daina kwaikwayon wasu, suna bayyana halayensu na musamman a gaban jama’ar duniya. Wadannan kayayyakin kasar Sin suna samun karbuwa a kasuwannin duniya ne sabo da fasahohin zamani da al’adu da ke tattare da su da ma yadda aka tsara fasalinsu, kuma hakan ya faru ne sakamakon cikakken tsarin samar da kayayyaki...
    Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ƙaddamar da wani babban kwamitin ƙirƙiro masarautu da gundumomin hakimai a jihar. An ƙaddamar da kwamitin ne a wani mataki na magance buƙatu da dama daga al’ummomi daban-daban da kuma inganta al’adu da tsarin mulki na asali a faɗin Jihar Bauchi. Abba ya naɗa Ahmed Musa a matsayin Babban Manajan Kano Pillars An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno Gwamna Bala ya shaida wa kwamitin da ya sake duba buƙatu na samar da sabbin masarautu a faɗin jihar. Ya ce, aikin kwamitin shi ne inganta harkokin gudanar da mulki na cikin gida da inganta al’adu da kuma ƙarfafa muhimmiyar rawar da sarakuna ke gudanarwa wajen haɗin kai da ci...
    Bayan Plato sai kuma masani Aristotle shi ma ya zo da ta shi fahimtar, a shekara 340 kafin zuwan Annabi Isah (AS). A tunani irin Aristotle, yawaitar al’umma ba ta da wani alfanu, don haka hakki ne da ya rataya kan gwamnati ta kayyade yawan iyalin da mutum zai iya haifa. Idan matar mutum ta samu juna biyu (ciki) bayan sun kai adadin da gwamnati ta shardanta, ba su da wata mafita, in ji Aristotle, da ya wuce a zubar da cikin. Shi kuwa masani Abdurrahman Ibn Khaldun wanda aka haifa a ranar 27 ga watan Mayun 1332 ya na daga cikin wadanda ke goyon bayan yawaitar al’umma. Ibn Khaldun ya ce, rashin tunani da hangen nesa ne ma mutum...
    Ya yi nuni da cewa, jami’o’i na cikin tsaka mai wuya wajen samun sauye-sauye a duniya cikin sauri da kuma bukatu na cikin gida, wanda ke bukatar lallai sai sun sake yin nazari sosai kan tsarinsu, da dabi’unsu, domin samar da ingantaccen muradun al’ummarmu da nahiyarmu. Ya kuma jaddada mahimmancin hangen nesa inda jami’o’i za su zama matattarar kirkire-kirkire, masu inganci da kawo sauyi a zamantakewar al’umma. “Bari in yaba wa Makarantar Tattalin Arziki ta Afirka saboda himma da hangen nesa, ASE ta riga ta nuna kyakkyawar manufa wajen inganta karfin matasan Afirka da daidaita manyan makarantu tare da bukatun juyin-juya halin masana’antu na hudu,” in ji shi. A cikin laccarsa mai taken, “Jami’ar Nijeriya ta Karni na 21: Matsaloli...
    Lallai wannan kalanda ana ce mata ta Musulunci; gaskiya ne, ta Musulmi ce tsantsa sannan kuma ta duk halitta ce domi duk halitta suna amfani da wannan, ko sun sani ko ba su sani ba. Sai dai kawai, mu a cikin ibadojinmu Addininmu Balarabe ne kuma Larabawa da wata suke yin kirgensu, kuma shi ne ya dace da halittar Dan Adam, mun gode Allah. Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, a bana idan Allah ya kai mu watan Rabi’ul Auwal maulidin da za a yi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa. Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki...
    Gwamnatin Nijeriya na da shiraruwa da dama da manufar wadata kasa da abinci, inganta samun kudin shiga a karkara da rage fatara ta hanyar shiraruwa masu dorewa na bunkasa aikin gona, sai dai a kodayaushe kalubalen ‘yan ta’adda na hana shiraruwan samun nasara. Rahotanni da dama sun ruwaito yadda ‘yan ta’adda ke tilastawa manoma biyan haraji gabanin su ba su damar shuka da girbe amfanin gona a gonakin su wanda hakan babban kalubale ne ga manoma da kasa bakidaya. A bisa ga kasa biyan harajin da barayin dajin ke tilasta masu, dimbin manoma sun rasa rayukan su wasu kuma da dama sun yi gudun hijira daga garuruwan su domin tsira da rayukan su. A watan Yuni da ya gabata kadai...
    Ya bayyana cewa, kungiyar na ci gaba da nazartar na rabar da man kai tsare, na shirin na matatar man ta Dangote, wanda daga baya, kungiyar za ta shiga cikin shirin gadan-gadan. Clement, ya sanar da cewa, kafin kungiyar ta shiga cikin shirin kai tsaye, yana da kyau a fara tattaunawa da Dangoten da kuma sauran da hukumomi. A cewarsa, ta hanyar tattaunawar ce, za ta sanya kungiyar ta shiga cikin shirin, domin a yanzu, muna ci gaba da yin nazari ne, kan shirin na Matatar ta Dangote. Sakataren ya ci gaba da cewa shirin da matar ta Dangote ta bullo dashi na rabar da man kai tsaye, musamman iskar Gas, abu ne da kungiyar take gani ya dace. “Shirin...
    Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan masu dawowa daga binne gawa a kauyen Rim na jihar Filato, inda suka datse wa daya daga cikin matasan da ke wurin hannu daya. Bayanai sun nuna cewa mutanen na kan hanyarsu ce ta dawowa daga bikin binne wani mutum ne a kauyen Bachit da ke da makwabtaka da su inda suka yi arba da maharan wadanda suka tare su suka bude musu wuta, sannan suka datse wa daya daga cikin mutanen hannu daya. Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA Wani Hadimin Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, mai suna Timothy Dantong, wanda yake cikin mutanen da suke dawowa...
    Dantsoho wanda ya samu wakilicin Babban Manajan a Hukumar ta NPA Femi Oyewole, ya bayyana cewa, Shugaban Hukumar ta NPA, Hukumar ta mayar da hankali wajen ganin cewa, ana kare kimar Tekunan kasar. “Hadurran zuba baraguzan kusan a kurkusa suke, wanda kuma, suke ci gaba da karuwa, wanda hakan ya nuna cewa, akwai matukar bukatar a dakile yadda ake duba baragunzan, a cikin Tekunan, baki daya,” Inji Dantsoho. Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA bata yi kasa a guiwa ba, wajen daukar matakan da suka kamata, domin magance wannan matsalar. “Duba da cewa, muna gudanar da ayyukan NPA yadda ya kamata da kuma bin ka;idojin da ke tafiyar da Hukumar, musamman wajen bai wa kayan Hukumar da ke...
    Kwamatin Harkokin Kananan Hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin kwanaki biyu a karamar hukumar Roni a ci gaba da rangadin kananan hukumomin jihar 27 da kwamatin ya kaddamar. A jawabin sa a sakatariyar karamar hukumar Roni, Shugaban kwamatin Alhaji Aminu Zakari, ya ce tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa ikon dubawa da kuma tantance yadda bangaren zartaswa ke aiwatar da manufofi da shirye shiryen gwamnati. Ya ce ziyarar za ta mayar da hankali ga dubawa da kuma tantance kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da kundin kasafin kudi na shekarar 2024 zuwa 2025 da Asusun kula da matsalolin muhalli da kundin bayanan kwamitocin karamar hukumar da takardun biyan kudade wato Voucher...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar riƙon ƙwarya ta Gwamnatin Mali ta bai wa Shugaban Mulkin Sojin ƙasar, Janar Assimi Goita, wa’adin mulki na shekara biyar, wanda za a iya sabunta shi fiye da sau daya ba tare da zaɓe ba. A bara ne Janar Goita ya yi alƙawarin maido da mulkin dimokuradiyya a ƙasar, sai dai hakan ba ta samu ba. Tsohon golan Super Eagles, Peter Rufai ya mutu Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir Ahmad Wannan matakin ya bude hanya ga Janar Goita ya ci gaba da jagorantar kasar ta yammacin Afirka har zuwa aƙalla shekarar 2030, duk da alƙawarin da gwamnatin sojan ta yi na komawa mulkin farar hula a watan Maris na shekarar 2024. Sai dai sabon ƙudirin dokar...
    Yayin taron manema labarai na yau Alhamis, kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin He Yongqian, ta ce ba su da wata masaniya, game da cewa shugaban Amurka na shirin jagorantar wata tawagar ‘yan kasuwa zuwa kasar Sin. Sai dai kuma duk da hakan, a cewarta har kullum matsayar Sin a bayyane take, cewa tana fatan ita da Amurka za su bi turba guda, kuma karkashin jagorancin yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka amince da su, za su rungumi ka’idojin mutunta juna, da zama cikin lumana, da gudanar da hadin gwiwar cimma moriyar juna, ta yadda za a ci gaba da cimma matsaya guda. Har ila yau, sassan biyu za su kai ga rage sabani, da karfafa hadin gwiwarsu, da bunkasa alakar...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, a yayin taron an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Yankunan Karkara, sannan aka tattauna da masu ruwa da tsaki, tambayoyi da amsoshi, ra’ayoyi, da kuma alƙawura.   A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya ce ya gaji matalauciyar gwamnatin a bangaten lantarki.   Ya ci gaba da cewa, “An katse ƙananan hukumomi da yawa daga babban lantarkin ƙasa. An sace wayoyin lantarki da dama, wasu kuma sun lalace, wasu muhimman ababen more rayuwa sun durƙushe a cikin shekaru saboda watsi da su, sannan masana’antu da kasuwancinmu sun gurgunta saboda rashin ingantaccen wutar lantarki.   “Duk da haka, mun zaɓi kada mu shiga wasan zargi,...
    Birgediya Janar Abdulsalam ya roƙi jama’a da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai, duk da cewa rufe kasuwannin na iya kawo wata matsala ga rayuwar yau da kullum. “Gwamnati na ƙoƙarin ganin an rage tasirin da rufe kasuwannin ka iya haifarwa ga al’umma. Muna roƙon ku fahimce mu saboda zaman lafiya da tsaro,” in ji shi. Ya kuma tabbatar wa mazauna yankunan cewa za a sake buɗe kasuwannin nan ba da jimawa ba, idan aka kammala aikin tsaro da ake gudanarwa. Kasuwannin da aka rufe suna daga cikin manyan kasuwanni a wannan yanki na Jihar Yobe. Wani mazaunin Kukareta ya shaida wa wakilinmu cewa ba su san dalilin rufe kasuwannin ba, kawai ji suka yi an ce an bayar...
    Baltasar Engonga Ebang, mutumin nan dan kasar Equatorial Guinea da a bara ya saki bidiyon lalatarsa da mata sama da 400 na fuskantar shari’a a kotu kan badakalar kudade. Baltasar, wanda tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta kasar Equatorial Guinea ne dai an gurfanar da shi a gaban kotu ne bisa zargin karkatar da kudade a karkashin Ma’aikatar Kudin kasar. Masu shigar da kara na neman a yanke masa hukuncin daurin shekara 18 a kurkuru sannan a umarce shi ya dawo da wasu kudaden masu yawa. ’Yan Najeriya sun fara begen Buhari saboda azabar TIinubu – Amaechi Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota Ana dai zarginsa ne da almundahana, azurta kai da kuma rub-da-ciki a...
    Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli. Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota “Farashi kayayyaki ya tashi sosai. Mutane ba za su iya siyan abinci ba. Babu kuɗi. Komai ya lalace,” in ji shi. Ya ƙara da cewa rayuwa ta yi tsanani har mutane sun fara tunawa da zamanin Buhari da muradin dawowarsa kan mulki. “Yanzu mutane na so Buhari ya...
    Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli. Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota “Farashi kayayyaki ya tashi sosai. Mutane ba za su iya siyan abinci ba. Babu kuɗi. Komai ya lalace,” in ji shi. Ya ƙara da cewa rayuwa ta yi tsanani har mutane sun fara tunawa da zamanin Buhari da muradin dawowarsa kan mulki. “Yanzu mutane na so Buhari ya...
    Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu. Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI. Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin...
    Jaridun kasar Amurka sun bayyana cewa; Isra’ila ta kasa cimma manufofin da ta ayyana a yaki da Iran, sannan kuma ta kara zama saniyar ware a duniya. Mujallar “Foreign Policy” ta yi ishara da sakamakon yakin da take cewa, ya zamarwa Amurka da kawarta   Isra’ila juyewar reshe da mujiya,domin harin da su ka kai wa Shirin Iran na Nukiliya bai iya kawo karshensa baki daya,maimakon haka ma sai ya jazawa Tel Aviv asarar mai yawa da kuma karfafa kishin kasa a tsakanin Iraniyawa.” Har ila yau, rahoton mujallar ta “”Foreign Policy” ya ci gaba da cewa; Asarar da aka yi a Isra’ila, tana firgitarwa”,amma a cikin Iran babu cikakken bayani akan girman barnar da aka yi- da hakan yake a...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Laraba a taron manema labaru da aka gudanar cewa, kayayyakin Sin sun shiga kasuwar duniya, inda suka kara baiwa masu sayayya na kasa da kasa damar samun zabi. Jami’ar ta yi tsokacin ne bisa yadda batun wasu kayan shayi na kasar Sin ya jawo hankalin sassan kasa da kasa, bayan shigarsu kasuwar hannun jari ta kasashen waje. Mao Ning ta bayyana cewa, kayayyakin Sin sun kara jawo hankulan masu sayayya na kasa da kasa ta hanyar fasahohi, da shaida al’adun gargajiya, da zane-zane da suke dauke da su, da kuma abubuwan dake hade Sin da kasashen waje. Daga kayayyaki kirar kasar Sin zuwa tambarin kayayyakin Sin, kasar Sin...
    Tsangayar Kwalejin koyar da aikin Jinya ta Jihar Jigawa dake garin Birnin kudu ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin dalibai 116 da za su yi karatun difloma ta kasa da babbar difloma ta kasa karon farko na shekarar karatu ta 2024 zuwa 2025. A jawabinsa wajen taron kaddamar  da daliban,  kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar Jigawa Dr. Muhammad Abdullahi Kainuwa, ya ce aikin sa na farko daga samun wannan mukami shi ne batun kafa hukumar Gudanarwar Kwalejin da sake fasalin Kwalejin, wanda hakan ya bada damar tantancewa da kuma samun amincewar Cibiyar kula da makarantun aikin Jinya ta Najeriya. Yana mai cewar, daukar wannan mataki ya bada damar kara yawan dalibai da Kwalejin take dauka daga 120 zuwa 240,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban hukumar kula da makarantun kiwon lafiya da bada lasisi ga likitoci kula da lafiya a matakin farko ta kasa Alhaji Dr Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya hori ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko da dukkannin masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya su rubanya kokari fuskar tabbatar da kwarewa domin inganta ayyukan kula da lafiya a Nijeriya. Dr. Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya yi wannan kiran ne a Katsina lokacin bukin rufe taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku na wannan shekarar wanda aka shiryawa Malaman koyar da darusan kiwon lafiya a matakin farko. Taron wanda ya samu halartan jami’an kiwon lafiya daga dukkannin jihohin yankin arewa maso yamma, yana da nufin ilimintar dasu ne kan yadda za...
    Iran ta nuna makamai masu linzami wadanda suka bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya A martanin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun nuna karfinsu na soji a matsayin wani bangare na “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda suka harba daruruwan makamai masu linzami na ballistic da hypersonic. A wani bangare na wannan harin na ramuwar gayya, Iran ta kai jerin hare-hare na hadin gwiwa, wanda kaso mafi tsoka na makamai masu linzami kamar Emad, Ghadr, Fattah 1, Sejjil da Khaybar. A halin yanzu rahotonni da hotuna daga haramtacciyar kasar Isra’ila suna kara fitowa kan yadda makamai masu linzamin Iran suka tarwatsa wurare masu muhimmanci na gwamnatin haramtacciyar...
    Jagoran sabuwar jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, zai jagorance su wajen karɓar mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. Jam’iyyar haɗakar, wacce ta ƙunshi fitattun ’yan siyasa, ta naɗa David Mark a matsayin Shugaba, tare da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin Sakatare. ’Yan sanda sun kama wani mutum da jabun kuɗi a Gombe Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba A wajen babban taron da ta gudanar a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja, Nwosu ya ce: “Mun sauka daga muƙamanmu domin mu bai wa David Mark dama ya jagoranci wannan tafiya zuwa fadar shugaban ƙasa.” Ya yaba wa Aregbesola, wanda ya taɓa kasancewa...
    Shugaban Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, Alhaji Bello Mohammed Jabaka, ya yi kira ga al’ummar yankin da su dauki matakan kariya domin dakile yaduwar cutar kwalara da sauran cututtukan da ke yaduwa cikin sauri a yankin. Ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, kan matakan da hukumar ta dauka domin dakile barkewar cutar ta amai da gudawa a wasu sassan karamar hukumar. Alhaji Jabaka ya jaddada muhimmancin tsaftar muhalli, musamman wajen tsaftace rijiyoyi da sauran hanyoyin samun ruwan sha, wuraren da ake dafa abinci, da kuma tsaftace muhalli gaba daya, tare da tsaftar jiki wanda ya ce shi ne mabuɗin hana yaduwar cutar ta kwalara. A cewarsa, kwalara cuta...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da Amurka a yankin yammacin Asiya ya kara rashin zamn lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadin haka ne a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Girka a jiya talata . Ya kuma kara da cewa hare-haren sun yu watsi da hanyar zaman lafiya da kuma zaman lumana a yankin. Ya kuma yi sanadiyyar karin tashe tashen hankula a yankin. Ministan ya bukaci kasashen duniya gaba daya su yi tir da HKI da kuma Amurka wadanda suka keta hurumin kasa mamba a MDD ba tare da wani daloli nay an haka ba. Ya ce hare-haren da...
    Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran na nakalto majiyar Fadar Majiyar fadar white House na bayyana cewa pentagon ko ma’aikatar tsaron kasar ta bada rahoton cewa rumbun ajiyar makaman kasar yayi kasa sosai don haka akwai bukatar a dakatar da aikawa kasar Ukraine wasu makaman, kamar garkuwan kare sararin samaniya da kuma makamai masu taimaka mata wajen kare kanta. Labarin ya nakalto Anna Kelly kakakin fadar white house na cewa an dauki wannan matakin en don sanya Amurka a gaba, duk da cewa ba zata dakatar da bawa kawayenta taimakon da ya dace ba.
    Rundunar ’sanda ta jihar Delta ta ja kunnen matasan jihar a kan yin shigar banza, inda ta ce duk wanda aka kama za a iya cin shi tarar da ta kai ta naira 50,000. A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar a jihar, SP Bright Edafe ya fitar ranar Talata, ya ce yin shigar banzan ya saba da dokar hana cin zarafin mutane ta (VAPP). Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU Kazalika sanarwar ’yan sandan ta nuna bacin rai game da shigar banza da matasa a jihar suka runguma. “Akwai wasu daga cikin dokokin da aka kafa da...
    Wani rikicin gado a kan fili da ya ɓarke tsakanin wasu ahali biyu a ƙauyen Kopkopshe na gundumar Tunkus da ke Ƙaramar Hukumar Mikang ta Jihar Filato, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da ƙone gidaje da dama. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, bayan aukuwar rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu wanda sun shafe fiye da shekaru biyu ba sa ga maciji a kan asalin mai haƙƙin gadon gonar daga iyayensu. An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin Hadimin Shugaban Ƙaramar Hukumar Mikang kan harkokin yaɗa labarai, Nkat Joseph Lakai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Burodi ya zama daya daga cikin abincin da ‘yan Najeriya basa iya yi babu shi. Yayin da wasu ke cin shi a matsayin abin Karin kumallo da safe, wasu kuwa na cin shi a matsayin abincin rana a wasu lokutan ma har da na dare.   A duk lokacin da aka ce masu sarrafa burodi sun shiga yajin aiki, ko fulawa tayi karanci hakan kan haifar da raguwar burodi a kasuwa wadda kan jefa masu cin shi a cikin mawuyacin hali. NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi? Shirin Najeriya A Yau na wannan makon zai yi...
    Lokaci bai kura wa sauran kasashe na koyi da Sin ba. Sun gwada aron tsare-tsaren kasashen yamma, kuma babu inda hakan ya kai su. Don haka za su iya tsara irin dabarun da ya dace da yanayinsu domin kyautata makomar kasashensu da al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rahoton LEADERSHIP ya tabbatar da cewa wannan ikirari ƙarya ne. Bincike ya nuna cewa ba wanda aka sace daga cikin mutanen da ke bidiyon yana da alaƙa da Gwamna Dauda Lawal. Haka kuma, binciken ya nuna cewa ƴar uwar Gwamnan da aka sani mace ce, ba namiji ba. Hakanan, mutumin da ke cikin bidiyon na bayyana cikin tsananin firgici da damuwa, alamar cewa yana fuskantar tilas daga barayin daji da suka umurce shi da ya faɗi abin da suke so. Da yake martani kan bidiyon, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa wannan wata sabuwar dabara ce da ɓarayin suka bullo da ita don jawo hankali. Ya ce, “Idan aka kalli bidiyon da kyau,...
    Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun tsaro na rundunar “Operation Hadin kai” sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 yayin wata arangama a yankin Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina Manjo Janar Markus Kangye ya ce aikin kawar da ‘yan ta’addan da aka aiwatar ranar Litinin ya faru ne bayan rundunar ta lashi takobin kawar da sauran ‘yan Boko Haram/ISWAP da ke ɓuya a yankin Tafkin Chadi. “Arangamar ta faru ne a lokacin wani aiki na haɗaka wanda aka...
    Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin zai gudanar da taron manema labarai a ranar Alhamis mai zuwa, da misalin karfe 10 na safe domin yin bayani kan shagulgulan al’adu da za a yi na bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin Japanawa da kuma yakin duniya na biyu. Jami’ai daga ma’aikatar al’adu da yawon bude ido da na hukumar gidan rediyo da talabijin ta kasar, da mataimakin shugaban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), da shugaban gidan adana kayan tarihi na yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin Japanawa, za su halarci taron manema labarun. Za su yi wa manema labarai karin haske kan wani baje koli mai...
    Ya samu munanan raunuka a harin da aka kai masa, wanda daga baya ya mutu. Janar Kangye ya ƙara da cewa Danbokolo ya fi Bello Turji tsabibanci, shi ne ya jagoranci harin watan Disamban 2021 a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, inda ya ƙone fasinjoji da ransu a cikin mota. Hakazalika, ya bayyana cewa Danbokolo na amfani da wata ƙwaya mai suna ‘pentazocine’ domin ci gaba da aikata miyagun laifuka. Yanzu haka, sojojin Operation FASAN YAMA suna ci gaba da neman Bello Turji wanda ya ɓuya. Janar Kangye ya tabbatar da cewa rundunar sojin Nijeriya tana da ƙwarin gwiwar samar da zaman lafiya a dukkanin sassan ƙasar nan. Ya kuma roƙi haɗin kan ‘yan Nijeriya don cimma wannan buri....
    Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya amince da kafa kwamitin mambobi 41 da nufin kafa sabbin masarautu a faɗin jihar. Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar ta bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi fitattun mambobi 41 da aka zabo daga ɓangarori daban-daban, ciki har da sarakunan gargajiya, ƙwararru, malaman jami’a, wakilan ƙungiyoyin farar hula, lauyoyi, jami’an tsaro, da ƙungiyoyin addini. Sanarwar ta ce, “Wannan shiri ya biyo bayan kiran da gwamnatin jihar ta yi tun da farko na gayyatar al’ummomi da su gabatar da buƙatunsu na sabbin masarautun gargajiya. “Kwamitin yana da alhakin tantance waɗannan bukatun bisa ƙa’idar adalci, daidaito, shigar da kowa cikin harkokin siyasa da zamantakewa, da ɗorewar tattalin arziki.” Alhaji Hamza Koshe ne zai...
    Dukkaninsu sun je ne domin girmama marigayi Dantata tare da halartar jana’izarsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Nijeriya ta karɓi bashin daga ƙasashen duniya da cibiyoyin kuɗi kamar Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Exim Bank na ƙasar Sin, da kuma daga Japan da wasu ƙasashen. Ta kuma karɓi bashin kasuwanci kamar na Eurobond. Bashin cikin gida kuwa wanda gwamnati ke karɓa daga cikin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 78.76, kwatankwacin dala biliyan 51.26. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...
    Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta ce: “Mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan an kai su asibitocin birnin Bangui.” Ba a samu ingantattun bayanan yawan wadanda suka mutu ba har zuwa yammacin ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da fashewar ta faru, sama da dalibai 5,300 ne ke zana jarrabawar kwana na biyu na jarabawar sakandare.
    Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa jami’an sa-kai sun kashe wani riƙaƙƙen ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan jihar mai suna Kacalla Ɗanbokolo. Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana kisan Ɗanbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro. “Ɗanbokolo mutum ne da ya fi Bello Turji fitina, ya fi Turji aikata miyagun laifuka, illa kawai shi Turji sunansa da ya karaɗe kafofin yaɗa labarai,” in ji Ahmad Manga. “Mutanensa da aka kashe sun haura 100, saboda haka wannan gagarumar nasara ce a gare mu,” in ji Manga. Ya bayyana cewa Kacalla Ɗanbokolo ya rasa ransa a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin jami’an sa-kai na Gwamnatin...