2025-08-14@11:56:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3191
«Ya ku mutane»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Shugaban kasar Kwango democradiyya Félix Tshisekedi, a gabatar da sauye-sauye a gwamnatinsa a jiya jumma’a inda ya shigo da sabbin ministoci guda biyu daga bangaren yan adawa. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika News’ ya bayyana cewa gwamnatinn kasar kwango ta fara wannan sauye –sauyen ne tun farkon wannan shekarar kuma har yanzun akwai wasu sauye –sauyen da zai gabatar a dai-dai lokacinda ake ci gaba da tattaunawa da jam’iyyun adawa da kuma yan tawayen M23. A wannan karon dai shugaban ya shigo da sanannun yan adawa guda biyu cikin gwamnatinsa, kuma sune, Adolphe Muzito, wanda ya taba zama firay ministan kasar, ya bashi matsayi na mataimakin firay minister, kuma shi ne zai kula da kasafin kudin kasar. Sai kuma...
Gwamnatin Tarayya ta naɗa Farfesa Mathew Adamu a matsayin sabon mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, wadda aka sake wa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon. Farfesa Adamu zai maye gurbin Farfesa Patricia Manko Lar, wadda ta riƙe wannan muƙamin na tsawon watanni shida tun daga Fabrairu 2025. Farfesa Adamu zai fara aiki daga ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, inda zai riƙe wannan muƙami na tsawon watanni uku. Farfesa Adamu ƙwararren masani ne a fannin likitancin dabbobi wanda ya fara karatunsa da digiri daga Jami’ar Maiduguri a 1998, sannan ya samu digirin digirgir a Jami’ar Pretoria, Afrika ta Kudu a 2012, an ɗaga darajar shi zuwa cikakken Farfesa a 2019. Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa Gwamnatin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan noma daga 2015 zuwa 2019, Audu Ogbeh, ya rasu a ranar Asabar, 9 ga Agusta, yana da shekaru 78 a duniya, kamar yadda iyalinsa suka tabbatar. A cikin wata sanarwa, iyalan sun ce: “Ya rasu cikin kwanciyar hankali, ya bar mana gado na gaskiya, hidima da jajircewa ga kasa da al’umma. Mun sami kwanciyar hankali daga yadda ya shafi rayuka da kuma yadda ya kafa misali.” Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – Inuwa Iyalan sun bayyana cewa za a sanar da yadda za a...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Shirin gwamnatin mamayar Isra’ila shi ne shirin share al’umma Falasdinu daga kan doron kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Shirye-shiryen da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take yi na mamaye yankin Zirin Gaza da kuma tilastawa al’ummar yankin gudun hijira wani karin shaida ne na musamman da wannan gwamnatin take da niyyar aikata kisan kiyashi a Falastinu da ta mamaye. Ismail Baqa’i ya bayyana shirin gwamnatin ‘yan sahayoniyya na mamaye garin Gaza da sojoji da kuma tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu a matsayin wani shiri na kammala kisan gillar da take yi wa al’ummar Falastinu, yana mai jaddada tofin Allah tsine da Allah wadai da wannan mummunan cin zarafi....
Kwamandan Dakarun Qudus na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Gudun da Amurka ta yi daga Yemen wani shan kaye na soji da ba a taba ganin irin sa ba Kwamandan Dakarun Quds na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ismail Qaani, ya kaddamar da wani kakkausar suka kan Amurka, yana mai bayyana sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na janyewa daga fagen daga a Yemen a matsayin “Halayen soja mafi wulakanci da kunya” a tarihin Amurka. A cewar wani faifan bidiyo da kafar yada labaran “Dakarun Qudus” suka wallafa a shafinsu na Telegram, Birgediya Qaani ya ce: Shugaban Amurka Donald Trump, da kansa ba wani ba—ba kawai kakakin...
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta janye shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya soki shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na kwace iko da birnin Gaza a jiya Juma’a, inda mai magana da yawunsa ya bayyana matakin a matsayin wani abu mai hadari. A nasa bangaren, Volker Turk, babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira a jiya Juma’a da a dakatar da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke da nufin wanzar da cikakken ikon soji a zirin Gaza ta hanyar mamaya. A cikin wata sanarwa da ta fitar sa’o’i kadan bayan da majalisar ministocin tsaron gwamnatin mamayar Isra’ila ta amince da kudurin...
Fitattun matsayi na kasashen Larabawa da kungiyoyi sun yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da matakin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Kasashe da kungiyoyin Larabawa sun yi Allah wadai da matakin da majalisar ministocin gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka mai hatsari na sake mamaye yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kusan miliyan daya gudun hijira daga birnin Gaza da arewacin zirin Gaza zuwa kudancin kasar. A cikin sanarwar da suka fitar a jiya Juma’a, sun yi la’akari da wannan shawarar da kuma shirin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a matsayin mai hatsarin gaske da zai haifar da bala’in jin kai a zirin Gaza kuma ba za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin ba, suna masu...
Mai ba da Shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da tsohon fira ministan Iraki sun jadadda goyon bayansu ga kugiyoyin gwagwarmaya Mai ba da shawara kan harkokin kasa da kasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tattauna kan ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya a wata tattaunawa ta wayar tarho da tsohon fira ministan kasar Iraki Nuri al-Maliki, kuma dukkansu sun jaddada goyon bayansu ga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa. A tattaunawar ta wayar tarho, Ali Akbar Welayati, mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasa, ya yi tambaya game da lafiyar tsohon Fira ministan Iraki Nouri al-Maliki. A cikin kiran, Velayati ya yi fatan samun koshin lafiya ga al-Maliki da samun sauki cikin gaggawa, inda ya...
Dortmund za ta buɗe kakar wasanta da Essen a zagayen farko na gasar cin kofin Jamus ranar 18 ga watan Agusta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun. ‘Yan Wasan Tsakiya Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini, ‘Yan Wasan Gaba Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo Ifeoma Onumonu, Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar yabo ta ƙasa ga kowace ‘yar wasa ta tawagar ƙwallon kwando a tawagar, tare da ba su kyautar gida a Abuja, a lokacin da yake jawabi ga tawagar, Shettima ya ce nasarar da suka samu alama ce ta ƙarfin haɗin kai. “Wannan nasara ta nuna abin da ke faruwa iɗan muka yi aiki tare, matan Nijeriya ba su tama bamu kunya a ɓangaren wasanni ba,...
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Masu Karya Tattalin Arziki ta Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa yawancin gidajen da aka yi watsi da su a Babban birnin Tarayya, Abuja, an gina su ne da kuɗin da ma’aikatan gwamnati suka sace. Olukoyede ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba a wani taron tattaunawa da zauren lauyoyi na Law Corridor ta shirya, mai taken “Muhimman Matsaloli da ke Addabar Harkar Gidaje a Najeriya.” Ya shaida wa mahalarta taron cewa EFCC ta kafa wata tawaga ta musamman da za ta fara binciken irin waɗannan gine-gine. “Za mu fara bibiyar dukkan gidajen, ba a Abuja kaɗai ba, har da sauran sassan Najeriya. Muna son sanin wa ke da su,” in ji Olukoyede....
Waɗan nan sune suka keɓe makomar Nijeriya, kuma suka yi garkuwa da ita. Har ila yau, a cewar majalisar dattawa ta 9 da ta yi bincike na sayar da ƙaddarorin gwamnati, wanan ɓarnar dukiyar ƙasa ne a rana tsaka, kuma kamar yadda ɗaya daga cikinsu ya bayyana kafin ya koma cikinsu, ya ce: “PRIƁATIZATION” ba komai ba ce face “PIRATIZATION” — wato sata da rabon ganima ce a fili. Waɗannan su ne masu kuɗi na yaki haram -yaki halas ,da suka ƙwace jam’iyyu, suka wawure zaɓuka, suka yi watsi da kowa sai nasu, suka kashe baitul-mali, kuma yanzu suna neman dawowa bisa kan Karagar Mulki da sunan dimokuraɗiyya. Wannan cutar dimokuraɗiyyar Nijeriya ce da ke ƙara bazuwa, kuma yaudara ne...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, ta wayar tarho a yau Jumma’a 8 ga wata. A tattaunawarsu, Putin ya bayyana ra’ayin kasar Rasha dangane da rikicin Ukraine a halin yanzu, da yadda Rasha ta tuntubi Amurka kwanan nan, inda ya ce, Rasha ta yaba sosai da muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a fannin shawo kan rikici ta hanyar siyasa. A nasa bangaren kuma, Xi ya jaddada matsayin kasar Sin, tare da bayyana cewa babu wata dabara mai sauki da ke iya magance matsaloli masu sarkakiya. Ba tare da la’akari da duk wani sauyi da za a fuskanta ba, kasar Sin za ta tsaya ga neman sulhu da gudanar da shawarwari....

Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka Sun Haɗa Gwiwa Don Wayar Da Kan ‘Yan Nijeriya Kan Sababbin Ƙa’idojin Samun Biza
Idris ya ce a tsawon shekaru ‘yan Nijeriya suna tafiya Amurka saboda dalilai daban-daban, ciki har da yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu, da kuma neman magani. Ya ce: “An san Nijeriya a duniya a matsayin ƙasar da ‘yan ƙasar ta suke yawan yin tafiya zuwa ƙasashe daban-daban, suna hulɗa da ƙasashen duniya ta fuskar harkar kasuwanci, ilimi, yawon buɗe ido, da sauran muhimman fannoni. Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suka fi ziyarta, abin da ke nuna zurfin dangantaka mai tsawo tsakanin ƙasashen biyu. “Yawancin ‘yan Nijeriya suna zuwa Amurka ne domin karatu, aiki, neman magani, ziyartar ‘yan’uwa, yawon buɗe ido, da damar zuba jari. “Wannan mu’amala mai ƙarfi tana...
Wannan irin jita-jitar tana kokain zana shi da kwatankwacin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sin ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na babbar kasuwar mutum-mutumin inji masu ayyukan masana’antu a duniya, wanda ta rike tsawon shekaru 12, kuma ita ce babbar kasa mai kera mutum-mutumin inji a duniya. Sin daya ce daga cikin kasashe masu samar da mutum-mutumin inji dake sahun gaba a duniya, kuma ana sa ran za su taka muhimmiyar rawa a fannonin hidimar gida da masana’antu da kayan ajiya. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa, daga cikin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa akwai mahaifiyar yaran wato Mariya Sani, ‘yar shekara 45 da kuma Mujahid Sani, ɗan shekaru 20, sai Zahariya Sani, ‘yar shekara 18. Sauran sun haɗa da Hauwa Sani, ‘yar shekara 15 da Amira Sani, ‘yar shekara 3 da kuma Nura Sani, ɗan shekara 5. Muhammad ya bayyana cewa yanzu haka akwai waɗanda suka samu raunuka, inda suke asibitin Katsina domin karɓar magunguna. Mahaifin yaran ya bayyana irin kaɗuwar da ya yi lokacin da ya samu labarin faruwar wannan al’amari, wanda ya ce ya yi wa Allah godiya, su kuma da suka rasu Allah ya jikansu. Yanzu haka dai ‘yan’uwa da abokan arziki na ci gaba da zuwa yi wa Malam...
Dabbobi 199 da aka sace (shanu 161 da tumaki 68) Motoci guda 3 da aka sace Babura 2 da ake zargi an sace su Miyagun ƙwayoyi da yawa ciki har da tabar wiwi Wayoyin wutar lantarki da aka lalata DSP Aliyu ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar jihar saboda haɗin kai da suka bayar, yana mai cewa ba za a cimma nasarorin ba tare da taimakon jama’a ba. Ya buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa ‘yansanda goyon baya, tare da kai rahoton duk wani abun zargi ta waɗannan layukan gaggawa: 0815697777722, 0902220969033, da 07072722539. “Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina za ta ci gaba da ƙoƙarinta don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar,” in ji shi....

Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da batan wasu 33. Shugaba Xi Jinping na bada muhimmanci sosai ga yanayin ibtila’i da mamakon ruwan sama ya haifar a wasu yankuna ciki har da gundumar Yuzhong na Lanzhou, babban birnin lardin Gansu. Cikin umarnin da ya bayar, Xi Jinping ya ce aiki na gaggawa shi ne yin dukkan mai yuwuwa wajen bincike da ceton mutanen da suka bata da ganowa da sake tsugunar da...
Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cikin fim din “Dead to Rights”, an ce, “Mu tuna da jinin da aka zubar a yakin, don mu kiyaye hasken da muke da shi yanzu.” Abin haka yake, yau mun waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ba don neman ci gaba da kiyaya da juna ba, a maimakon hakan, muna son kira ga al’ummomin duniya da su tsaya tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiya da magance yaki a tsakaninsu. Yakin duniya na biyu babbar masifa ce ga dan Adam, kuma irin ra’ayi da ake rike da shi game da tarihin yakin, ya zama wata jarrabawa ga dan Adam. A bana ake cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka samu nasarar yaki da mahara Japanawa, da ma...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar mutane a wajen cirar kuɗi a ATM. Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkareem, ya ce an kama Umar Abubakar mai shekara 24 da Abdulaziz Mohammad mai shekara 25 daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano. PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu An kama su lokacin da suke ƙoƙarin yaudarar wani mutum a wajen ATM na bankin Fidelity da ke Damaturu. Ana zargin matasan da amfani da wasu dabara wajen damfarar mutane ta hanyar nuna kamar suna taimaka musu, amma daga baya sai su sauya musu katin ATM. A wani...
An samu mummunan iftila’i a garin Pulka na ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno, inda fashewar Gurneti ya kashe yara uku a yammacin jiya Alhamis. Yaran da suka mutu sun haɗa da Fati Dahiru, Aisha Ibrahim da Fati Yakubu. Rahoton wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa, wani ɗan ƙungiyar CJTF, Buba Yaga, ya ce yaran na wasa da wani bam da ake zargin Boko Haram sun bari, kafin ya fashe da misalin ƙarfe 2:20 na rana. Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno Bayan faruwar lamarin, jami’an kunce bam (EOD) na Ƴansanda, da Sojojin Operation Haɗin Kai, da...
Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara A cewar Goɓspend, an kashe maƙudan kuɗaɗe a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu a tsakanin Afrilu da Agusta 2024 wajen kula da jiragen saman shugaban ƙasa. Farkon kashe kuɗaɗen a ranar 14 ga Yulin 2023, lokacin da aka biya naira miliyan 846.03 a matsayin kuɗaɗen tafiye-tafiyen shugaban ƙasa na wucin gadi. Kwanaki biyu daga bisani, an sake kashe naira miliyan 674.82. A wannan watan kaɗai, jirgin ya laƙume sama da naira biliyan 1.5. A watan Agusta, kashe kuɗaɗen sun ƙaru. An kashe...
Sayyid Abdul-Malik al-Houthi, shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya ja kunnen Amurka da HKI kan kara tada hankali a yankin Asia ta kudu. Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadin haka a jiya Alhamis, a lokacinda yake jawabi ga mutanen kasar jawabinsa na mako mako. Sayyid Huthi ya bayyana cewa kasashen biyu suna son ci gaba da yiwa wadan nan kasashen mulkin mallaka, da kuma mamayarsu. Yace: HKI ba abinda take so in kara fadada kasarta don kaiwa ga gurinta na Isra;ila babba, ya kamala da cewa kasashen biyu suna son tababatar da cewa tunaninsu na mulkin mallaka da kuma ci gaba da sace arzikin yankin. A wani bangare na Jawabinsa, Sayyid Huthi ya bayyana cewa, sojojin ...
Sakamakon kama Mu’azu Ɓarga, yanzu haka abokan ta’asar tasa sai tsallakewa suke domin tserewa kamun rundunar ‘yan sanda, duk da gudun da suke rundunar na ci gaba da farautarsu har kuma an samu nasarar ƙara damƙe mutane biyu cikin sama da mutane arba’in da Ɓarga ya bayyana wa ‘yan sanda. Wannan tasa a ranar Juma’ar da ta gabata Al’ummar Sheka ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Muryar Jama’ar Sheka ta ziyarci Shelkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai domin jinjina wa ƙoƙarinsu. Cikin shahararrun mafaɗatan da suka gamu da ajalinsu alokacin arangama daban-daban akwai matashin da ya addabi al’ummar Unguwar Ɗorayi mai Suna Barakita, sai kuma wani mai suna Khalufa ɗan unguwar Ƙofar Mazugal Da kuma wani guda da ke tafka irin wannan...
Sayyid Abdul-Malik al-Houthi, shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya ja kunnen Amurka da HKI kan kara tada hankali a yankin Asia ta kudu. Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadin haka a jiya Alhamis, a lokacinda yake jawabi ga mutanen kasar jawabinsa na mako mako. Sayyid Huthi ya bayyana cewa kasashen biyu suna son ci gaba da yiwa wadan nan kasashen mulkin mallaka, da kuma mamayarsu. Yace: HKI ba abinda take so in kara fadada kasarta don kaiwa ga gurinta na Isra;ila babba, ya kamala da cewa kasashen biyu suna son tababatar da cewa tunaninsu na mulkin mallaka da kuma ci gaba da sace arzikin yankin. A wani bangare na Jawabinsa, Sayyid Huthi ya bayyana cewa, sojojin ...
Wa jirgin sama na daukar marasa lafiya ya yi hatsari ya kuma fadi a kan gidajen mutane a kusa da birnin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya a jiya Alhamis.AMREF Flaying Doctor, jirgi ne karamin samfurin XLS ya tashi daga tashar jiragen sama na Nairobi da nufin zuwa wasu yankuna a kasar Somaliland ya fadi jim kadan bayan tashinsa. An ce matukin bai yi korafin ko akwai Malala a cikin jirgin ba, kuma wani wani gargadi sai kawai anji ya fadi. A halin yanzu dai ba’a san sababin faduwarsa ba, kuma jami’an tsaro basu bada wani bayani har yanzun yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba, ku kuma sunaye da kamanin ko matsayin mutanen da suke cikin jirgin ba. Har’ila...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari. Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah, ya bayyana haka yayin mika kayan kayan abincin na musamman da aka sayo ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da UNICEF a shirin Child Nutrition Match Fund, wanda aka gudanar a Cibiyar Kiwon Lafiya (PHC) ta Karamar Hukumar Takai. Mista Rahma, wanda Daraktan Lafiya na UNICEF, Dakta Serekeberehan Seyoum Deres ya wakilta, ya ce kashi 51.9 bisa 100 na yaran Kano suna fama da mat girma...
Mazauna kauyuka akalla 30 daga Dan-Isa da Kagara dake karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara, sun mamaye gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar domin nuna takaicinsu kan yadda rashin tsaro a yankin na su “yaki ci yaki cinyewa” a ranar Alhamis. Masu zanga-zangar da suka hada da mata da kananan yara suna dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce kamar: “Muna bukatar zaman lafiya a kauyukan Kaura-Namoda,” “Gwamna Dauda Lawal da Matawalle ku kawo mana dauki”, “Ana kashe mu kowace rana,” da dai sauransu. Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago Da yake jawabi a gidan gwamnati, jagoran masu...
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba. Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana. Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya biya Naira dubu 800 kafin a bar mazauna yankin su yi noma. NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti “Kowanne ƙauye kuma zai sake biyan Naira dubu 800, don bai wa mazauna yankin damar girbe amfanin gonakinsu, wannan ita ce yarjejeniya da muka cimma da shugaban ’yan bindiga da ke kula...
“An kashe da dama, kuma wasu da yawa sun sami munanan raunuka.” In ji Kaftin Adewusi Bayan farmakin ta sama, sojojin kasa na Birget 1 dake karkashin sashe na 2 na OPFY sun kaddamar da wani samame ta kasa a ranar 5 ga watan Agusta, inda suka yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna kan hanyar zuwa kauyen Yankuzo, inda rahotanni suka ce an kai ‘yan ta’addan da suka jikkata domin yi musu magani. A cewar majiyoyi da bayanan sirri daga Kauyen, an kashe ‘yan ta’adda fiye da 30 a yayin samamen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa. A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, shugaban ƙasar ya bukaci waɗanda aka naɗa su yi amfani da ƙwarewarsu wajen tabbatar da burin gwamnatinsa a fannin wutar lantarki. Onanuga ya bayyana cewa waɗannan nade-naden suna jiran tantancewar Majalisar Dattawa. Sai dai, domin kauce wa gibin shugabanci a hukumar, Shugaba...
Da yake la’antar kisan a matsayin “mummuna, dabbanci, kuma lamarin da ba za a lamunta ba,” gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da adalci. Ya umurci hukumomin tsaro da su dau mataki tare da kama wadanda ke da hannu a kisan nasa nan take. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da ƙwato jaririn da aka sace a wani asibiti da ke Ado-Ekiti ranar Litinin. An miƙa jaririn ga iyayensa, Mustapha Aliyu mai shekara 29 da kuma Salmatu Lawal mai shekara 22, bayan da jami’an ’yan sanda suka tsananta binciken lamarin. An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno A cewar Eribo, an samu nasarar ne bayan samun wani sahihin daga wani da ya ba da rahoto ya tuntuɓi wani babban jami’in ‘yan sanda, inda ya nuna shakku kan wata mata da ta yi imanin cewa tana da alaƙa da sace jaririyar da ta ji a cikin labarai....
Gwamnatin Jihar Jigawa ta biya iyalai 14 da aikin sake gina Babban Masallacin Gumel ya shafa kudaden diyya da suka kai Naira miliyan 277 da dubu 44. An gudanar da bikin bayar da takardun cekin kudin ne a Fadar Mai Martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmad Muhammad Sani, tare da halartar masu rike da sarautu, da shugabannin al’umma da manyan jami’an gwamnati. Da yake jawabi yayin bikin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, wanda Babban Sakataren Harkokin Gudanarwa da Kudi na Ofishinsa, Alhaji Abdullahi Sa’idu, ya wakilta, ya shawarci iyalan da su yi amfani da kudaden ta hanya mai amfani wajen gina sabbin gidajensu tare da rungumar sauyin wurin zama cikin hakuri da tawakkali. Malam Bala Ibrahim ya jaddada cewa...
Hukumar NDLEA ta Nijeriya da takwararta ta Indiya sun amince da yin aiki tare domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu. Wannan yarjejeniya ta fito ne daga wata tattaunawa ta kafar intanet tsakanin Shugaban NDLEA na Nijeriya, Janar Buba Marwa (mai ritaya), da shugaban hukumar ta Indiya, Anurag Garg. Shugabannin sun jaddada buƙatar haɗin gwuiwa, musamman wajen hana shigo da haramtattun magunguna daga Indiya zuwa Nijeriya. Marwa ya ce akwai buƙatar a ƙarfafa wannan dangantaka bisa yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu a shekarar 2023. Bayan Shekaru 7 Yana Ɓoye, NDLEA Ta Cafke Babban Dillalin Ƙwayoyi NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke Mutane 19 A Kano Buba Marwa ya roƙi hukumar Indiya da ta tallafa wa...
Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun fada alhini sakamakon rasuwar wasu mutum hudu ’yan gida daya. Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayakin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalin su. An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore Majiyoyin da ke kauyen na sun shaida wa rundunar ’yan sandan jihar cewa wadanda suka mutun sun hada da Yakubu Samanja, matarsa Esther Yakubu, da ’ya’yansu biyu, Amos Yakubu da Maryamu Yakubu. Wani dan uwan mamatan mai suna Ibrahim Samanja, ya ce ya gano faruwar hakan...
Majiyoyi daga cikin jami’an tsaron sun bayyana cewa sojoji da ‘yan sa-kai sun fafata da ‘yan bindigar. Sun kashe ‘yan bindiga da dama, sannan suka ƙwato bindigogi AK-47 guda uku daga hannunsu. ‘Yan bindigar sun gudu, wasu daga cikinsu na da raunuka ko kuma an kashe su, sai dai adadin ba a tabbatar da shi ba tukuna. Bayan faɗan ta yi tsanani, an tura ƙarin sojoji zuwa yankin domin ci gaba da matsa wa ‘an bindigar da suka tsere lamba tare da hana su sake kai hari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo. A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu. Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da rikicin da ya mayar da babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari daya daga cikin mafiya hatsari a Najeriya. Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Daga shekara ta 2015, mazauna yankin sun sha fama da hare-hare da garkuwa da su, yayin da matafiya kuma...
Shugaban Amurka, Donald Trump, yana shirin ƙara tsaurara wa Rasha takunkumi idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba kafin ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta. Ko da yake Rasha ita ce ƙasar da aka fi ƙaƙaba wa takunkumi a duniya, har yanzu tana amfani da arziƙin man fetur da iskar gas da ta ke da su domin ɗaukar nauyin yaƙin da ta ke yi da Ukraine. Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma Trump ya bayyana cewa zai sanya sabbin takunkuman da za su hana Rasha cin gajiyar kasuwanci da wasu ƙasashe. Daga cikin matakan, akwai sanya haraji har kashi...
Kwamishinan ya ce tuni ya ba da umarni a fara bincike kan waɗanda ake zargin. Ya kuma tabbatarwa da jama’a cewa duk wanda ya kawo ƙorafi za a saurare shi, ba tare da an tsananta masa ba. A cewar rundunar, an daɗe ana samun ƙorafi cewa wasu ɓata-garin ‘yansanda suna karɓar kuɗi daga masu laifi domin su rufa musu asiri. Amma wannan karon, hukumar za ta bi sahun ƙorafin domin ganin an yi gyara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Su dai kawai abin da suke alfahari da shi, shi ne dukiya, yawan gidaje da jirage. Ba su san cewa mutane na kallonsu a matsayin ɓarayi ba.” Sanusi II, ya ƙara da cewa ba shugaban ƙasa ko gwamna kaɗai ke da laifi ba, hatta shugabannin addini da sarakuna ma sun ɓaci a yanzu. “Yawancin shugabanninmu sun shiga ruɗani, babu wanda ya tsira,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara. Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da jahilci yake taimakawa wajen yaduwar cutar a kasar. A sassan Najeriya da dama dai, ba kasafai mutane ke iya bambance Zazzabin Lassa da sauran nau’ukan zazzabi ba. Shin yaya za a iya gane Zazzabin Lassa a kuma bambance da sauran nau’ukan zazzabi? NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A fannin noma ma, watsa shirye-shiryen da Sinanci zai taimaka wajen bayyana burin Nijeriya na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, musamman yadda take neman aikewa da karin kayayyakin amfanin gona zuwa babbar kasuwar kasar Sin, tare da bai wa masu ruwa da tsaki na kasar Sin damar sanin abubuwan da Nijeriya za ta iya yi, da ka’idojinta ta yadda hakan zai kara daidaita al’ummomin kasashen biyu kan dabarun kasuwanci da kara habaka musayar noma. A halin yanzu, masana’antun kirkire-kirkiren fikira da na fina-finai, da na kayan kwalliya, da kide-kide da wake-wake suna taka rawar gani wajen harkokin al’adu da kasuwanci. Watsa shirye-shirye da Sinanci zai bai wa masu ruwa da tsaki a wannan fani na kirkire-kirkiren fikira na Nijeriya...
Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa; Dole ne kasashen musulmi su hana ci gaba da aikata laifuka a Gaza Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim, ya jaddada bukatar kasashen musulmi su dauki matakin hana ci gaba da bala’in jin kai a Gaza ta hanyar diflomasiyya da kuma matsin lamba na siyasa. A safiyar yau Laraba ne shugaba Pezeshkian ya tattauna da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim ta wayar tarho, inda ya jaddada cewa: “Aikin ta’addancin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aiwatar a Gaza ba abin da za a amince da shi ba ne ga kowane mai ‘yanci,” yana mai bayyana fatansa na ganin “kasashen Musulmi za su yi aiki...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Taya Ali Larijani Murnar Nada Shi Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya taya Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasa Abbas Araqchi, ministan harkokin wajen kasar Iran, ya taya Ali Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar. A cikin sakon taya murna, Araqchi ya taya Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon sakataren majalisar koli ta tsaron kasar, tare da yi masa fatan samun nasara a sabon mukamin nasa. A cikin sakon taya murnarsa, Araqchi ya bayyana cewa, shi da takwarorinsa na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a shirye suke su ba da hadin kai sosai ga Larijani wajen gudanar da muhimman ayyukansa, musamman a fannonin diflomasiyya...
Da safiyar Larabar nan ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da taron tattaunawa game da batun rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda a jawabinsa game da aniyar Isra’ila ta tsananta hare-haren soji, da mamaye daukacin zirin Gaza, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana matukar damuwa kan hakan, yana mai kira ga Isra’ila da ta kauracewa wannan mataki mai hadari, yana mai fatan daukacin sassan da lamarin ya shafa za su gaggauta kaiwa ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta mai tsorewa. Geng Shuang, ya kuma jaddada muhimmancin aiwatar da sahihin mataki na dakatar da bude wuta yadda ya kamata, ta yadda hakan zai kubutar da rayukan al’umma, tare da bayar da damar sakin wadanda ake tsare...
Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya. Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta aiwatar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma’aikata masu ƙaramin albashi da ke ƙarƙashin tsarin fansho na haɗin gwiwa (Contributory Pension Scheme – CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare da zai taimaka wa rayuwarsu. A wata sanarwa da mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma bada umarnin a gaggauta aiwatar da karin fansho da aka dade ana jiran shi, tare da kafa mafi ƙarancin adadin fansho domin kyautatawa tsofaffin ma’aikata mafi rauni a tsarin CPS. Wannan umarni ya biyo bayan bayani da Daraktar Janar ta Hukumar Kula da Fansho...
Mutum 22 sun gamu da ajalinsu, yayin da wasu 20 suka jikkata, bayan wata babbar mota da ta yi lodin mutane da dabbobi ta yi hatsari a kan hanyar Lambata zuwa Lapai da ke Jihar Neja. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin. Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato Motar ta taso daga Kano zuwa Legas ne lokacin da hatarin ya auku da misalin ƙarfe 3 na safe, sakamakon gudun wuce ƙima. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta ce dukkanin fasinjojin da ke cikin motar maza ne. An kai gawarwakin Babban Asibitin Suleja, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati...
Malaman jami’o’i sama da 100 daga Isra’ila sun bayyana cewar jan kafar da ƙasar Jamus ke yi wajen ɗaukar matakin matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila na iya bai wa ƙasar damar ci gaba da aikata manyan laifuffuka a Gaza. Wata wasika da masanan suka rubuta wa ɗaya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar SPD da ke mulki a Jamus, ta ce rashin ɗaukar matakin na iya bada damar gudanar da wasu sabbin laifuffuka a Gaza, tare da watsi da irin tarihin da aka koya a shekarun baya. A ranar 22 ga watan Yuli, biyu daga cikin jiga jigan kawancen jam’iyyun dake jagorancin Jamus, sun bukaci ƙasar da ta shiga cikin ƙasashen duniya da ke ƙawance domin gaggauta kawo ƙarshen yaƙin Gaza...
A jawabin da Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ya yi ta bakin mataimakinsa, Farfesa Sanusi Rafindadi, ya yaba da yadda taron ke taimakawa wajen wayar da kai game da wannan cuta mai hatsari. Ya kuma gode wa Hajiya Fatima bisa amsa gayyatar jagorantar taron. Shugabar Sashen Kula da Mata, Farfesa Rahanatu Lawal, ta jaddada buƙatar haɗin kan kowa da kowa wajen yaƙi da cutar. Ta ce mata ba za su iya wannan yaƙi su kaɗai ba, dole ne maza su ba su goyon baya. Daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabi akwai Dakta Aminat Jimoh daga Asibitin Koyarwa na ABU. Ta buƙaci mata da su riƙa duba kansu akai-akai, musamman idan suna da tarihin ciwon a cikin danginsu. Ta...
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya kawata jami’ai 390 da aka daga matsayinsu zuwa sabon mukami a rundunar. An gudanar da bikin kawata jami’an ne a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Gusau, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sanda, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya taya sabbin jami’an murna tare da bukatar su tabbatar da cancantarsu da mukaman da aka ba su, ta hanyar rubanya kishin aiki, ladabi da kwarewa a ayyukansu. Ya jaddada bukatar jami’an da su dage wajen yin aiki da jajircewa da kuma bayar da ingantaccen tsaro ga al’ummar Jihar Zamfara da Najeriya gaba ɗaya. Daga cikin waɗanda suka sami...
Kakakin dakarun juyin juya halin musulun a nan Iran ya bayyana cewa nasarar da JMI ta samu na tunkude hare-harenda HKI ta kawowa kasar ya saya abubuwa da dama a bangaren siyasa da wasu al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto General Ali Mohammad Naeini yana fadar haka a wani wani taro na tunawa da daya daga cikin shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kallafawa kasar. Ya kara da cewa duniya ta sauya sabada nasarar sannan musamman a fagen diblomasiyya da kuma kafofin yada labarai a duniya, wanda ya bar tasiri mai kyau ga kasar. Labarin ya kara da cewa, akalla kasha 60 % na mutanen duniya...
‘Yansanda a kasar Iran sun bada labarin cewa suna amfani da jiragen leken asiri da wasu kayakin masu aiki da lantarki na zamani don tabbatar da lafiyar masu tattalin 40 zuwa wurare masu tsarki a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Ahmad Ali Goodarzi shugaban yansanda a nan kasar Iran ya bayyana cewa, yansandan kasar suna aiki tare da rana wajen kyautata ayyukan tsaro a dukkan kofofi shiga Iraki daga Iran guda 6 saboda tabbatar da tsaron masu zuwa 40 na Imam Hussain (a). Ya ce: Yansa a kan iyakokin kasar suna sanya kula da musamman a kofofin shiga kasar Iraki, wadanda suke da cinkoson mutane. Tare da amfani da jiragen marasa matuka...
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cikakken goyon bayan rundunar ‘yan sanda ga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano wajen tabbatar da kiyaye dabi’u da yakar munanan halaye a cikin al’umma. CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar wayar da kai da Sakatare na Hukumar, Abba El-Mustapha, ya kai tare da tawagarsa zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sandan Kano. A yayin ganawar, CP Bakori ya yaba da jagorancin hukumar, musamman kokarin da El-Mustapha ke yi wajen tsara harkokin masana’antar Kannywood da kuma kare tarbiyya ta hanyar sa ido mai tsauri. Ya tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin rundunar da hukumar, musamman wajen dakile cin zarafi da amfani da kafafen sada zumunta...
Mataimakin shugaban kasar Iran Muhamad Reza Aref ya bayyana cewa kasar Iran tana goyon bayan dukkan shirin zaman lafiya a yankin musamman tsakanin kasashen Armenia da kuma Azarzaijan. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aref yana fadar haka a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Armenia Vahagn Khashaturyan a kasar Tukeministan ake ake gudanar da taron kasashen wadanda basa kan bakin ruwa a duniya a ranar Litinin. Majalisar dinkin duniya ce ta take shrya wannan taron don ci gaban irin wadannan kasashe a duniya karo na 3TH. Aref yace yana fatan zaman zafiya ta dore a cikin kasashen yankin don amfanin kowa. Daga karshe mataimakin shugaban kasan Iran ya bayyana cewa Iran tana goyon bayan kasar Armenia ta...
’Yan bindiga sun sace mutum 150 a mabanbantan hare-haren da suka kai kauyuka daban-daban na jihar Zamfara a cikin kwana hudu. Kakakin Gwamnatin jihar ta Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa ne ya tabbatar da hakan ga BBC. Sai dai duk da yake bai bayyana hakikanin adadin mutanen da aka sace ba, amma ya ce gwamnatinsu na iya kokarinta wajen ganin ta ceto su. Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’ Haka na zuwa ne a daidai lokacin da malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunna, ya ce kwamitin zaman lafiyar da yake jagoranta ya sami nasarar kulla yarjejeniyar zaman...
A dai dai lokacinda ake yaki na kwanaki 12 tsakanin Iran da HKI da Amurka, daga ranar 13-24 na watan Yunin da ya gabata, cibiyoyin yakin yanar gizo na kasar Iran sun gwada karfinsu da kuma kwarewansu a wannan fagen fama. Kanfanin dillancin labarai na Tasnim na kuma kasar Iran ya nakalto sharhin wasu kafafen yada labarai na kasashen yamma dangane da shi. Makarantar Midle East Institute ya dubi wannan al-amarin a cikin wabi bayani da ya fitar. Inda yake cewa cibiyoyin yakin yanar gizo na Iran sun shagaltu a wannan lokacin da kare cibiyoyin kasar Iran, amma ta kuma ya aiki da kare kasar taga makiya musamman masu taimakawa HKI a wannan yakin. Kuma da hakan ta kare wurare...
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kare gaskiya, bayyana ta da kuma ɗaukar nauyin ayyukanta a bainar jama’a. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne duba da muhimmancin al’amuran da suka shafi jama’a da kuma halin da ake ciki. Ya ce: “A matsayina na ɗaya daga cikin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu matasa sun zabi tallata ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda bai kamata ba a wasu lokutan. Tallata ‘yan siyasa da matasan suke yi kan haifar da hatsaniya, ko kiyayya, a intanet ko ma a zahiri a tsakanin su. NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa suka zabi zama “sojojin baka” ko “karnukan farautar” ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta. Domin sauke shirin, latsa nan
Gwamnan ya kuma jaddada kudirinsa na ci gaba da tabbatar da adalci, ladabtarwa, da yakar laifukan da suka shafi sha da fataucin miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u da ke addabar matasa da al’umma jihar Kano. Gwamna ya kuma yi gargaɗi ga duk masu rike da mukaman siyasa da su rika yin taka-tsantsan kan al’amuran da suka shafi jama’a, tare da neman izini daga hukuma kafin su shiga irin waɗannan harkoki marasa daɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya kuma kara da cewa, a Benuwe, sama da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a gwamnatin baya. Nuhu ya bayyana cewa, ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin Arewa-maso-Yamma sun kai ga ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025. An kuma kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan bindiga da tawagarsu a jihohin Zamfara, Kaduna, da Katsina. A wajen taron, akwai manyan shugabannin Arewa da suka hada da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, tare da gwamnoni na yanzu da tsofaffi, Ministoci, Hakimai, da masu rike da mukaman siyasa. Ribadu ya kammala da jaddada kudirin gwamnati na tabbatar...
A cewar mahaifin marigayen, Dankama, ya bayyana cewa ba ya gida lokacin da katangar ta fado, inda ya ce ya kadu da jin labarin. “Wannan lamarin ya faru da kusan mutane goma, amma mutane 6 sun riga mu gidan gaskiya. A yanzu haka, uku suna kwance a asibiti suna karbar magani,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.89, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 544.9. Cikin wannan adadi, alkaluman hidimomin da aka fitar daga kasar Sin ya karu da kaso 15 bisa dari, wato darajar da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 1.69, yayin da na wadanda aka shigo da su kasar ya karu da kaso 3.2 bisa dari, daidai da kudin Sin tiriliyan 2.2. Sai kuma gibin cinikayya a fannin na bayar da hidimomi...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Haɗin kai tsakanin kafofin watsa labarai, diflomasiyya da fage na tabbatar da ƙarfi da ci gaban ƙasa A jajibirin ranar ‘yan jarida ta kasa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ziyarci hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBO) inda ya gana da shugaban kungiyar da sauran jami’an kafofin yada labarai na kasar. A yayin taron, shugaban kungiyar ta NBO, Peyman Jebli, ya yi maraba da minista Araqchi, ya kuma yaba da kokarin da hukumomin diflomasiyya ke yi wajen inganta manufofin harkokin waje da kuma kare muradun kasar. Mista Jebli ya bayyana hadin kai da hadin gwiwa tsakanin harkokin diflomasiyya da kafafen yada labarai da cewa yana da matukar muhimmanci wajen...
Sojojin Yemen sun kaddamar da hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa a haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa, domin mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba masifar yunwa da makiya yahudawan sahyoniya suka aikata a kan ‘yan’uwansu a zirin Gaza, da kuma mayar da martani kan gungun yahudawan sahayoniyya da suke kutsawa cikin masallacin Al-Aqsa tare da wulakanta farfajiyar sa mai alfarma. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa; Rundunar ta kai wani harin soji mai inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da...
Dokta Muhammad Tahir da aka yi wa barazanar kisa ya bayyana abin da ya gani na masifa a Gaza Dr. Muhammad Taher ya dauki kashe-kashe da kakaba yunwa da ke faruwa a Gaza a matsayin abin tunawa da abin da ya faru da Imam Husaini (a.s), kuma Gaza ita ce Karbala ta wannan zamani. A jajibirin taron tunawa da Arbaeen na Imam Husaini (a.s) Dr. Muhammad Taher ya halarci taron kiran Al-Aqsa karo na hudu a birnin Karbala mai tsarki. A gefen taron, Dr. Muhammad Taher ya kasance bako a cikin shirin “Tattaunawa da Baki” a tashar talabijin na Al-Alam. Dr. Muhammad Taher wani likitan fida ne dan kasar Iraqi wanda ya sadaukar da kansa wajen kula da mutanen Gaza...
An samu bullar sabani da rikici a tsakanin ‘yan sahaypniyya game da mamaye Gaza a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare da kuma rage yawan sojojinsu a yankin Yakin kisan kiyashi yana ci gaba da gudana a Gaza ta hanyar ci gaba da kai hare-hare kan mai uwa da wabi, tare da nau’o’i daban-daban na aiwatar da kashe-kashe da kuma kakaba yunwa. Duk da yadda kasashen duniya ke ci gaba da nuna bacin ransu kan irin girman kai da gwamnatin mamayar Isra’ila ke nuna wa, kafafen yada labaran haramtacciyar kasar isra’ila sun rawaito cewa: Majiyar fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ta bayyana cewa ya yanke shawarar mamaye yankin gaba daya da aka killace saboda yana...
Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko. A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na da muhimmanci matuƙa wajen tabbatar da lafiyar yara da kuma inganta cigaban su tun daga ƙuruciya. Ta kuma bayyana cewa makon yana da nufin wayar da kan jama’a musamman a tsakanin iyalai game da amfani da shayar da nono, tare da ƙarfafa gwiwar ma’aikatan lafiya da su ci gaba da fafutukar wayar da kai a fadin karamar hukumar. A nata jawabin, Sakatariyar Lafiya...
Rahotanni sun bayyana cewa, fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda Bello Turji ya mika wuya tare da sako wasu mutane 32 da aka yi garkuwa da su, biyo bayan wani shirin zaman lafiya da malaman addinin musulunci suka yi a jihar Zamfara. Wani fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah ne ya bayyana hakan yayin wani taron addini da aka yi a ranar Litinin a Kaduna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen Abuja ta sanar da cafke wasu mata ’yan gida ɗaya da ake zargi da kitsa garkuwar ƙarya da zummar karɓar kuɗin fansa na naira miliyan biyar a wurin mahaifinsu. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniya Ta bayyana cewa sun samu tushen faruwar lamarin ne bayan da wani Mista Innocent, ya kai rahoton ɓacewar ’yarsa mai shekaru 16 a ranar 18 ga Yuli, 2025. Mista Innocent ya shaida wa ’yan sandan cewa ’yar tasa ba ta dawo gida ba tun bayan da ta fita domin...

Xizang Ya Cimma Nasarorin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Suka Kafa Tarihi Cikin Shekaru Fiye Da 60
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tosin Demehin ta nuna godiya da jin daɗinta, tana mai cewa wannan girmamawa daga jiharta na ƙarfafa mata gwuiwa da sauran ’yan mata masu burin taka leda a matakin duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra’ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza. Jami’an sun ce “tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana ga Isra’ila”. “Amincin da kake da shi a wajen Isra’ilawa zai ƙara ba ka damar sanya Firaiminista [Benjamin] Netanyahu da gwamnatinsa a kan hanya daidaitacciya: A kawo ƙarshen yaƙin, a dawo da mutanen da ke tsare a kuma daina gallaza wa Falasɗinawa,” kamar yadda suka rubuta. Roƙon nasu na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa Netanyahu na ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan soji a Gaza...
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere. A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mai wakiltar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kowane dan wasa zai karbi dala 100,000, yayin da koci da kungiyar kwararru za su samu dala 50,000 kowanne, tare da karramawar kasa ga daukacin kungiyar. Ya kuma yi alkawarin karin tukuicin da zai zo. Shettima ya ce ba wai don murnar nasarar da kungiyar ta samu a cikin shekaru 78-64...
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba wa sabbin ma’aikatan aikin gona 1,038 da aka dauka aiki takardun su na kama aiki. Bikin, ya gudana ne a gidan gwamnatin Kano. Da yake jawabi yayin bikin gwamnan ya gargade su da su guji cin hanci da rashawa, ya kuma bukace su da su yi wa jihar hidima cikin himma da gaskiya. Ya ce matakin ya nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da jihar ke yi na inganta samar da abinci da kuma habaka arzikin iyali. Gwamna Yusuf ya bayyana daukar ma’aikata a matsayin cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe da kuma wani muhimmin mataki na cimma wadannan manufofin. ...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da karin kudin da gwamnatoci a matakin jiha suke samu daga asusun tarayya, ’yan Najeriya da dama suna korafin ba sa gani a kas. Manazarta dai sun ce ko kafin karin ma ya kamata ya yi a ce ayyukan da gwamnatcin jihohi suke yi sun fi da ake gani Ko mene ne ya sa jihohi “ba sa kashe karin kudaden da suke samu yadda ya kamata”? NAJERIYA A YAU: Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin ‘yan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin yahudawan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. A lokacin da yake halartar taron manema labarai da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya gudanar a yau Litinin, Araqchi ya ce: Na farko dai ya zama wajibi a gare shi ya girmama dukkanin shahidai: shahidan juyin juya halin Musulunci, shahidan tsaro mai alfarma (1980-1988), da dukkanin shahidan da suka sadaukar da rayuwarsu wajenkare kasa, tun farko-farko har zuwa yau, musamman ‘yan jaridu da shahida yakin matsorata masu wuce gona da iri na...

Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba
Shugaban Amurka ya aike da jakada zuwa Rasha tare da yin barazanar sanyawa Moscow takunkumi Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Manzonsa na musamman Steve Witkoff zai ziyarci kasar Rasha a mako mai zuwa, yayin da wa’adin da ya sanyawa Moscow na kawo karshen yakin da take yi da Ukraine ke gabatowa. A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gwabza yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, inda Moscow ta sanar da lalata jiragen Ukraine guda 18. Yakin da ake yi a Ukraine na kara kamari zuwa ci gaba mai hatsari a daidai lokacin da wa’adin da shugaban Amurka Donald Trump ya gindaya wa Rasha ke gabatowa, da kuma halayensa na tunzura jama’a,...
Rundunar sojin kasar Sin (PLA) ta yi sintiri a yankin tekun kudancin Sin daga ranar 3 zuwa 4 ga wata. Kakakin rundunar PLA ta kudancin kasar Tian Junli ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne biyo bayan matakan Philippines na sanya kasashen dake wajen yankin cikin abun da ta kira da sintirin hadin gwiwa, wanda ke neman lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin. A cewarsa, dakarun rundunar ta kudancin kasar za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana da kare ikon kasar kan yankunanta da muradunta na teku ba tare da yin kasa a gwiwa ba, yana mai cewa za a dakile duk wani matakin soja dake nemen tada hankali da rikici a...

Sojojin Somaliya Sun halaka Mayakan Kungiyar Al-Shabab Fiye Da Hamsin A Kudu Maso Yammacin Mogadishu
Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a yankin kudu maso yammacin birnin Mogadishu fadar mulkin kasar somaliya Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa; Sama da mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab 50 ne suka halaka a wani samame da dakarun sojin Somaliya suka kai a garin Bireire da ke kudu maso yammacin Mogadishu fadar mulkin kasar. Tawagar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: “A samamen hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya domin kwato garin Bireire a ranar 1 ga watan Agusta, ya haifar da hasara mai yawa ga ‘yan ta’addar, tare da kashe mayakan Al-Shabaab fiye da 50, wasu...
Bayanin da Hukumar Haraji ta Kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, a rabin farko na wannan shekara, kudaden cinikin da kamfanoni a duk fadin kasar suke samu ya ci gaba da karuwa cikin kwanciyar hankali. Masana’antu sun sami ingantaccen ci gaba yayin da manufofin “sabunta manyan kayan aiki na kasa” da “Maye gurbin kayan amfani da suka tsufa da sababbi” suka yi tasiri sosai. Kudin da aka samu a bangaren sana’ar kere-kere ya karu da sauri fiye da matsakaicin karuwar dukkan kamfanoni da kashi 1.5%. Wannan ya tabbatar da cewa masana’antu su ne tushen karfafa tattalin arzikin kasar. Kazalika, masana’antun kirkire-kirkire sun kara habaka, inda kudaden da aka samu a bangaren sayar da kayayyaki na masana’antun kimiyya mai inganci ya...

Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15
Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya bayar da muhimmin umarni game da binciken ra’ayoyin jama’a masu amfani da shafukan Intanet kan aikin tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 a kwanan nan, inda ya ce, ya kamata aikin tattara ra’ayoyin jama’a ta yanar gizo wajen tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15 ya samu shigar jama’a sosai, kuma ya kasance wani aiki na dimokuradiyya dake shafar dukkan bangarori. Jama’a sun yi ta ba da shawarwari tare da gabatar da ra’ayoyi masu muhimmanci, wadanda ya kamata sassan da abin ya shafa su yi nazari a hankali tare da shigar da su cikin tsarin. Kuma dole ne...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe. Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa gwamnatin na nan tana duk abin da za ta iya yi don kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin. Lokacin da ya ke mayar da jawabi, shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, Manir Haidara ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin ta samar da tsaro a duk faɗin jihar Zamfara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati. Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin. Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko. Ta kara...
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a majalisar masarautar Gudi. Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule Wasu Kungiyoyi Sun Yi Kira Ga Dan Majalisa Aminu Sani Jaji Ya Fito Takarar Gwamnan Zamfara Kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya da fasaha na jihar, Farfesa Muhammad Bello Kawuwa ne ya mika takardar nadin ga sabon sarkin a madadin gwamnan. Da yake isar da sakon Gwamnan, Farfesa Kawuwa ya bayyana muhimmiyar...
Gwamnan ya bukaci kamfanin da ke aikin da ya bi ka’idoji da tsarin tsaro, tare da roƙon al’ummomin da abin ya shafa da su ba da haɗin kai ga masu aikin da kuma kare rayuka da kayan aiki. “Wannan aiki wani ɓangare ne na kudirin Gwamnatin Jihar wajen samar da ci gaban ababen more rayuwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da ganin cigaba ya kai kowane yanki,” in ji Gwamna. Da yake kaddamar da aikin, Gwamna Sule ya sake jaddada kudirin Gwamnatinsa na kada a bar ko wata al’umma a baya wajen kawo ci gaba, domin samar da jihar Nasarawa da tabbatar da lafiya da haɗin kan ‘yan jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Wukari/Ibi ta jihar Taraba a majalisar wakilai, Hon. Shiddi Danjuma Usman ya fice daga jam’iyyar APC. Usman ya bayyana rikicin cikin gida na jam’iyyar da rashin bin ka’idojin dimokuradiyya a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar. ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi Shiddi, wanda ya wakilci mazabarsa a majalisar wakilai ta 8 da ta 9, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai a ranar Lahadi. Tsohon dan majalisar ya ce, matakin da ya dauka na ficewa daga jam’iyya mai mulki ya biyo bayan tunani na tsawon watanni da kuma...
Wakilin hukumar abinci na noma ta duniya FAO, Farrukh Toirov, ya bayyana cewa sauyin yanayi ya shafi dukkan kasashen yankin Asiya da kudu, don haka yana daga cikin ayyukansu su samar da sabbin dabarbanun ayyukan noma tare da kasar Iran. Sannan JMI a matsayin kasa wacce take tsakiyar kasashen yankin tana iya aika da wadan nan dabarbaru ga sauran kasashen yankin. Kamfanin dillancin labaran Iran Press ko IP na kasar Iran ya nakalto Farrukh Toirov yana fadar haka, a dai-dai lokacinda ya mika takardun kama aiki a nan Tehran, daga babban cibiyarsu a MDD. Sabon wakili FAO a Iran ya kammala da cewa hukumarsa zata yi aiki tare da makarantu da cibiyoyin ayyukan noma don aiki tare da kuma samun...