2025-08-14@13:49:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3192

«Ya ku mutane»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Rahotanin sun bayyana cewa Shettima ya ziyarci Kano ne don yin ta’aziyyar rasuwar hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu kwanan nan, da kuma jajanta wa mutanen Kano kan wannan rashi. Haka kuma rahotannin sun bayyana cewa a irin wadannan manyan taruka a Nijeriya, an saba ganin shugabannin jam’iyya da goyon baya su tarbi manyan jami’ai kamar mataimakin shugaban kasa, amma lamarin ya bambanta yayin ziyarar Shettima, wanda ya haifar da zazzafar muhawara. Da yake musanta cewa akwai rikice-rikice na cikin gida a jam’iyyar, sakataren APC a Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida cewa rashin halartar shugabannin jam’iyyar a ziyarar ta’aziyya da mataimakin shugaban kasa ya kawo Kano ya faru ne sakamakon rashin sadarwa. “Mun san cewa ziyarar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ce; Amincewa da aikata zalunci, ya yi daidai da hada baki da mai aikata shi.” Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Dr. Baka’i wanda ya wallafa sako a shafinsa na X cewa; Shugaban gwamnatin kasar Jamus yana ci gaba da nuna goyon baya ga munanan ayyukan da HKI take aikatawa wanda yake cin karo da yarjeniyoyin MDD da kuma dokokin kasa da kasa.” Haka nan kuma Dr. Baka’i ya ce; Abinda Jamus din ta aikata zai mayar da ita wacce za ta amsa tambayoyi a matsayin wacce take yin zuga a aikata laifi. A lokacin da HKI ta fara kawo wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran hare-hare dai shugaban...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta bayyana dalilin da ya sa ta gayyaci malamin addini Sheikh Lawal Triumph. A wata sanarwa da ta fitar, ’yan sanda sun ce sun sani cewa wasu daga cikin wa’azozin da Sheikh Triumph ke yi suna haddasa rashin jituwa a tsakanin al’ummar jihar. Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote Rundunar ta ce kowa na da ’yancin faɗin albarkacin bakinsa, amma dole ne komai ya kasance bisa doka. Saboda haka ne Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, ya gayyaci Sheikh Lawal Triumph don tattaunawa da jami’an gwamnati, shugabannin addini da na al’umma. Manufar...
    Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana a yau Juma’a da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a Kuala Lumpur na Malaysia, inda suka yi musayar ra’ayi kan danganatkar Sin da Amurka da batutuwan dake jan hankalin kasashensu. Wang Yi ya yi cikakken bayani kan matsayar Sin game da raya dangantakarta da Amurka, yana mai nanata bukatar bangarorin biyu su aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen suka cimma zuwa manufofi da ayyuka na hakika. Ya ce fatan ita ce Amurka ta kalli Sin da ra’ayi na sanin ya kamata da tsara manufar hulda da Sin bisa burin zaman lafiya da hadin gwiwar moriyar juna da tafiyar da dangantakarta da Sin bisa matsayi na daidaito da girmamawa da moriyar...
    Kamfanin dillancin labarun “Associated Press” wanda ya sami hotunan tauraron dan’adam na cibiyar sojojin Amurka dake “al-udid” a kasar Qatar, ya nuna yadda harin ya sami wata Qubba, da a cikinta akwai na’urorin sadarwa da Amurka ke amfani da su.” Hotunan tauraron dan’adam na ” Planet Labs” sun nuna yadda Qubbar ta sansanin Amurka a Qatar take sa’o’i kadan gabanin a kai harin a ranar 23 ga watan Yuni. Rundunar Amurka ta 379 mai aikin ttatara bayanai ta kafa wannan Qubbar ne tun a 2016 da kudin da sun kai dalar Amurka miliyan 15. Haka nan  kuma tauraron dan’adam din ya nuna yadda qubbar ta  bace, da kuma yadda ginin da yake  kusa  da ita ya illata. Kamfanin dillancin labarun...
    Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar  wanda ya yi hira a wata tashar talbijin din kasar ya yi amfani da salon maganar wani mawakin Amurka  mai suna Flavour Flav da ya shahara a shekarun baya, wajen mayarwa da shugaban Amurka Donald Trump martani da cewa: Babu abinda zai iya yi ma ka.” Jaridar Wall Street Jouran ta buga labarin dake cewa; A yayin taron da aka yi a tsakanin wasu shugabannin kasashen Afirka biyar da shugaban kasar Amurka a fadar White House, an bijiro musu da karbar bakuncin ‘yan ci-ranin kasashe waje da Amurka take son kora daga cikinta. Jaridar ta ambaci Nigeria a cikin kasashen da Amurka ta bijirowa da bukatar ta karbi bakuncin ‘yan ci-ranin kasar Venezuela...
    An kaddamar da shirin koyar da Sinanci mai taken “Hello China”, na gidan rediyon Nijeriya (FRCN), a Abuja babban birnin kasar. Kusan mutane 100, ciki har da jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai da darakta janar na FRCN Mohammed Bulama ne suka halarci bikin kaddamarwar da ya gudana a jiya Alhamis. Cikin jawabin da ya gabatar, Yu Dunhai ya ce kaddamar da shirin na koyar da Sinanci da gidan rediyon ya yi, zai samar wa ‘yan Nijeriya wani sabon dandali na koyon harshen Sinanci da fahimtar kasar Sin, tare da samar da kuzari mai dorewa ga hadin gwiwar moriyar juna a fannonin cinikayya da tattalin arzikin tsakanin Sin da Nijeriya Daga ranar 16 ga wata ne za a fara watsa...
    Ministar Raya Al’adu, Hannatu Musawa, ta ce ya kamata shugabancin ƙasar nan ya ci gaba da kasancewa a hannun ’yan Kudu domin a samu adalci da daidaito. Ko da yake kundin tsarin mulkin Najeriya bai tilasta tsarin karɓa-karɓa ba, manyan jam’iyyun siyasa suna bin tsarin sauya mulki tsakanin Arewa da Kudu. An tsare mutum 20 da ake zargi da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato Ba lallai matatun man gwamnati su sake aiki ba har abada a Najeriya – Ɗangote A wata hira da ta yi da gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Hannatu Musawa ta ce tun da an samu Shugaba daga Arewa (Muhammadu Buhari) na tsawon shekaru takwas, to ya dace yanzu kuma a bar ’yan Kudu...
    Amurka ta bayyana dalilin sabunta manufofin, tare da lura da cewa “an tsara sharuddan bizar Amurka da ka’idoji domin kare tsarin shige da fice na Amurka.” Ofishin jakadancin ya kara da cewa “wadannan ka’idoji sun dogara ne kan ma’aunin fasaha da tsaro na duniya.” A cewar ofishin jakadancin Amurka yana aiki tare da hukumomin Nijeriya domin cimma wadannan matakan. Sanarwar ta ce “Tawagar Amurka tana aiki tare da gwamnatin Nijeriya domin tabbatar da cewa Nijeriya za ta iya cika sharuddan.” Misalin wannan sabon tsari ya hada da “Takardun tafiye-tafiye masu aminci: tabbatar da cewa kasashe suna ba da amintattun takaddun balaguro tare da ingantattun bayanan matafiyi, Kada aikin gudanar da Bisa ya wuce lokacin da aka dauka:.” Duk da sabbin...
    A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, ƙaddama da shirin na nuni da ƙwazon gwamnatinsa na yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin aiwatar da dabaru daban-daban na ƙara yawan ɗalibai a makarantun jihar Zamfara.   Ya ci gaba da cewa, “Alƙawarinmu na yin garambawul ya haɗa da tsare-tsare na yaƙi da rugujewar sassan ilimi da samar da haɗin gwiwa, kamar Bankin Duniya ta hanyar shirin AGILE da kuma UNICEF. A kwanakin baya Ma’aikatar Ilimi, Kimiya da Fasaha tare da haɗin gwiwar UNICEF, sun kafa wani kwamitin fasaha na shugabannin hukumomin da masu ruwa da tsaki domin ziyartar mananan hukumomi 14, da tantance yaran da ba su zuwa makaranta, da kuma tabbatar da shigar su makarantu.  ...
    A nata bangaren, Mrs. Adeniji ta bayyana cewa akwai yawaitar yara marasa zuwa makaranta a ƙananan hukumomi 14 na jihar, tare da tabbatar da cewa ta hanyar wannan shirin zai taimakawa ɓangaren ilimi a jihar Zamfara. “Muna aiki tare domin tabbatar da cewa babu wani yaro da aka bari s baya,” Cewar ta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran kayayyakin da aka raba sun haɗa da irin shinkafa kilogiram 34,800, irin masara kilogiram 80,000, da lita 23,740 na maganin ciyawa, lita 11,735 na maganin kwari, da buhunan sinadarai na gyaran iri 23,470.   A yayin jawabin maddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa rabon takin zamani kyauta na nuni da yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin kawo sauyi a jihar Zamfara ta hanyar noma mai ɗorewa da bunƙasa karkara.   Ya ce, “Aikin noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jiharmu, ba sashe kaɗai ba ne, amma asalin al’ummarmu ne.   “Gwamnatinmu ta rungumi taken ‘noma abin alfaharinmu ne’. Noma na nuna ainihin ko su wane ne mu da kuma abin da ya kamata mu ba da...
    Ɗangote Ya ƙara da cewa “A yau, bayan kashe sama da dalar Amurka biliyan 18 wajen gudanarwa tare da gyara matatun man har yanzu basa aiki. Kuma bana tunanin nan gaba za su iya ci gaba da aiki. Ƙoƙarin zamanantar da su kamar misalin zamanantar da tsohuwar motar da ta yi shekara 40 ne, ko an canja inji ba zai sa ta koma dai-dai da ta zamani ba”. Alhaji Aliko Ɗangote ya ce ya yanke shawarar gina matatar man fetur ne mai fitar da ganga dubu ɗari shida da hamsin a rana bayan da marigayi Umaru Musa Yar’adua ya yanke shawarar ƙin siyar masa da matatun man fetur ɗin ƙasar nan. Sabuwar matatar man fetur ta Ɗangote ana saran za...
    Ya mika saƙon ta’aziyyarsa Kwamishinan ‘Yansandan Jihar, Shetima Jauro Mohammed, ga iyalan mamacin tare da tabbatar da cewa an ƙaddamar da bincike mai zurfi tare da shiga farautar waɗanda suka aikata harin domin a cafke su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “A wajen jahilai, tsagaggen lebe lahani ne a kan makogwaro da lebe, amma idan akwai shinge tsakanin hanci da baki, ana kiran sa da suna handa. Wani abu ne da ba a san abin da yake kawo shi ba, amma kuma ana danganta shi da abubuwa da dama kamar karancin rashin sinadarin bitamin B.” “Don haka, muna shawartar mata masu juna biyu da su mayar da hankali wajen yawan zuwa awon ciki, sannan kuma su rika shan magungunan da ake ba su na yau da kullum, ta yadda za a rage haihuwar masu dauke da wannan cuta. “Hakika wannan babban abin takaici ne a cikin al’umma, shi yasa kwararrun likitoci, ma’aikatan jinya, jami’an jin dadin al’umma da likitocin makogwaro, hanci...
    “An tsara kungiyar ne domin hada kan Arewa da magance matsalar rashin aikin yi Wanda hakan ya sanya aka tattaro manyan hafsoshin soja da suka yi ritaya, da tsaffin gwamnoni, da masu rike da sarautun gargajiya, da masu fafutukar kare hakkin jama’a, da kungiyoyin matasa, da kwararrun a fannin ci gaban kasa wadanda da yawa daga cikinsu sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da mulki da kuma mayar da muradun Arewa saniyar ware a ‘yan shekarun nan”   “Yankin arewa na iya shawo kan kalubalen da suke fuskanta ta hanyar hadin kai da kuma sabunta kudurin samar da ci gaba,”   Bafarawa ya kuma tabbatar da cewa ba an kafa kungiyar bace a matsayin dandalin siyasa ba, kuma...
    Kamfanonin inshora za su kauracewa jiragen ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila saboda tsoron fuskantar hare-haren Yemen Jiragen ruwan da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila za su fuskanci kaurace daga kamfanonin inshora, sakamakon munanan hare-haren baya-bayan nan da sojojin Yemen suka kai kan jiragen Magic Seas da Eternity Sea, wadanda suka kai ga nutsewa, a teku a ranar Alhamis. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa ya bayyana cewa: Majiyoyin masana’antar inshora sun ce “kamfanonin inshora za su yi kokarin kauce wa rufe duk wani jirgin ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ko da kuwa alakar a kaikaice ne.” Kamfanin dillancin na Reuters ya nakalto daga Munro...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da umarninsa ga sabbin kwamandojin da kansu a lokacin yakin baya-bayan nan Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, yayin da yake ishara da umarnin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar a yakin kwanaki 12 da aka kakabawa Iran, ya ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kasance a dakin kwamandoji sau biyu a lokacin yakin tare da bayar da umarninsa ga sabbin kwamandojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A wata hira da aka yi da shi ta gidan telebijin, Qalibaf ya kara da cewa kwamandojin da aka nada sa’o’i bayan fara kai hare-hare kan kasar Iran,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi tsokaci kan takunkumin Amurka ta kakaba kan jami’ar Majalisar Dinkin Duniya da cewa: Ba za a iya murkushe gaskiya ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi tsokaci kan takunkumin da Amurka ta kakaba wa wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese. A cikin wani rubutu a dandalin “X” a ranar Juma’a, Baqa’i ya bayyana cewa: “Ba za a iya murkushe gaskiya ba.” Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan halin da ake ciki na kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu,  Francesca Albanese, ta fuskanci takunkumi da girman kai saboda fallasa gaskiya da kuma tsayin...
    Mataimakin shugaban kasar na farko ya jaddada cewa: Kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Iran Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: kalmar mika wuya ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron kasar. Arif ya ce: Kamar yadda kuke gani kalmar “mika kai” ba ta da gurbi a al’adun siyasa da tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa, su mutane ne masu wayewa, tare da ingantaccen tarihin al’adu wanda ya wuce dubban shekaru. Ba su neman yaki, kuma ba su fara shi ba. Sun yi imani da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kuma a shirye suke don tattaunawa, amma ba za su mika wuya a...
    Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana aiwatar da shirye-shirye masu ɗaukar hankali ta hanyar manyan ayyukan gine-gine, shirye-shiryen tallafa wa matasa, da kuma sauye-sauye a fannonin noma, makamashi, ilimi da ƙere-ƙere.   Ministan ya bayyana cire tallafin fetur a matsayin ɗaya daga cikin manyan matakan da gwamnatin ta ɗauka domin farfaɗo da tattalin arziki.   Ya ce: “Ɗaya daga cikin manya kuma mafi tasiri daga cikin matakan da wannan gwamnati ta ɗauka shi ne cire tallafin fetur, wanda ko da yake ya kasance mai raɗaɗi, amma sauyi ne da ya zama dole. Bayan ceton tattalin arzikin ƙasa daga rugujewa, wannan mataki ya hana ɓarna da asarar kuɗi sosai a tattalin arzikin mu.”   A cewar sa, kuɗaɗen da aka ceto...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matasan Najeriya da dama suna son yin arziki amma ba tare da sun sha wahala ba.   Sau da yawa matasa sun fi neman hanya mafi sauki da za ta basu arziki ba tare da sun sha wahala ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa bin yanke don tara abin duniya. Domin sauke shirin, latsa nan  
    Mai taimaka wa Sarkin Bayero kan harkokin yada labarai, Khalid Uba, ya shaida wa LEADERSHIP cewa magoya bayan Sarkin Bayero ba su da makamai. Uba, wanda ya zanta da wakilinmu ta wayar tarho, ya ci gaba da cewa babu wani daga cikin tawagar Sarkin Bayero da ke dauke da wani makami, sai dai an tilasta musu dakile harin. A cewarsa, wannan ba shi ne karo na farko da Sarkin Bayero ya taba bi ta wannan hanyar ba. “Bayan isowarmu daga gidan Dantata domin jaje, wasu matasa sun mamaye titin da duwatsu da makamai a Kofar Kudu. “Lokacin da muka isa Kofar Kudu, sai suka fara jifan mu, amma aka yi sa’a, mun yi nasarar fatattakar su zuwa cikin gida, kuma...
    shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibof ya bayyana cewa asarorin da HKI ta yi a yakin kwanaki 12 da JMI suna da yawa. Kuma babu shakka ya fi abinda ta bayyana. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a lokacinda yake hira da wata tashar talabijin a nan Tehran . Ya kuma kara da cewa. Maganar cewa uahudawa 3500 kawai suka ji rauni a yakim gaba daya karya ce. Qalibof ya ce yana da tabbacin cewa yahudawa akalla 500 suna halaka sanadiyyar hare-haren da sojojin Iran suka kai a kan HKI a yankin kwamaki 12. . Ya ce sojojin yahudawan sun saba boye yawan mutanen...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya fadawa shugaban majalisar tarayyar Turai Antonio Costa, kan cewa huldar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA zai kasance tare da sharudda. Saboda hukumar ta yi watsi da ayyukanta na asali ta koma siyasa. Ta fita daga bangaren kwararru ta zama tana bin bukatun wasu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar ta IAEA a da can ta zuciya guda ce, bata boyewa hukumar wani abu a cikin ayyukanta na makamashin Nukliya. Amma a halin yanzu mun gano cewa hukumar ce take bawa HKI bayanai dangane da ayyukammu na Nikliya ta kuma bada sunaye dadireshin masana fasahar Nukliya na kasar HKI ta zo ta kashesu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Har ya zuwa yanzu, ’ya’yan JKS na ci gaba da nuna kyawawan misalai a fannin yayata manufar samar da ci gaba mai inganci, da kyautata jagoranci tun a matakin farko, da sauke nauyin dake wuyansu, da gudanar da ayyuka masu cike da kalubale, wanda hakan ya zamo kashin bayan ingiza nasarar jam’iyyar da ma kasar Sin baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban yahudawan Iran Rabbi Younes Hamami Lalezar ya  ce, Isra’ila tana amfani da addini yahudanci domin cimma manufofinta, tana kuma bayyana Iran a matsayin wacce take fada da addinin yahudanci,alhali a cikin iran da akwai zaman lafiya tsakanin Mabiya dukkanin addinai. Haka nan kuma ya ce, kiyayyar da Isra’ila take da shi akan Iran ne, yake sa take jinginawa Iran din kin jinin yahduawa,wanda aikin ‘yan sahayoniya ne su samar da rabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Iran bisa addini da kuma kabila. Isra’ila tana bayyana kanta a matsayin mai bai wa yahudawa kariya, sai dai  da dama daga cikin Mabiya addinin yahudanci, wadanda ba ‘yan sahayoniya ba, suna zarginta da amfani da addini saboda manufofi na siyasa. Fiye da  shekaru ...
      Ganin irin yawan kalubalen tattalin arziki da siyasa a Arewacin kasan nan ya sanya Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya kaddamar da wata sabuwar kungiya mai taken Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative.   An kaddamar da wannan kungiyoyi ce a wajen wani babban taro da aka gudanar a Arewa House, Kaduna, inda manyan baki da mahalarta daga sassa daban-daban na Arewa suka halarta.   A yayin taron, Bafarawa wanda shi ne Shugaban Kwamitin Amintattu na tafiyar, ya bayyana wannan mataki a matsayin sabon hanyar da za ta yi maganin baraka da inganta fahimtar juna da kuma karfafa ci gaban mai dorewa a yankin Arewa.   Ya ce Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da...
    A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adam. A cikin sakonsa, Xi ya jadadda niyyar Sin na hadin gwiwa da kasashe daban-daban, don tabbatar da shawarar raya wayewar kan duniya bisa tushen adalci, da koyi da juna, da mu’ammala da yin hakuri da juna, ta yadda za a kafa nagartaccen tsarin mu’amalar wayewar kan bil Adam a duniya, matakin da zai gaggauta bunkasa wayewar kan bil Adam, da bunkasar duniya cikin lumana. Shugaba Xi ya kuma yi fatan mahalarta taron za su zurfafa mu’amala, da cimma matsaya daya, da taka rawar ganin wajen karfafa cudanyar al’ummun kasa da kasa, da...
    Wannan sabon birni na da ganuwa mai tsawon kilomita 8.5 da zai kare Legas daga ambaliyar ruwa, kuma yana da gidaje, ofisoshi da wuraren kasuwanci da na nishaɗi. Dangote ya ce wannan aiki yana daga cikin manyan abubuwan tarihin da Shugaba Tinubu zai bari. Hakazalika, ya nuna godiyarsa bisa fara aikin titin gaɓar teku daga Legas zuwa Kalaba da kuma aikin titin Sakkwato zuwa Badagry, waɗanda za su inganta sufuri da tattalin arziƙi a faɗin ƙasar. Ya kwatanta hangen nesan Tinubu da yadda ƙasar Netherlands ta kasance wajen samar da muhallai a cikin ruwa don raya birane. Dangote ya ƙara da cewa kamfaninsa na jin daɗin irin goyon bayan da gwamnati ke ba shi wajen sauƙaƙa kasuwanci da bunƙasa tattalin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, sata, zamba da kuma tayar da hankalin jama’a. An kama waɗannan mutane ne ƙarƙashin sabon samamen da rundunar ta ƙaddamar mai suna “Operation Kukan Kura” wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli, 2025. Kotun ƙoli ta tabbatar da Okpebholo a matsayin gwamnan Edo Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Alhamis. Ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na ƙoƙarin daƙile aikata...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, sata, zamba da kuma tayar da hankalin jama’a. An kama waɗannan mutane ne ƙarƙashin sabon samamen da rundunar ta ƙaddamar mai suna “Operation Kukan Kura” wanda ya fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli, 2025. Kotun ƙoli ta tabbatar da Okpebholo a matsayin gwamnan Edo Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai a ranar Alhamis. Ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na ƙoƙarin daƙile aikata...
    Gwamna Malam Umar Namadi na Jihar Jigawa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na farfado da harkar kasuwanci mara shinge a Maigatari, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin ginshikin bunkasar tattalin arziki, kasuwanci da masana’antu a jihar. Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Kwamandan Yankin K da Jigawa na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Kwamanda Dalhat Abubakar, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a Fadar Gwamnati da ke Dutse. Gwamna Namadi ya taya Kwamanda Abubakar murnar nadin nasa, tare da yaba wa hukumar Kwastam bisa goyon bayan manufofin cigaban jihar Jigawa, musamman wajen farfado da aikin Maigatari da aka yi watsi da shi. Ya nuna godiya bisa goyon bayan  Kwamandan ya bayar, tare da yabawa da rahotannin da ke...
    Ministan Tsaron Iran ya bayyana cewa: Hare-haren da Iran ta kai ne suka tilasta wa gwamnatin mamayar Isra’ila daukan matakin tsagaita bude wuta Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana cewa: Munanan hare-haren da sojojin kasar Iran suka kaddamar a matsayin mayar da martani ga yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita bude wuta. A wata tattaunawa ta wayar tarho guda biyu da ya yi da ministocin tsaron Venezuela da Armeniya, Birgediya Janar Nasirzadeh na rundunar sojin sama ya jaddada cewa: Hare-haren da sojojin Iran suka kaddamar kan yahudawan sahayoniyya ne suka kai ga neman tsagaita wuta. Ministan tsaron na Iran ya kara da cewa: Sojojin kasar Iran sun shirya tsaf domin mayar da martani ga...
    Kwamandan sojojin kasa na sojojin Iran ya jaddada wajabcin Karin daukan matakan kare iyakokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kwamandan sojojin kasa na kasar Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya jaddada wajibcin kare cikakken kan iyakokin kasar akida, al’adu, da yanki, yana mai cewa: Dole ne dukkanmu al\umma su zama masu kare wannan kasa da kuma samun kwarin gwiwa daga tafarkin shahidai. A yayin wata ganawa da iyalan shahidan kwanaki 12 da gwamnatin sahayoniyawa ta kakaba wa Iran a birnin Sarpol-e Zahab na lardin Kermanshah a ranar Larabar da ta gabata, Birgediya Janar Heidari ya bayyana cewa: Sojojin kasar suna kan gaba wajen kare ‘yancin kai da yankinsu na kasar, kuma a kodayaushe suna nuna godiya da irin hakurin da iyalan...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa; Mayar da martanin Iran ga ‘yan sahayoniyya sun murkushe girman kan makiya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Martanin da Iran ta mayar wa yahudawan sahayoniyya a lokacin arangamar da suka yi a baya-bayan nan abin nuni ne, domin kuwa a duk tsawon tarihin haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta taba samun irin wannan martanin mai gauni ba. Ghalibaf, wanda ya karbi bakwancin jakadan Belarus a birnin Tehran, Dmitry Kaltsov, a jiya Laraba, ya yaba da matakin da gwamnatin Belarus ta dauka dangane da hare-haren da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka dauika na kai wa cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran hare-haren wuce gona da iri. Yana mai...
    Manjo Janar Hatami: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Dakarun tsaron sama na sojojin Iran sun cimma wani gagarumar nasara a yakin da suka yi da makiya yahudawan sahayoniyya. A wata ganawa da iyalan shahidi Kanar Bostan Afrouz, Manjo Janar Hatami ya kara da cewa: Makiya sun kasa cimma tsare-tsare da shirye-shiryensu da suka rigaya sukaaniyar cimmawa, kuma sun fuskanci mummunar martani da shan kashi. Ya ci gaba da cewa: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya duk da karfin soja da kudi da suke da su, baya ga bayanan sirri da suke tabbatar...
    Wani manazarci na Amurka ya bayyana sansanonin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da Iran ta kaiwa hare-hare Wani manazarci Ba’amurke ya tattara jerin sansanonin da Iran ta kai wa hare-harer a wata makala inda ya bayyana cewa: Iran ta samu nasara a yakin da ta yi da ‘yan sahayoniyya. Wani mai sharhi kan harkokin siyasa da ke zaune a birnin Washington Mike Whitney ya yi nazari kan dalilan da ba a bayyana dalilan da suka sa Iran ta yi nasara kan haramtacciyar kasar Isra’ila ba a yakin kwanaki 12 a wani bincike da ya gudanar. Yana mai cewa; “Me yasa ba zato ba tsammani gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince da tsagaita bude wuta da Iran?” Whitney ta rubuta a cikin...
    A harin, mutane 13 daga cikin baƙin suka rasu, ciki har da mata da yara. Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya bayyana cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin. Daga baya kuma, Kwamishinan ‘Yansandan zai yi jawabi a hedikwatar rundunar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.   Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi  ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya. NAJERIYA A YAU: Sarƙaƙiyar da ke gaban Haɗakar ADC: Atiku ko Peter Obi DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata. Domin sauke shirin, latsa nan
    Duk da haka, an kashe ɗaya daga cikinsu, sannan sojojin suka lalata wasu gine-gine da ke sansanin. Abin farin ciki, babu wani soja da ya jikkata ko rasa ransa a wannan farmaki, wanda hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa a yaƙin da suke yi da ta’addanci. Sojojin sun ƙwato kayayyaki kamar bindiga AK-47 guda shida, alburusai 90 masu ɗango 7.62mm, da kuma tutar Boko Haram Wannan nasara na daga cikin ci gaban da gwamnatin Nijeriya ke samu wajen fatattakar ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Tattaunawa na baya-bayan nan tsakakin HKI da Hamas ya tashi ba tare da wani ci gaba ba a birnin Doha na kasar Qatar. Idan an cimma wannan yarjeniyar dai ana saran musayan fursinoni 10 na HKI sannan za’a saki wasu da dama dake hannun HKI, Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa rashin nasarar wannan taron ya sanya makomar yaki a Gaza cikin rudu don yanzun kuma ba’a san abinda zai faru ba. Kuma bamu san manufar HKI ba a wannan yakin. Wani jami’in Falasdinawa ya fadawa tashar talabijin ta Al-Sharq kan cewa da alamun tawagar yahudawan sunzo ba taren da niyyar cimma wani Abu ba, tunda duk abunda aka  tambayesu sai suce sai sun tambayi tel-Aviv,...
    Ya ƙara da cewa, Tinubu na mutunta dimokuraɗiyya da doka. Haka kuma, gwamnati ta san cewa ba za ta iya aiki yadda ya kamata ba tare da kafafen yaɗa labarai ba. Idris ya ce a baya, wasu jami’an gwamnati suna sukar gwamnati, amma shi kullum yana tattaunawa da ƙungiyar ’yan jarida da masu wallafa jaridu domin warware matsaloli cikin lumana. “Idan muna yin daidai, ku yabe mu,” in ji shi. “Idan kuma muna kuskure, ku faɗa mana cikin lumana domin mu inganta ayyukanmu.” Ministan ya ce gwamnatin Tinubu tana da kyakkyawar mu’amala da kafafen labarai kuma hakan zai ci gaba. Ya roƙi ’yan jarida ka da su ɗauki wasu ƙananan matsaloli su yi wa gwamnati hukunci a kai gaba ɗaya....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattaunawa da Firay minister da kuma yerma mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya Mohammad bin Salman kan karfafa dankon zumuncim  tsakanin kasashen biyu da kuma abubuwan da ke faruwa a yankin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran Aragchi ya hadu da dan sarkin ne a Makka, a ranar talata , kafin haka ministocin harkokin wajen kasashen biyu wato Faisal Bin Farhan kan wadan nan batutuwan. Dangantaka tsakanin kasashen biyu masu karfi a yankin, ya shiga cikin tsarin JMI na makobta da farko. Bin salman dangane rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da HKI da kuma Amurka, y ace yana fatan karshensa ya zama mai samar da zaman lafiya a mai dorewa...
    Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa wata ma’aikaciyar MDD takunkumi saboda yadda take amfanin laifukan yaki da take yi a gaza da kuma irin tallafin da Amurka take bawa HKI yasa tana da hannun a kissan kiyashin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa shi ya sa hannu a kan umurnin takunkuman da aka dorawa Francesa Albanese, jami’a mai kula da tattara bayanai na musamman a kan Falasdinu ga hukumar kare hakkin bil’dama da MDD. Rubio ya bayyana cewa sanadiyyar rahoton ta ne kotun ICC ta fidda samacin kama Banyamin Natanyaho, da kuma tsohon ministansa na Tsaro Yoav Galant. Banda haka takan bada rahoto kan yadda Amurka da...
    Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, ciki har da ɗan sanda da ’yan sa-kai guda uku, a wani hari da ’yan bindiga suka kai garin Mongoro da ke Ƙaramar Hukumar Mariga, a Jihar Neja. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Laraba. Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II ’Yan ƙabilar Ibo ne suka fi aikata laifi a Jihar Anambra ba Fulani ba — Gwamna Soludo Mazauna garin Wamba, sun ce har yanzu suna cikin fargaba saboda ‘yan bindigar ba su bar yankin ba. A ranar 24 ga watan Yuni, maharan sun kai hari wani sansanin sojoji da ke Kwanan-Dutse, inda suka kashe sojoji 17, tare da jikkata wasu 10. A cewar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamana Charles Soludo na Jihar Anambra ya ce mafi rinjayen kaso na waɗanda jami’an tsaro ke kamawa da aikata laifuka tsawon shekara uku da suka gabata ’yan kabilar Ibo ne. BBC ya ruwaito Soludo yana bayyana hakan a yayin wani taro da ’yan asalin jihar mazauna ƙetare suka gudanar a Amurka. Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya Soludo wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne ya yi watsi da zargin da ake yi wa Fulani makiyaya na aikata satar mutane a jihar. “Yanzu shekara uku da wata uku ke nan ina kan mulki. Idan muka kama masu laifi 100 to kashi 99 cikin 100 matasan ƙabilar...
    Tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgediya  Muhsin Rizai, ya sanar da cewa; Dakarun IRGC sun yi nasarar harbo jirage manya da marasa matuki na HKI har guda 80, kuma da akwai baraguzai 32 daga cikinsu da ake rike da su. Birgediya Rizai ya kuma kara da cewa; Daga cikin wadanda aka harbo din da akwai samfurin “Hermes” da “Hermon” da sune kira ta karshe da ‘yan sahayoniya suke takama da su. Birgediya Muhsin Rizai wanda memba ne a majalisar fayyace maslahar tsarin musulinci ta Iran, wanda tashar talbijin ta yi hira da shi da marecen jiya Talata, ya yi Magana akan bangarori da dama na  kallafaffen yakin kwanaki 12 inda ya ce:” Gabanin mu yi...
    Shugaban kungiyar Kurdawa ta kasar Turkiya ( PKK) Abdullah Ojlan ya sanar da kawo karshen amfani da makamai a fafutukar da kungiyarsu take yi na kare hakkokinsu a kasar Turkiya. Shugaban kungiyar Kurdawan na Turkiya wanda yake tsare a kurkuku na shekaru masu tsawo, ya aiko da sako na bidiyo da a cikin ya ce; Har yanzu ina kan kiran da na yi a ranar 27 ga watan Febrairu  na ajiye makamai”. Ojlan ya kara da cewa; Muna sanar da kawo karshen amfani da makamai ne bisa radin kanmu, haka na kuma ya ce; Mun shiga Zangon aiki da doka da kuma siyasa da tsarin demokradiyya, wanda shi kanshi nasara ce mai dimbin tarihi ba asara ba.” Kuniyar PKK ta...
    A yau Laraba, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanya wasu kamfanoni 8 na yankin Taiwan cikin jerin sunayen wadanda aka takaita sayar muku kayayyaki. Sanarwar da ta fito daga ma’aikatar ta ce, an dauki matakin ne domin kiyaye tsaron kasa da kare muradunta da kuma cika wajibcin hakkin kasa da kasa kamar hana yaduwar abubuwa masu cutarwa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanarwar ta ƙara da cewa mutane 3,824 da suka yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin jiha sun samu N7,960,162,598.64, yayin da 4,833 daga ƙarananan hukumomi aka tantance kuma an biya su N5,983,876,606 a matsayin garatuti. A jimlace, an biya N13,944,039,204.64 a matsayin kuɗaɗen garatuti. Gwamna Lawal bayan ya karbi rahoton ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen daidaita biyan haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati, musamman waɗanda suka yi ritaya bayan shekaru 35 suna aiki kuma suka kai shekaru 60.   “Gwamnatinmu ta gaji sama da Naira Biliyan 13 a matsayin bashin kuɗaɗen garatuti na waɗanda suka yi ritaya daga Jiha da Ƙananan Hukumomin daga 2011 zuwa 2023, jinkirin ya jawo wahalhalu, kuma wasu da suka yi ritaya sun mutu su na...
    Karuwar tasirin da kasar Sin ke yi a fagen ci gaban kimiyya da fasaha a duniya ba barazana ba ce, sai dai wata dama ce ta kawo ci gaba mai gamewa. Diamond ya kara da cewa, “Kasancewar na yi aiki kafada da kafada da wasu jami’o’i da cibiyoyin kasar Sin na tsawon shekaru masu yawa, na yi amanna da yadda kasar Sin ta dukufa ga samar da kimiyya da fasaha mai bude kofa ga duk duniya bisa adalci.” Kazalika, masanin kimiyya, mamba a makarantar nazarin kimiyya da fasaha ta Afirka, Farfesa Felix Dapare Dakora, ya nuna yadda kasar Sin ke karfafa shigar kasashe masu tasowa cikin harkokin kimiyya a duniya. Yana mai cewa, “A halin yanzu, an gode da samuwar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan  sahayoniyya kan kasar Iran Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren. Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari. A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a...
    Shi ma Uban taro mai masaukin baki, shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya bayyana a jawabinsa na taron kolin cewa, “Idan har ba a samu sauyi a tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa a wannan karni na 21 ba, to ya zama wajibi kasashen BRICS su taimaka wajen ganin an sabunta shi.” BRICS taska ce ta hadin kai, daidaito da kuma kokarin tafiya tare don samun ci gaba da tsira tare, da kuma karfafawa kasashe masu neman ‘yancin fadin albarkacin bakinsu a harkokin tsare-tsare na hadin kan kasashen duniya. Taron kolin kungiyar na bana, na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwannin duniya ke cike da firgici biyo bayan yakin cinikayya da kasar Amurka ta kaddamar,...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki. Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a...
    Shugaban Majalisar Kolin siyasar kasar Yemen ya jaddada ‘yancin kowa da kowa wajen gudanar da zirga-zirga a teku in banda makiya ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen, Field Marshal Mahdi al-Mashat, ya jaddada aniyar kasar ta Yemen na ba da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa ga kowa da kowa in banda makiya yahudawan sahayoniyya da kuma masu goya musu baya a lokacin da suke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza. A cikin wata sanarwa da Al-Mashat ya fitar ya ce: Ba su da wani sha’awar kai hari ga duk wanda ba shi da alaka da goyon bayan makiya yahudawan sahayoniyya, yana mai kira ga dukkanin kamfanonin jiragen ruwa da su...
      Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan.   Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyara ta jaje ga iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a Zaria, inda ya nuna alhini da ta’aziyya ga dangin waɗanda wannan al’amari ya shafa.   Tsohon Akanta Janar na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Kajuru, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai jaddada cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na kashe...
    Jam’iyyar ADC ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu shugabanni daga yankin Kudu sun buƙaci Atiku Abubakar, da ka da ya fito takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce wannan labari ƙarya ne, wanda aka ƙirƙira don haddasa rikici , musamman a wannan lokaci da ake ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya. Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense Jam’iyyar ta ce: “Ba mu taɓa zama da wasu wakilai daga Kudu domin yin irin wannan magana ba. “Wannan rahoto ba kawai ƙarya ba ne, yana kuma...
    Amma yanzu, sabon tsarin ya rage wa’adin bizar zuwa wata uku kacal, kuma mutum zai iya shiga sau ɗaya ne kawai da ita. Ma’aikatar ta ce wannan mataki yana daga cikin gyaran tsarin alaƙar diflomasiyya da tsaro da Amurka ke yi da sauran ƙasashe. Sai dai ta bayyana cewa za a iya sauya wannan tsari a nan gaba, idan an samu canji a dangantakar diflomasiyya, tsaro ko dokokin shiga ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan ya janyo tambayoyi kan ko za ta iya komawa nan take. A lokacin da aka tambaye ta me take yi a lokacin da aka dakatar da ita, Sanata Natasha ta ce ba ta tsaya ba, har yanzu tana gudanar da ayyuka tare da wakiltar mutanenta. “Na kasance ina aiki a duk lokacin. Na ci gaba da aiki kuma ina shirin gabatar da wasu dokoki a kan ma’adanai. Ba zan iya miƙa su ga wani ba,” in ji ta. Ta ƙara da cewa duk da cewa ba ta halartar zaman majalisa, ta ci gaba da yin ayyukan ci gaba ga mutanenta. “Fitar da ni daga majalisa ba kawai ni aka daƙile ba, an hana muryar Kogi ta Tsakiya fitowa fili,”...
    Gwamnan jihar Texas ta Amurka ya ce sama da mutane 160 ne har yanzu ba a gano ba sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a ranar Juma’ar da ta gabata. Greg Abbott ya ce wannan adadi na lardin Kerr ne kaɗai, ɗaya daga cikin wuraren da lamarin ya fi muni. Hukumomi dai sun bayar da rahoton mutuwar fiye da mutum 100. Masu aikin ceto na aiki a sannu a ƙoƙarin kawar da tarkacen da ruwan ya janyo domin gano ko akwai mutanen da ke maƙale a ƙarƙashinsu musamman a yankin gaɓar kogin Guadalupe. A jihar New Mexico da ke makwabtaka da Texas, ruwa ya tafi da wani gida inda wani uba ke zaune da ‘ya’yansa biyu a yankin Ruidoso, kuma...
    Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Ilorin ta kai wa daliban makaranta yakin da ta yi da cin hanci da rashawa domin fadakar da su illar cin hanci da rashawa.   Da yake jawabi ga dalibai a makarantar Nursery da Primary School, Tanke, Ilorin, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a, Daraktan Hukumar EFCC, Ayodele Babatunde, ya ilmantar da daliban a kan ma’anar cin hanci da rashawa, daban-daban da illolinsa da yadda kowa da kowa, ciki har da yara, za su iya bayar da tasu gudunmuwar wajen gina Nijeriya mara cin hanci da rashawa.   Ya ce cin hanci da rashawa yana yin abin da bai dace ba ne, musamman idan ya shafi wasu...
    Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, ta bayyana kudurinta na kara zurfafa dangantakarta da kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen jihar Kano.   Wannan alkawari ya fito ne daga bakin kwamandan sashin, Kwamandan Corps Muhammad Bature, a lokacin da yake karbar sabbin shugabannin majalisar a hedikwatar hukumar FRSC da ke Kano.   Sabbin shugabannin kungiyar masu aiko da rahotanni ta NUJ sun ziyarci hukumar FRSC ta Kano domin taya rundunar murna kan kokarin da take yi na inganta hanyoyin kiyaye hadurra da kuma gano sabbin hanyoyin hadin gwiwa.   Kwamandan sashin ya yi maraba da ziyarar, inda ya bayyana ta a matsayin wata babbar alama ta tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin FRSC da...
    Kungiyar Kano Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (Kano-ACReSAL) ta kaddamar da yakin neman ilimin sauyin yanayi zuwa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta ’Yan Mata da ke Kano a wani bangare na shirinta na “Catch Them Young”. Wato Ilmantar da Matasa.   Gangamin wayar da kan jama’a wani bangare ne na kashi na biyu na yunkurin aikin na jawo dalibai, malamai, da kwararrun muhalli wajen tattaunawa kan sauyin yanayi da kuma shigar da matasa wajen magance shi.   Mukaddashin mai kula da ayyukan, Dr. Abdulhamid Bala, ya sanar da daliban cewa sauyin yanayi ya kasance babban kalubalen da ba za a yi watsi da shi ba.     “Sauyin yanayi ya kasance barazana mai dorewa ga dorewar duniya. Amsarmu dole ne...
    An kaddamar da jam’iyyar African Democratic Party, ADC a Gombe mako guda bayan wasu jiga-jigan ‘yan adawa sun hada kai cikin jam’iyyar.   Shugaban jam’iyyar ADC a jihar Gombe kuma tsohon ministan sufuri Alh. Idris Abdullahi, ya ce makasudin shiga jam’iyyar shi ne ceto kasar nan daga kangin tattalin arziki da dora ta kan turbar ci gaba.   A cewarsa gamayyar jam’iyyun adawa sun zabi jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyya daya tilo da za ta samar da hanyar kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027.   Sanata Idris Abdullahi ya jaddada kudirin kungiyar a Gombe na ci gaba da kasancewa da hadin kai domin cimma burin ta.   Shugaban jam’iyyar ADC na jihar Gombe Alh. Auwal Barde ya ce...
    Na Biya Bashin Garatutin Naira Biliyan 13.6 Da ’Yan Fanshon Zamfara Ke Bi Tun 2011, Inji Gwamna Lawal Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana jin daɗinsa na biyan bashin Naira Biliyan 13,944,039,204.64 da aka riƙe wa ’yan fansho a Zamfara tun daga shekarar 2011 zuwa 2023. A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin aiwatar da ayyukan fansho tare da karbar rahoto daga kwamitocin haɗin gwiwa kan biyan bashin kuɗaɗen garatuti da aka yi a gidan gwamnati da ke Gusau. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, warware tarin bashin kuɗaɗen guratuti da fansho da aka tara daga shekarar 2011 zuwa 2023 na ɗaya...
    Mai magana da yawun matatar Dangote, Mista Anthony Chiejina, ya tabbatar da rage farashin a Legas. Ya ce, “Farashin man fetur ya ragu daga Naira 840 zuwa Naira 820 kan kowace lita.” Ya bayyana cewa rage farashin da aka yi a baya zuwa Naira 840 ya faru ne sakamakon hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya sanadiyyar rikicin da ya auku a Gabas ta Tsakiya. Kamfanonin da ke haɗa kai da Dangote irin su MRS, Heyden, Ardova (AP), Hyde, Optima, da Techno Oil za su fara sayar da fetur a sabon farashin. Haka kuma, wasu sabbin kamfanonin da ke dillancin mai sun shiga jerin masu rarraba man Dangote. Kamfanonin sun haɗa da: TotalEnergies, Garima Petroleum, Sunbeth Energies, Sobaz Nigeria Ltd., Virgin...
    Tsohon babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci wato IRGC ya bayyana cewa a yakin da JMI ta fafata a cikin watan da ya gabata , ya tabbata cewa JMI tana iya yaki da Amurka da HKI a lokaci guda. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Mohsen Rezaei, yana fadar haka a lokacinda wata talabijin ta cikin gida take hira da shi a jiya Talata . Labarin ya kara da cewa Janar Rezaei ya taba rike mukamin babban kwamandar rundunar IRGC jim kadan bayan nasarar juyin juya halin musulunci a shekara 1979. Yace: Shahid Janar Qasem Sulaimani, Babban kwamandan rundunar Qudus ne  ya fara furta zancen cewa , Iran tana da karfin fuskantar Amurka....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci taron mataki na 2 da na 3 na ganawar shugabannin BRICS karo na 17 da aka gudanar a Rio de Janeiro hedkwatar kasar Brazil, tsakanin ranakun 6 zuwa 7 ga watan nan da muke ciki, tare da gabatar da jawabi. Li ya ce, hadin gwiwar kasashen BRICS dole ne ya nace ga matsayin kiyayewa da tabbatar da cudanyar bangarori daban-daban a duniya, da gaggauta kafa tsarin ciniki da tattalin arzikin duniya mai adalci da bude kofa, da hada kan kasashe masu tasowa, don taka rawar gani ga samun bunkasar duniya mai dorewa. Ya kara da cewa, ya kamata a dukufa kan shimfida halayen tattalin arzikin duniya mai bude kofa, da daga matsayin hadin...
    Kamfanin CRCC na Sin ya cimma nasarar kammala shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 135 a jiya Litinin. Aikin ya kasance mataki na farko na shirin shimfida layin dogo na farko a hamadar Afrika, na jiragen kasa masu dakon kayayyaki mafiya nauyi, wanda zai hada jihar Bechar da yanki mai samar da karfe na Gala Jebilet a Jihar Tindouf dake yammacin kasar Aljeriya. Gwamnan jihar Tindouf Mustapha Dahou, da babban darektan CRCC Dai Hegen sun halarci bikin kammala aiki. A gun bikin, Dahou ya ce, CRCC da jiharsa, sun yi hadin gwiwar daga matsayin layin dogon zuwa masana’antu, matakin da ya ingiza bunkasar tattalin arzikin wuri zuwa mataki na gaba. Ya kuma yi fatan bangarorin biyu za su kara hada...
    Fim din  Iran mai taken: Akharin Kuse Nahang” wanda Ramtin Balf ya shirya shi ya samu kyauta a baje kolin fina-finan ta Shangahi. Shugaban ma’aikakar al’adu da koyarwar musulunci ta Iran a yankin Bu-Shehr Muhammad Hussain Zaduyan ya sanar da cewa; Fim din wanda na ilmantarwa ne, yana daga cikin fina-finai masu muhimmanci da aka fitar da shi a Iran. Shi dai wannan bikin  na baje kolin fina-finai a Shanghai an yi shi ne daga ranar 3 ga watan Yuli zuwa 7 ga gare shi a wannan shekarar ta 2025. An yi wannan bikin ne na baje-koli ne a daidai lokacin da ake yin taron kungiyar “BRICS” da taron kasashen Asiya. Zanduyani ya kuma ce; Fim din na Iran wanda...
    A matsayin sabon babban manaja, Musa ya buƙaci haɗin kai da goyon bayan kowa don tabbatar da gaskiya da amana a dukkan harkokin kulob ɗin. Ya kuma roƙi magoya bayan ƙungiyar su ci gaba da marawa kulob ɗin baya a wannan sabuwar tafiya ƙarƙashin jagorancinsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Amurkawa sun jefa bama-bamai a kan teburin tattaunawa tare da lalata harkar diflomasiyya Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce Iran na gudanar da shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, amma sai suka jefa bama-bamai a kan teburin tattaunawa tare da lalata hanyar diflomasiyya. A wata hira da Tucker Carlson mai watsa labarai na Amurka, shugaba Pezeshkian yayi magana da Carlson cewa: Mr. Carlson! Mun kasance a kan teburin shawara kuma ana cikin tattaunawa saboda shugaban Amurka ya kira zuwa ga zaman lafiya kuma a wannan taron sun gaya mana cewa gwamnatin Isra’ila ba za ta kai wani hari ba. Pezeshkian ya kara da cewa: Amma a jajibirin taro na shida, muna cikin...
    Kakakin hafsan hafsoshin sojojin Iran ya ce; Iran tana dora wa Amurka  alhakin duk wani hari da za a kai mata Kakakin hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Birgediya Janar Abul-fazl Shekarchi ya jaddada cewa: Iran tana dorawa Amurka alhakin duk wani harin wuce gona da iri da za a kaddamar kan kasarta. A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Mayadeen, Shekarchi ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran ba su ne suka kaddamar da harin kan wata kasa ba, amma sun mayar da martani cikin kwanaki 12 na arangama da munanan hare-hare da suka fuskanta daga mabartan ‘yan sahayoniyya makiya. Ya kara da cewa, “An sanya wa makiya tsagaita bude wuta ne bayan da suka fuskanci...
    Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka halaka yayin da wasu 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da aka kai musu a arewacin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka sheka lahira sannan wasu akalla 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da ‘yan gwagwarmaya suka kai a Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza. Har yanzu wani sojan Isra’ila ya bace kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka ruwaito. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da s’yan gwagwarmaya suka tayar da bam a cikin wata motar sojin Isra’ila mai sulke dauke da sojoji, sannan suka nufi wani mutum-mutumi da ke dauke da harsashi da makami mai linzami a lokacin...
    Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila.   Yana...
    Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta. ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun. Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba. “Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Wannan yajin aiki ba wata sabuwar tattaunawa ba ce,” in ji shi. “Abin da muke yi kawai martani ne ga halin ƙunci da mambobinmu ke ciki. Ofishin Akanta-Janar na ƙasa ne ke jinkirta biyan albashin da gangan.” ASUU ta ce ta riga ta gana da hukumomin gwamnati don bayyana matsalolinta, amma ba a ɗauki mataki ba. Farfesa Piwuna, ya kuma ƙara da cewa har yanzu malaman jami’a na bin gwamnati Naira biliyan 10 daga cikin Naira biliyan 50 da za a biya su a matsayin haƙƙoƙinsu (Earned Academic Allowances – EAA). Ya gargaɗi gwamnati cewa duk wata jami’a da ba a biya malamanta albashi ba, za ta ci gaba da yajin aiki har sai an warware matsalar. Daga kanmu,...
    “Mun riga mun binne sama da mutum 60 a Kukawa kaɗai,” in ji shi. “Wadanda suka tsira sun ce ‘yan bindigar sun fi ƙarfinsu.” Wani mazaunin ƙauyen Bunyun da ke gundumar Nyalun a ƙaramar hukumar Wase, Musa Ibrahim, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai hari ƙauyensu, inda suka kashe ‘yan sa-kai 10 da ke tsaron yankin. Musa ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun ƙone gidaje da dama a ƙauyen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas arachi ya bayyana cewa mutanen kasarsa a shirin suke su ci gaba da kare kasarsu daga Amurka da kuma HKI . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda yake ganawa da tawagar kasar Brazil a gefen taron kungiyar BRICS karo 17 wanda ke tafiya a halin yanzu a birnin Rio de Jenero na kasar Brazil. An gudanar da wannan taron ne saboda hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa JMI a baya bayan nan, da kuma tasirinsa a cikin al-amuran siyasa da kuma tattalin arziki a yankin Asiya ta yamma da kuma duniya gaba daya. Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren...
    Wata majiya wacce bata son a bayyana sunanta a nan Iran ta fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa a ziyarar da Benyamin Natanyaho yake yi a halin yanzu a kasar Amurka ya nuna cewa yana son ci gaba da yaki da kasar Iran sannan da alamun shugaba Trump yana tare da shi. Labarin ya kara da cewa matsayin shuwagabannin biyu a yanzun bai da bambanci da matsayinsu bayan yakin kwanaki 12. Majiyar ta bayyaa cewa Iran a shirye take ta kare kansa, kuma tana ganin ziyarar da Natanyahu yake a Amurka duk yaudara ce, saboda tuni sun rika sun yanke shawara kan ci gaba da yaki. Dangane da sake dawowa kan teburin tattaunawa da Amurka kuma,...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu a takardan doka ta soke kungiyar yan ta’adda ta Jihatun Nusra, wacce ake kira Hay’at Tahrirusham a matsayin kungiyar yan ta’adda a duniya. Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya, ya bayyana cewa shugaban ya cire HTSH daga jerin kungiyoyin yan ta’adda ne, saboda taimakawa kungiyar tabbatar da ikonta a kan kasar Siriya ta kuma share fagen dauke wa kasar takunkujman tattalin arzikin da aka dorawa kasar. Labarin ya kara da cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio ne ya sanya hannu a kan takardan cire shugaban kasar Siriya mai ci Ahmed Al-Sharaa ko wanda aka fi sani da Jolani daga jerin yan ta’adda a duniya. Wanda kuma...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ‘Yan Najeriya suna ci gaba da tafka muhawara a kan  wanda jamiyyar hadaka ta ADC zata tsayar takarar Shugaban Kasa a zaben 2027.   Yayin da wasu suke ganin Atiku Abubakar yana da dimbin magoya baya, wasu kuwa gani suke yi shi ma Peter Obi ba kanwar lasa bane. Ko me zai faru idan daya daga cikin su ya samu tikitin tsayawa takara a 2027? NAJERIYA A YAU: Mene ne tasirin naɗin Mataimaka na Musamman a rayuwar jama’a? DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wannan lamari. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ɗan wasan gaban Napoli, Victor Osimhen, ya amince da komawa Galatasaray na dindindin, wani ɗan jarida a Nijeriya kuma makusancin Osimhen, Buchi Laba ne ya bayyana hakan. Ya ce “Osimhen ya bayyana cewa yana son komawa Galatasaray daga Napoli, duk da cewar ƙungiyar ta ƙasar Italiya na fatan ci gaba da kasancewa da tsohon ɗan wasan na Lille, Bula ya rubuta a shafinsa na X. Manyan Kugiyoyin Gasar Firimiya Sun Fara Zawarcin Victor Osimhen Rashin Osimhen A Cikin Tawagar Nijeriya Babbar Asarace – Samson Siasia Yayin da yake zaman aro a Galatasaray, Osimhen ya taimakawa ƙungiyar ta lashe gasar Super Lig ta Turkiyya, ɗan wasan na Super Eagles ya zura ƙwallaye 25 a wasanni 36 da ya buga, hakan yasa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Yangquan na lardin Shanxi a yau Litinin. Shugaban ya ziyarci dandalin da aka kebe domin tunawa da katafaren gangamin soji na yaki da harin Japan, inda ya gabatar da furanni ga wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin. Ya kuma ziyarci babban dakin tunawa da gangamin. Shugaban ya kuma yi bitar irin jarumtar da sojojin suka yi yayin yakin da kuma tarihin yadda JKS ta jagoranci sojoji da al’umma wajen hada kai domin yakar ‘yan adawa da bijirewa kutsen Japan, da fahimtar tarihin juyin juya hali a wurin da gado da yayata ruhin yakin kin harin Japan. Daga baya, ya je wani kamfanin kere-kere na valve dake birnin, inda ya fahimci...
    Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar. Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga irin buƙatar da ake da ita wajen sauya sheƙa da kuma haɗin kan ƴan adawa, inda ya misalta abin da yake faruwa da shekara ta 2013, lokacin da aka samar da jam’iyyar APC wadda ta kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP a wancan lokaci. Shima wani masanin siyasa a Nijeriya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna yadda al’ummar ƙasar suke buƙatar...
    Kasar Sin ta gudanar da bikin cika shekaru 88, da dukkan al’ummar kasar ta fara yakin kin jinin harin sojojin Japan a yau Litinin. Inda a wani bangare na bikin aka kaddamar da wani baje koli mai taken “Domin ‘yantar da kasa da zaman lafiyar duniya”. An gudanar da bikin tare da baje kolin ne a babban dakin adana kayayyakin tarihi masu nasaba da yakin, wanda ke kusa da gadar Lugou, wadda kuma ake kira da “Marco Polo Bridge”, wurin da sojojin Japan suka fara kaiwa sojojin kasar Sin hari a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937, lamarin da ya zamo tushen mamayar da sojojin na Japan suka yiwa kasar Sin. Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS,...
    Kamfanin jirgin sama mallakar jihar Enugu, wato Enugu Air, ya fara aiki a hukumance ranar Litinin bayan ƙaddamar da shi a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu. Mutane da dama sun halarci bikin ƙaddamarwar tare da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da sauran manyan baki da suka halarci bikin ƙaddamarwar. APC Ta Tafka Asara, Wani Jigo Ya Fice A Enugu  Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu Enugu Air wani ɓangare ne na hangen nesa da ƙudurin Gwamna Peter Mbah, don inganta harkar sufuri da mayar da Enugu cibiyar jiragen sama a Nijeriya. Kamfanin ya fara aiki da jirage uku na Embraer E170 da E190, wadanda suka dace da zirga-zirgar cikin gida. Jirgin zai fara tashi tsakanin...
    An kashe mutane tara tare da jikkata wasu huɗu a wani da mayakan Boko Haram suka kai yankin a Malam Fatori da ke Jihar Borno. Gwamna Babagana Zulum, wanda baya kasar a halin yanzu, ya tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Sugun Mai Mele, domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa da kuma tantance halin da ake ciki. Mai Mele ya jaddada aniyar Gwamna Zulum na jajircewa wajen tabbatar da tsaron Malam Fatori saboda muhimmancinsa. Ya sanar da shirin tura manyan injina domin tona ramuka a kusa da hedikwatar ƙaramar hukumar don hana hare-hare nan gaba daga Boko Haram da ISWAP. Turji: Sai ka sako mutanen da ka sace za a yi sulhu — Gwamnatin Sakkwato Sarkin Ibadan ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da babban malamin yahudawa rabbi mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron BRICS a Brazil Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana kuma ya zanta da wani babban malamin yahudawa mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron kasashen BRICS a kasar Brazil. Rabbi Yisrael Dovid Weiss, wanda ya je Brazil domin ganawa a gefen taron BRICS, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, inda suka yi musayar ra’ayi da shi. Wani abin lura shi ne cewa a baya malamin ya ziyarci ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke kasar Brazil bayan bude littafin ta’aziyya ga shahidan da yahudawan sahayoniyya da suke kai wa hari a                                                                    kasar hari. A...