2025-08-14@12:00:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3191
«Ya ku mutane»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
’Yan bindiga sun tarwatsa kauyaku sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina. Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono. Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su. Hakan dai ya haifar da kauracewa ƙauyukan ga mazaunansu da...
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da shirin a hukumance da aka gudanar a cibiyar lafiya matakin farko na Birji da ke karamar hukumar Madobi. Ya yi nuni da cewa, wannan aikin ya hada da na rigakafi na yau da kullun ga yara, karin sinadarin Vitamin A, Rarraba gidajen sauro masu maganin kwari ga mata masu juna biyu. Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa...
Rundunar sojin ba ta fitar da sanarwa ba game da wannan hari na baya-bayan nan, amma hukumar DSS ta tabbatar da faruwar lamarin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar New York ya jaddada alƙawarin kasa da kasa na kawo ƙarshen yaƙin a Gaza da aiwatar da hanyoyin samar da ƙasashe biyu Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a cikin “Sanarwar New York” da yarjejeniyar kasa da kasa kan matakan dole da suka dace don kawo karshen yakin Gaza da aiwatar da Shirin samar da kasashe biyu da zai kai ga kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci, da sake gina Gaza, da tura tawagar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya. Sanarwar karshe da taron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar kan sasanta rikicin Falasdinu cikin lumana ya sanar da amincewar kasashen duniya kan daukar matakai na bai daya don kawo karshen hare-haren wuce gona...

Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba
Fira ministan Birtaniya ya bayyana cewa: Za su amince da kasar Falasdinu a watan Satumba idan yanayin Gaza bai canza ba Keir Starmer ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare tsarin kasashe biyu, kuma kasarsa na da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyanta wajen ganin an samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu. Ya ce tallafin da kasarsa ke baiwa Tel Aviv yana nan daram. Fira ministan na Burtaniya ya jaddada cewa kin amincewar da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi na samar da kasashe biyu kuskure ne kuma kuskure ne na dabi’a da dabaru. Ya jaddada cewa dole ne a bude mashigar kasa sannan kuma a bar manyan motocin...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta bayyana cewa: Laifukan da aka aikata a Yammacin Kogin Jordan na Falasdinu ayyukan ta’addanci ne Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da cewa tashe-tashen hankula da laifuffukan da tsagerun yahudawan sahayoniyya suke yi a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye sun zama ayyukan ta’addanci, biyo bayan kashe wani mai fafutukar yaki da mamayar da tsagerun ‘yan sahayoniyya suka yi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya ce: “Faransa ta yi Allah-wadai da wannan kisan gilla da kakkausar murya, da kuma dukkan ayyukan ta’addanci da gangan da masu tsattsauran ra’ayi ke yi kan Falasdinawa, wanda ke karuwa a ko’ina cikin yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan.” Ya kara da cewa, wadannan ayyukan wuce gona da irin, hakikanin ayyukan...
Har ila yau, Ribadu ya ce yanzu mutane suna iya zuwa gonakinsu a wuraren da a baya ba a iya shiga saboda barazanar ‘yan bindiga. Sai dai duk da wannan ikirari, har yanzu wasu yankunan kamar Zamfara, Benuwe da Filato na fama da hare-haren ‘an bindiga da rikicin ƙabilanci. A ƙarshen makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun kashe mutane a Kauran Namoda a Jihar Zamfara. Sannan ƙungiyar Boko Haram har yanzu na ci gaba da zama barazana a Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar hukumar Hisbah da inganta aikinta. A cewar sa, naɗin ya haɗa da Dr. Husaini Yusuf Baban a matsayin Babban Mataimakin Kwamanda Janar, da Lawan Danbala a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar da hedikwatar hukumar, da kuma Yunusa Idris Barau a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar naYankin Dutse. Sauran su ne Abdulkadir Zakar, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Hadejia, da Suraja Adamu, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Gumel, da...

Kwamitin Neman Sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba Ya Gabatar Da Takardar Bukatarsa Ga Majalisar Dattawa
Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba, Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim ya bayyana cewar wannan yunkuri ya bi duk sharuddan da kundin tsarin mulki ya shimfida don kafa sabuwar karamar hukuma. Makaman na Ringim ya kara da cewar, daukacin al’ummar yankin Kanya Babba, ciki da wajen mazabar na matukar goyon bayan hakan domin bunkasa ci gaban tattalin arziki da al’umma a yankin. Da yake karbar takardar, Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril,...
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya kammala rahoton aikinsa na wucin gadi. Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin da ke Karaye. Ya ce rahoton ya ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi aikin Hajji tun daga lokacin da aka ƙaddamar da kwamitin a birnin Makkah, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf. “Rahoton ya kunshi cikakken bayani kan ayyukan da kwamitin ya gudanar zuwa yanzu, kuma zai kasance muhimmin ɓangare na rahoton ƙarshe da za a miƙa ga Gwamna,” In ji shi. Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau Talata, kwamitin kwaskwarima da raya kasar Sin, ya fitar da kudin Sin RMB yuan miliyan 200, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 28, domin tallafawa wajen farfado da sassan birnin Beijing da bala’in ambaliyar ruwa ya shafa, musamman ma fannin sake gina ababen more rayuwar jama’a na sufuri, da samar da ruwan sha, da kiwon lafiya, da na hidimomin al’umma a gundumomin Miyun da Huairou, a kokarin ganin rayuwa ta dawo kamar yadda take a wuraren, an kuma dawo da ayyuka kamar yadda aka saba. Ban da haka kuma, ma’aikatar kudi, da ma’aikatar lura da ayyukan gaggawa ta kasar sun zuba kudin Sin yuan miliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 49 don tallafawa biranen Beijing, da Tianjin, da lardunan Hebei, da...
Rundunar Ƴansandan jihar ba ta fitar da bayani kai tsaye ba, amma wani babban jami’i da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da kama wanda ake zargi, tare da ce wa an tafi da shi zuwa Lokoja domin cigaba da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta bayyanawa duniya karfinta da jajircewar a ga duniya. Da kuma tabbatan JM tayi a kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron cika kwanaki 40 da shahadar wadanda suka yi shahada a yankin. Labarin ya kara da cewa mafi yawan wadanda suka halarci tarun iyalan shahidan yakin kwanaki 12 ne da jami’an gwamnati da kuma manya-manyan sojojin kasar da sauran Jama’a. Jagoran ya kara da cewa, HKI da Amurka basu fadawa JMI da yaki don shirin ta makamashin Nukliya ko don take hakkin...
Likitoci a jihar Lagos na tarayyar Najeriya sun fara yajin aiki na gargadi na kuma kwanaki 3 saboda nuna rashin amincewasu da rage hakkokinsu da kuma hanasu kudadensu wanda gwamnatin jihar take yi. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa duk tare da kokarin da ma’aikatar kiwon lafiya ta yi don kada likitocin su shiga yajin aiki amma a safiyar jiya litinin likitocin sun dakatar da ayyuka a dukkan asbitocin gwamnatin Jihar. A bangaren kasha na jami’ar koyon aikin likita na Jami’ar Lagos marasa lafiya da dama sun fito don ganin likotocinsu amma sai aka fada masu duk sun shiga ya jin aiki. Wanta marasa lafiya wacce taki fadar sunanta ta fadawa Premium times kan cewa ta zo ganin...

Xi Ya Yi Kira Da A Yi Azamar Kare Rayukan Al’umma Yayin Da Ake Fuskantar Ibtila’in Ambaliya A Wasu Sassan Kasar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin. Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen. Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa. Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama. Dr Shuaibu ya bayyana cewa,...
Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu. Daga bisani ’yan sanda sun sun bi su, inda suka fatattake su suka gudu zuwa cikin kungurmin Dajin Madam. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ne ya sanar da mutuwar mutanen a yayin taron zaman lafiya da aka gudanar a garin Nahutan Darazo a kokarinsa na sasanta rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya da ya yi sanadin jikkatar wassu mutane a Darazo. Gwamnan ya kuma nuna matuqar damuwarsa kan...

Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci. Haka nan kuma ya ce; Daga...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau kuma Sarkin Katsina na Masarautar Gusau. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarwarin da masu zaɓen sarakuna na masarautar Gusau suka bayar, tare da bin al’ada da dokokin da suka dace. A wata sanarwa da mai taimakawa na musamman kan harkokin yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, ya ce sabon Sarkin, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, shi ne ɗa na farko ga marigayi Sarki, kuma kafin naɗin nasa yana riƙe da mukamin Bunun Gusau. Alhaji Abdulkadir ya hau karagar...
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta samu nasarar kama mutane 15 da ake zargi da laifuka daban-daban, ciki har da wani kasurgumin dan fashi da makami mai suna Mu’azu Barga, a wani samame da aka lakaba wa suna “Operation Kukan Kura”. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano. Ya ce samamen, wanda dakaru na musamman suka gudanar a unguwannin Sheka, Ja’oji, da Kurna a ranar 26 ga Yulin 2025, na da nufin gano da kuma hana aikata laifuka, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun. Kiyawa ya bayyana cewa, wadanda aka kama ‘yan tsakanin shekaru 14 ne zuwa 28, kuma an...
Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari. Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sai dai ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi ya tsaya takara a 2023, amma yanzu lokaci ya yi ne da zai yi gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya. Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta...

Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba. Basil Khairudden wakilin gidan talabijin na Al-Alam a Gaza, ya ce: “A ranar Juma’a, shi da iyalinsa da daukacin al’ummar Gaza ba su iya samun ko da biredi guda da za su ci ba, sakamakon yunwa da ake fama da ita a Gaza.” Ya tabbatar da cewa a Gaza akwai mutanen da ba su ci abinci ko da sau daya a tsawon kwanaki uku. A ranar...
Amma yanzu, babu matsalar gaba ɗaya a ƙananan hukumomi 11, yayin da aka samu sauƙi a wasu tara. Ya ce har yanzu ana fama da hare-hare a ƙananan hukumomi huɗu: Faskari, Ƙankara, Safana da Matazu. Kwamishinan ya jaddada cewa jami’an tsaro suna iyakar ƙoƙarinsu, kuma gwamna yana ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar. Ya buƙaci al’umma da su daina suka, su kuma tallafa wa jami’an tsaro da addu’a da fahimta, ganin irin sadaukarwar da suke yi domin kare rayukan jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar. Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma, a cewar ma’aikatar tsaron jihar. Kwamishinan tsaron jihar, Nasir Mua’zu ya sanar da haka ne a martaninsa kan wasu rahotanni da ke yawo a kafofin sada zumunta, waɗanda ya ce ana amfani da su domin tayar da hankalin jama’a. Mu’azu ya ce Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa yana yin iya bakin koƙarinsa wajen shawo kan matsalar ’yan ta’adda kuma ana samun nasara a kansu. Kwamishinan...
Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu. Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare da fahimtar ainihin abin da ke faruwa ba, inda ya ce hakan yana da nasaba da tuggun siyasa da son zuciya. Ya bayyana cewa maƙasudin ambaliyar sun haɗa da ruwan sama mai yawa da toshewar hanyoyin ruwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya shirya taron manema labaru na yau da kullum. A wajen taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da aka kulla tsakanin Amurka da kungiyar EU. A yayin da yake ba da amsa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin a ko da yaushe tana ba da shawarar cewa, ya kamata dukkan bangarori su warware bambance-bambancen tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tattaunawa, domin kiyaye yanayin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. Bugu da kari, dangane da taron tattauna batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a kasar Sweden, Guo Jiakun ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka...
Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu. Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC. Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda tauye musu ‘yancin su. Kotun ta kuma bayyana cewa cin zarafi da muzantawar da suka fuskanta daga hannun jami’an NYSC ya ci karo da ‘yancinsu na yin addini da bayyana shi a aikace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Shugaban kungiyar Hamass ya bayyana cewa HKI da gwamnatin kasar Amurka sun janye daga tattaunawa tsakaninsu da kungiyar ne don sake komawa yaki har zuwa lokacinda zasu shafe falasdinawa a gaza. Tashar talabijin nta Presstv a nan Tehran ya nakalto Kkalilul Hayya, yana fadar haka a wani jawabin da aka watsa a tashoshin talabijin nay au Litinin. Alhayya ya bayyana cewa akwai ci gaba a tattaunawar tsagaiuta wuta tsakanin kungiyar da HKI da kuma Amurka, amma janyewar HKI da kuma Amurka a wannan tattaunawar wata dasisa ce don ci gaba da kissan kiyashi a gaza. Ya ce: masu shiga tsakanin sun tabbatar da cewa akwai ci gaba a tattaunawar da ake yi a doha, sai dai sun janye ne don...
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki. Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar masar kan cewa masar bazata taba kyale mutanen Gaza a halin da suke ciki ba har abada. Ya ce: Gwamnatin kasar Masar tana daga cikin kasashen da suka tsaya don ganin an kawo karshen wannan yakin, tare da Amurkan da kuma kasar Qatar don tabbatar da cewa an kawo karshen yakin . Shugaban daga karshe ya gabatar da shawarar samar da kasashe biyu a matsayin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569. Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya bayyana tsarin fansho na jihar a matsayin daya daga cikin mafi nagarta a kasar nan. A cewarsa, fiye da jihohi ashirin sun kai ziyara jihar Jigawa domin koyon yadda take tafiyar da shirin fansho. Ya jinjina wa Gwamna Umar Namadi saboda dagewarsa da kuma jajircewarsa wajen dorewa da inganta tsarin fansho a jihar. Alhaji Dagaceri ya yabawa Gwamna Namadi kan...
A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin gudanar da bincike mai zurfi. Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya kaddamar da kwamitin a madadin gwamnan. An umurci kwamitin da ya gudanar da binciken cikin mako guda, domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma ba da shawarwari kan matakin da ya dace a dauka. Shugaban kwamitin shi ne Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Dokoki,...
Ministan Harkokin Tsaron Ƙasa, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya baiwa iyalan marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, gudummawar naira miliyan biyar da kuma kayan abinci, bayan rasuwarsa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja sakamakon gajeruwar rashin lafiya. Dakta Matawalle, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi na Mai Martaba. Baya ga gudummawar kuɗi, ministan ya kuma bada buhunan shinkafa 20, gero 10, masara 10 da kuma dawa 10 ga iyalan mamacin. Wata tawaga mai ƙarƙashin jagorancin Sanata Hassan Muhammad Nasiha, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara a zamanin mulkin Matawalle ne suka miƙa gudummawar a madadin ministan. Dakta Matawalle ya bayyana marigayi Sarkin Gusau a matsayin shugaba mai ɗabi’a ta gari, wanda ya kasance...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce rasuwar Dakta Usigbe babban rashi ne ba kawai ga kamfanin jaridar Tribune da fagen aikin jarida ba, har ma da ƙasar nan baki ɗaya. “Nijeriya ta yi rashi matuƙa — mun rasa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan jarida, wanda ilimin sa, jarumtar sa, da himmar sa ta sa kowa yana girmama shi.” A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga shugabanni da ma’aikatan Tribune, da gwamnati da al’ummar Jihar Edo inda marigayin ya fito, da kuma iyalan sa, da abokan sa, da ma dukkan masu mu’amala da shi. “Allah ya jiƙan sa, ya ba duka waɗanda ya bari haƙurin jure wannan babban rashi,” inji Ministan. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Kasar Amurka ta sanar da dakatar da bai wa mutanen Nijar bisa ta shiga cikin kasarta har illa masha Allahu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da cewa an dakatar da bayar da bisa din ga ‘yan kasar Nijar da suke son shiga cikin kasar, saboda abinda ya kira matsala da ake da ita da gwamnatin Nijar, ba tare da yin Karin bayani ba. Sai dai kuma sanarwar ta yi togiya akan jami’an diflomasiyya da sauran jami’an gwamanti,kamar yadda wani sako na diplomasiyya ya nuna a ranar 25 ga watan Yuli. Wannan matakin na Amurka ya biyo byan rashin jituwar da ake da shi a tsakanin gwamatin Amurka da gwamnatin Jamhuriyar Nijar. A watan Satumba...
A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun da safiyar yau domin daukar jana’izarsa zuwa garin Bakfaya. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Rahbani ya rasu yana dan shekaru 69 bayan da ya yi gajeruwar rashin lafiya. A lokacin rayuwarsa ya shahara da wakoki na gwgawarmaya da kishin kasa, daga cikin da akwai wakar da ya yi wa Shahid Sayyid Hassan Nasarallah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara da cewa; Wannan mataki na diflomasiyya ya karfafa kimar Iran a duniya, bayan da ta samu goyon bayan kasashe fiye da 120 wadanda suka yi Allah wadai da cin zarafin da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran a baya-bayan nan. Hakan dai ya zo ne a yayin wata ganawa da aka yi da Araghchi, inda ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliyar...

Babban Jami’in Hamas A Gaza; Makiya ‘Yan Sahayoniyya Suna Rufe Gazawar Sojojinsu Da Kisan Kare Dangi
Babban jami’in kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya bayyana cewa: Makiya yahudawan sahayoniya suna rufe gazawar sojojinsu da kisan kare dangi Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula. A cikin wani jawabi kai tsaye ta gidan talabijin, Al-Hayya ya bayyana cewa: “Ya ku ‘ya’yan Dakarun Qassam, da na Quds Brigade, da kuma sauran kungiyoyin gwagwarmaya, abin da kuke yi ya kawo cikas ga farmakin da motoci masu sulke na makiya suke yi. Khalil ya jaddada cewa: Babban hafsan hafsoshin sojin makiya yana rufe gazawar sojojinsa da kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen...
Fiye da mutane 21 ne suka mutu a wani harin ta’addanci da aka kai kan wani coci a gabashin Kongo Rahotonni sun tabbatar da cewa; Sama da mutane 21 ne aka kashe a wani hari da mayakan ‘yan tawayen kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) suka kai kan wani cocin Katolika da ke gabashin Kongo, wanda ya hada da kona gidaje da shaguna a yankin. A ranar Lahadin da ta gabata ne mayakan da suke da alaka da kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) da ke samun goyon bayan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS suka kaddamar da harin ta’addanci kan wata majami’ar Katolika a gabashin Kongo. “Sama da mutane 21 ne aka kashe a ciki da wajen cocin,” Dieudonné Duranthabo, wani jami’in...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a matsayin dalilansu na rashin kaɗa ƙuri’a. Ko waɗanne matakai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) take ɗauka don ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwan fitowa su kada ƙuri’a a zaɓen 2027? NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa nasarar ayyukan tsaro a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aisha ta koma gidan mijinta, marigayi Muhammadu Buhari da ke Jihar Kaduna, bayan shafe kwanaki a Daura tana karɓar gaisuwa. Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ce ta jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen tarbar Aisha a Filin Jirgin Sama na Kaduna a ranar Lahadi. Tsohon shugaban jami’ar Kashere ya rasu a Abuja Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP Daga cikin waɗanda suka tarbe ta akwai Shugabar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Munira Suleiman Tanimu, da wasu manyan jami’an gwamnati. Tarbar da aka yi mata ta nuna yadda jihar ke ci gaba da girmama tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da iyalinsa bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban ƙasar nan. Bayan tarbar ta,...
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, Zhao Leji, ya kai ziyarar sada zumunta a kasar Kyrgyzstan daga ranar 23 zuwa 24 ga wata, inda ya gana da shugaban kasar Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov a birnin Bishkek. Yayin ganawarsa da Japarov, Zhao Leji ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen tsakiyar Asiya ciki har da Kyrgyzstan, don inganta gina al’umma mai makoma bai daya tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya. Japarov ya bayyana cewa, layin dogo tsakanin Sin da Kyrgyzstan da Uzbekistan, ba wai wata muhimmiyar hanyar sufuri ce kadai ba, har ma wata “hanyar abokantaka” ce dake sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin yankin.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Domin neman mafita da samar da zaman lafiya mai ɗaurewa, gwamnan ya kafa kwamiti na musamman da zai hhaɗa ukkanin bɓangarorin da abin ya shafa da jami’an gwamnati domin daddale asalin filayen da aka ware domin noma da ware iyakokin noma da kuma na kiwo domin tabbatar da adalci da gaskiya a tsakanin kowane ɓangare. Gwamnan ya jaddada cewa dukkanin ɓangarorin biyu na manoma da makiyaya kowa na da rawar da yake takawa wajen ci gaban tattalin arziki, don haka ya nemi a mutunta juna a zauna lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan cewa sun tsaida yaki na wucin gadi a gaza, don baya kungiyoyin agaji na MDD su shigar da abinci zuwa zirin gaza inda Falasdinawa suke mutuwa saboda yunwa. Babu wata majiya ta MDD ko kuma na kungiyoyin agaji masu zaman kansu da suka tabbatar da labarin. Kuma mafi yawan kungiyayin sun bayyana cewa sai gani a kasa. Don hki ba abar amincewa bace. Tun shekara ta 2023 ne HKI ta kara tsananta hana shigo da abinci gaza.
Allah Ya yi wa tsohon shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe, Farfesa Alhassan Gani, rasuwa a safiyar Lahadi a wani asibiti da ke Abuja. Ya rasu yana da shekaru 66 a duniya. Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo Kafin rasuwarsa, Farfesa Gani yana koyarwa a Sashen Kimiyyar Halittu na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Farfesa Gani, ya yi fice wajen sadaukar da kansa wajen ci gaban ilimi, musamman lokacin da yake jagorantar Jami’ar Kashere. Gwamna Inuwa Yahaya ya aike da saƙon ta’aziyyarsa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana rasuwar Farfesan a matsayin babban rashi ga harkar ilimi da...
Bisa alkaluman da aka fitar a dandalin shafin intanet, ya zuwa ranar 27 ga watan, jimillar kudin shigar da kasuwar fina-finai ta Sin ta samu a lokacin zafi na bana ya zarce yuan biliyan 5, kuma adadin masu kallon fina-finai a lokacin ya kai miliyan 129. Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yaki da hare-haren sojojin Japan da kuma yaki da mulkin danniya a duniya ko kuma yakin duniya na biyu. Daya-bayan-daya zuwa yanzu, ana ci gaba da fitar da wasu fina-finai, da shirye-shirye, da wasannim kwaikwayo, da kide-kide, da raye-raye da kuma ayyukan fasaha dake da jigon tunawa da tarihin yaki da hare-haren na Japan da kuma gadon ruhin yaki da hare-haren. Daga cikinsu, za a fitar...
Ma’aikatar sharia a nan Tehran ta bada sanarwan yake hukuncin kisa kan mutane biyu mambobi a kungiyar yan ta’adda ta MKO ko wadanda aka fi sani da munafukai. Kamfanin dillancin larabann Tasnim na JMI ya nakalto majiyar ma’aikatar na cewa mutanen biyu Mahdi Hassani da Behrouz Ehsani, sun yi amfani da makamai wadanda suka hada da gurneti da kuma wasu ind suka kashe mutane fararin hula a dai dai lokacinda ake hargitsi a cikin kasar don tada hankalin mutane da kuma wargaza harkokin tsaro a cikin kasar. Labarin ya kara da cewa an tabbatar da tare da wata shakka ba suna aiki tare da kungiyar ta MKO wadanda suke adawa da JMI tun ranar kafa ta. Kungiyar MKO dai it...
An fitar da wani sabon tsarin aiki na Shanghai na gina wani yanki da zai zamo kan gaba a fagen tafiyar da motoci masu tuka kansu jiya Asabar, yayin da ake ci gaba da gudanar da taron fasahar kirkirarriyar basira na duniya a birnin dake kudancin kasar Sin. An tsara shirin ne da nufin ganin motoci masu tuka kansu a mataki na 4 sun yi jigilar fasinjoji fiye da miliyan shida nan da shekarar 2027, tare da bude hanyoyi sama da kilomita 5,000 domin motocin masu tuka kansu, tare da tabbatar da cewa an sanya wa fiye da kashi 90 cikin dari na sabbin motocin birnin na’urorin tuka kai na mataki na 2 da kuma mataki na 3. An rarraba...
Babban sufeton ƴansanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya sake tabbatar da ƙoƙarin rundunar wajen tabbatar da cikakken tsaro a faɗin ƙasar nan ta hanyar samun bayanan sirri daga jami’ansu. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan ya ce rundunar ta duƙufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan, sannan ya buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri da goyon baya domin samar da tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da marecen jiya Asabar ne dai sojojin HKI su ka kutsa cikin jirgin ruwan da yake dauke da masu fafutuka da su ka fito daga kasashe mabanbanta, wadanda suke son zuwa bagar ruwan Gaza domin kawo karshen killace yanki da aka yi tun 2006 da kuma kisan kiyashin da HKI take yi musu. Kananan jiragen ruwa na sojojin HKI ne su ka nufi jirgin ruwan mai suna; “Hanzalah” sannan su ka kutsa cikinsa. Bayan shigar sojojin cikin jirgin ruwan sun hau cikinsa sannan su ka fara dukan mutanen da suke cikinsa. MAsu kula da jirgin na Hanzalah sun bayyana cewa; Sojojin HKI sun kame mutanen da suke cikin jirgi tare da yin awon gaba da su, zuwa wani wuri. Dama...
Da safiyar Yau Lahadi Adadin sojojin mamaya na HKI da aka kashe a yankin Khan-Yunus sun kai 3. Jaridar Yediot Ahranot ta ‘yan sahayoniya ta buga labarin cewa; An kuma kashe waji jami’in soja na rundunar Gulani ta hanyar fashewar nakiya da aka dasa akan hanyar motarsa a jiya Asabar a Kudancin Gaza. Har ila yau jaridar ta ce, an kuma jikkata wani jami’in sojan mamayar bayan da nakiya ta daki wata motar jigilar sojoji. A nata gefen, rundunar Kassam ta kungiyar Hamas ta sanar da kai wa motar daukar sojojin HKI hari ta hanyar nakiyar da ta dasa a gidan gaban motar. Bugu da kari dakarun na Kassam sun sanar da kai wani harin akan motar soja ta 3...
Shugaban kasar Iran ya yi kiran cewa: Ina masu fafutukar kare hakkin bil’adama suke a bala’in Gaza? Shugaban kasar Iran Dr. Masoud Pezeshkian ya jaddada muhimmancin sauya salon tafiyar da gwamnati da kuma karfafa alaka da kasashen da ke makwabtaka da ita, yana mai cewa masu takama da kare hakkin bil’adama suna nuna fuska biyu a aikinsu, inda suka yi shiru kan munanan laifukan da ake yi wa al’ummar Gaza. A safiyar yau ne shugaba Pezeshkian ya isa ma’aikatar harkokin wajen kasar, inda ya gana da mataimakan ministoci da daraktocin ma’aikatar. A lokacin da yake jawabi a taron, shugaban ya ce, “Tun da yake dan majalisar shawarar Musulunci bai canza ba, har yanzu shi mutum daya ne, dole ne al’umma...
Yadda za a hada: Da farko za ki wanke Acca sai ki fid da kasar sai ki ajiye waje guda, Sannan ki sanya mai a tukunya idan ya yi zafi sai ki sa albasa wadda dama kin gyara ta kin yanka ta sai ki zuba ki soya ta sama-sama ta dan yi ja, sannan ki kawo kayan miyanki wanda dama kin gyara su kin jajjaga su ki zuba ki soya, sannan ki zuba magi, gishiri, kori, tayim sai ki zuba ruwa daidai yadda kika san zai dafa miki ya dahu sannan ki zuba nama sai ki rufe ki bar shi naman ya dahu. Sannan ki zuba Acca sai ki gauraya ta ki bar ta ki rufe ta na dan mintoci...
Sojojin mamayar Isra’ila sun yi furuci da halakar daya daga cikin sojojinsu sakamakon raunukan da ya samu a Zirin Gaza Majiyar sojojin mamayar Isra’ila ta tabbatar a ranar Asabar din da ta gabata cewa: Wani soja ya mutu sakamakon raunukan da ya samu kwanakin baya -bayan nan sakamakon tashin bam a kan hanyar wata motar soji a zirin Gaza. Tun da farko, sojojin mamayar Isra’ila sun amince da mutuwar Sajan Reserve Vladimir Loza, mai shekaru 36, daga matsugunin Ashkelon. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan gwagwarmayar Falastinawa ke ci gaba da kai hare-hare da kuma kwantan bauna kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a fagage da dama a zirin Gaza, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da...
Shugaban kasar Amurka ya shiga sahun masu mafarkin zasu rusa kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da ke Falasdinu Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar kawar da kungiyar Hamas idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba, yana mai zargin kungiyar da rashin son cimma matsaya. A halin da ake ciki kuma, fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa; Yana nazarin hanyoyin da Amurka za ta bi domin kwato fursunonin yahudawan sahayoniyya daga Gaza. Da alama mai shiga tsakani na Amurka ya yanke shawarar jagorantar kai farmakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke kaiwa Gaza, inda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta kawar da kungiyar Hamas. Ya yi ikirarin cewa: Kungiyar...
Masu karatu za su so jin dan takaitaccen tarihinki? An haife ni a garin Gombe, amma sai daga bisani na bar garin Gomben da zama na dawo Kano, tun ina ‘yar shekara biyar da haihuwa, sakamakon mahaifina yana aiki a Kanon. Kazalika, na girma a gaban iyayena, na yi firamare da sakandare duk a garin Kano, sannan kuma ban taba yin aure ba; budurwa ce ni. Wace irin rawa kike takawa a cikin masana’antar shirya finafinai ta Kannywood? Ina fitowa ne a matsayin Jaruma kawai, amma kuma ina da niyyar zama mai bayar da umarni a nan gaba kadan insha Allah. Me ya ja hankalinki, har kika tsunduma harkar fim? Wato batu na gaskiya, fim yana burge ni...

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya
A baya-bayan nan Robert Tarjan, Ba’amurke masanin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa, wanda ya taba lashe lambar yabo ta “Turing”, ya ce Sin ta kafa tsarin bunkasa ilimin kimiyya a matakin farko, a matsayin dabara ta tsawon lokaci da kasar ke baiwa fifiko, kuma hakan abu ne mai matukar ban sha’awa. Kazalika, a halin yanzu, Sin ta cimma manyan nasarori, yayin da a gaba kuma, ake sa ran ganin karin ci gaba da kasar za ta cimma. Tarjan wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kafar CMG ta Sin, ya ce a matakan ingiza ci gaban basirar AI, Sin na da manyan damammakin takara, wadanda suka hada da dagewa wajen cimma burika na tsawon lokaci, da tsarin bayar da ilimin...
Duba da tsadar kayayyakin noma da ke kara ta’azzara a fadin kasar nan, da kuma janye hannun manoma da dama daga noman shinkafa da masara sakamakon tsadar taki,Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kaddamar da rangwamin kashi 45 zuwa 50 cikin 100 na farashin buhun taki, tare da tura manyan motocin daukar kaya domin rarraba takin a kananan hukumomi 27 na jihar. Rediyon Nigeria ya ruwaito cewa, karamar hukumar Kirikasamma ta karbi buhuna 1,200 da za a sayar wa manoma a farashi mai rangwame. Shugaban sashen aikin gona da albarkatun kasa na karamar hukumar, Alhaji Sabi’u Kani, ya bayyana cewa za a sayar da buhun takin NPK na kamfanin Solar Brand a kan 28,800. Yayin kaddamar da fara sayar...
A karon farko, filin baje hajoji masu nasaba da taron ya kai sama da sakwaya mita 70,000, kana adadin kamfanoni mahalarta taron sun haura 800, yayin da aka gabatar da kayayyaki sama da 3,000, wadanda suka hada da manyan na’urori da masu amfani da fasahar AI, da mutum-mutumin inji. Kana an gabatar da sabbin kayayyaki sama da 100 da aka gabatar da su a karon farko. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jiya Juma’a an kammala zagayen karshe na gasar kirkire-kirkire, ta daliban kasa da kasa ta kasar Sin ta yankin Afirka a birnin Nairobin kasar Kenya, wadda jami’ar koyon ilmin aikin gona ta Nanjing ta kasar Sin ta karbi bakuncin shiryawa. Wannan shi ne karon farko da aka gudanar da gasar a nahiyar Afirka. Rahotanni na cewa, an gudanar da gasar ne a tsawon kwanaki biyu, kuma dalibai 559 daga jami’o’in Afirka 115 sun yi rajitar halartar gasar, kana an baje kayayyakin shiga gasar har 185, wadanda suke shafar fasahohin aikin noma da abinci, da amfani da basirar AI, da kiyaye muhalli, da samun ci gaba mai dorewa da sauransu. A karshe, alkalan gasar sun tattauna, tare da tsai da kudurin...
Sanata Dickson ya ƙara da cewa duk da wasu jami’an gwamnati ba su bi umarnin shugaban ƙasa ba, amma shi ya lashe zaɓen, kuma ya gode wa Buhari. Hakazalika, ya ce bayan ya kammala wa’adinsa a 2020, a lokacin da APC ke shirin karɓar mulki a Bayelsa, kotun ƙoli ta yanke hukunci cewa ɗan takararsu bai cancanta ba, amma Buhari bai matsa lamba kan kotun ta sauya hukuncin ba. “A lokacin mutane sun shirya rantsar da ɗan takarar APC a Bayelsa, amma cikin ƙasa da awa guda, kotun ƙoli ta soke nasararsa. Duk da haka Buhari ya karɓi hukuncin,” in ji shi. Ya ce Buhari shugaba ne na gari, wanda duk da bambancin siyasa da ra’ayi, bai taɓa nuna bambanci...
Wasu yan bindiga wadanda ake dangantasu da kungiyar Jaishul-Zulum sun dauki alhakin kai hare-hare a cikin wata kotu a birnin Zahidan babban birnin lardin Sistab Baluchistan a yau Asabar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yan ta’addan sun shigo da motarsu har zuwa a wata kotu a garin da Zahidan, sannan suka sauka suna son shiga kotun amma jami’an tsaro a kotun suka hanasu shiga. Daga nan kawai suka fara jefa nakiya irin da yaki a kansu. An yi ta musayar wuta tsakaninsu da jami’an tsaro zuwa wani lokacin suka sami nasarar halakasu. Amma kuma sun kai mutane 6 ga shahada uku daga cikinsu jami’an tsaron kotun da kuma wani yaru da kuma wata mata yar...
3- Shan miyagun kwayoyi, jike-jiken magungunan karfin maza da sauran nau’o’in kayan karfin maza da ake amfani da su yau da kullum. Don haka, akwai bukatar a lura da hadarin da zuciya take shiga; bayan shan ire-iren wadannan magunguna na karfin maza. A nan, ana tursasa zuciya ne tare kuma da tunzura ta ta yi aiki tukuru fiye da ikon da take da shi na lafiyarta, wanda hakan ko shakka babu, zai haifar mata da gagarumar matsala. Haka zalika, bugun zuciya yana kara sauri tamkar gudun doki, jini kuma yana hauhawa fiye da lafiyayyen hawa yayin saduwa da iyali. Kazalika, bugun numfashi yana karuwa; domin musayar iska fiye da ikon lafiyar da huhu da jijiyoyin jinni suke da shi, sannan...
A tattaunawarsa da da LEADERSHIP, Shugaban Kungiyar NULGE na Kasa, Aliyu Haruna Kankara, ya zargi gwamnonin jihohi da shirya wani shiri da gangan na yi wa shari’a zagon kasa, wanda hakan ke kawo cikas ga ci gaban kasa da kuma jin dadin ma’aikatan kananan hukumomi. Kankara, ya kuma yi gargadin cewa; kungiyar za ta iya shiga yajin aiki a dukkanin fadin kasar, idan har gwamnatin tarayya ta gaza aiwatar da hukuncin da ya dace. Kankara ya danganta jinkirin da aka samu wajen aiwatar da ‘yancin cin gashin kan, ta bangaren harkokin kudi da dabarun siyasa da gwamnatocin jihohin ke yi. Har ila yau, ya yi zargin cewa; gwamnonin sun jajirce wajen nuna adawarsu ga ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomin...
Wannan yana cikin wani tsari na noma da aka kirkiro musamman don masu bukata ta musamman domin su dogara da kansu maimakon rokon hatsi ko neman taimako. Wannan yana cikin wani tsari na noma da aka kirkiro musamman don masu bukata ta musamman domin su dogara da kansu maimakon rokon hatsi ko neman taimako. Wakilinmu ya ziyarcj wata kebabbiyar gona dake cikin garin Kaduna, inda gungun wasu manoma da ke fama da lalurori daban-daban irin su makanta da gurguntaka da kurma, suka rungumi sabbin dabarun noma na zamani domin tallafawa rayuwarsu, musamman a wannan damina da aka shiga. Gonakin da wadanda makafi da guragu ne suke nomawa a duk shekara Sun bayyana cewa suna gudanar da nomansu ne ba tare...
A wani lamari makamancin haka da ya faru a Jihar Taraba, a watan Yuli, 2025, da misalin karfe 11:45 na rana, jami’an ‘yansanda sun amsa kiran da aka yi musu na satar mutane a hanyar Wukari, jim kadan a bayan jami’ar tarayya ta Wukari. Wata farar mota kirar Toyota bas dauke da fasinjoji 17 daga Enugu zuwa Yola, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi musu kwanton bauna. Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi gaggawar kai farmaki inda lamarin ya faru. Da ganin tawagar jami’an tsaro na zuwa, sai masu garkuwar suka yi bar wadanda abin ya shafa suka gudu cikin daji. An ceto dukkan fasinjoji 17 ba...
Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) za ta buga wasan ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Afirika yau da ƙasar Moroko a filin wasa na Olympique da ke birnin Rabat na ƙasar Moroko, za a buga wasan da misalin ƙarfe 9 na dare agogon Nijeriya. Wannan ne karo na biyu da ƙasashen biyu za su haɗu a tarihi, sun haɗu a karon farko a shekarar 2022 a wasan kusa da na ƙarshe na gasar kofin ƙasashen Afirika na mata, inda Moroko ta fitar da Nijeriya bayan bugun Fenarati, a wannan karon duka ƙasashen biyu na daga cikin waɗanda ake hasashen za su iya lashe kofin, duba da cewa babu kanwar lasa a cikinsu. Kano Pillars: Yaushe Kungiyoyin Kwallon...
Mujallar New York Times ta Amruka ta ce, harin da Iran ta kai wa sansanin sojan Amurka na Udaid, ya jazawa Amurkan asarar kudin da sun kai dala miliyan 111. Mujallar ta kuma ce; harin ya sa Amurka ta koyi darussan akan abinda zai iya faruwa idan har fada ya barke a tsakaninta da China ko Korea Ta Arewa.
A jiya Juma’a ne dai wanda ya isa birnin Beirut ya yi kira ga al’ummar kasar da su yi riko da hadin kan kasa da dukkanin bangarorinsu, sannan kuma su ci gaba da zage damtse wajen kalubalantar makiyar kasar Lebanon,musamman ‘yan sahayoniya. Goerge Ibrahim Abdullah wanda kuma ya gabatar da taron manema labaru a garinsu na “Qubyat’ ya kara da cewa; Kamar yadda mu ka kasance garkuwa mai bayar da kariya ga kasa, za mu ci gaba da zama haka’ sannan kuma ya kara da cewa: Saboda jinanen Shahidai kasar Lebanon za ta iya kalubalantar dukkanin hatsurran da take fuskanta.” Har ila yau, ya bayyana cewa;sojojin kasar Lebanon suna da mazajen da za su iya kare kasa,illa iyaka abinda ya...
A yayin da ‘yan sandan ke gudanar da bincike a yankin, rahotanni sun ce jami’an sun gano wata mata ‘yar Nijeriya a Coach A-2, Seat No. 27, tare da wani yaro da wata jakar balaguro kala-kala. Rahoton ya bayyana cewa bayan an yi mata tambayoyi, ta bayyana sunanta Doris daga Nijeriya kuma ta ce yaron da ke tare da ita, wanda ta bayyana sunansa Miracle, nata ne. RPF ta lura cewa “da aka yi mata tambayoyi a gaban shaidu masu zaman kansu, matar ta amsa cewa tana dauke da kayan maye.” Daga baya an kai ta zuwa gidan RPF a Panbel domin cikakken bincike. Rahoton ya lura cewa a cikin jakar balaguron, jami’an sun gano bakaken fakiti guda biyu da...
Mambobin kwamitin sun haɗa da: 1. Barr. Aminu Hussain – Shugaba 2. Barr. Hamza Haladu – Mamba 3. Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba 4. Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba 5. Manjo Janar Sani Muhammad (Rtd.) – Mamba 6. 6. Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba 7. Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya Yayin da yake sanar da kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna matuƙar damuwarsa game da zargin da ke kan jami’in gwamnati, tare da jaddada aniyarsa ta yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da duk wasu munanan ɗabi’un da ba su dace ba a fadin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....

Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincikar Kwamishinan Sufuri Kan Karɓar Belin Dilan Miyagun Kwayoyi A Kano
Mambobin kwamitin sun haɗa da: 1. Barr. Aminu Hussain – Shugaba 2. Barr. Hamza Haladu – Mamba 3. Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba 4. Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba 5. Manjo Janar Sani Muhammad (Rtd.) – Mamba 6. 6. Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba 7. Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya Yayin da yake sanar da kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna matuƙar damuwarsa game da zargin da ke kan jami’in gwamnati, tare da jaddada aniyarsa ta yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da duk wasu munanan ɗabi’un da ba su dace ba a fadin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Wani abin karin farin ciki shi ne, yadda masu rauwa da tsaki a fannin, suka jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan yadda ya zabo ya kuma nada Dantsoho, a matsayin shugaban NPA, inda akasarin su, suka yi ittifakin cewa, zabo, bai zama zabar Tumun dare ba, musamman duba da irin dimbin ci gaban da yake ci gaba da samar wa a fannin, a cikin shekara daya kacal. Gyaran Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar: Tun bayan da ya dare karagar shugabancin NPA Dantsho ya lashi Takon, inganta ayyukan Tashoshin, inda ka fara da tattara bayanan ayyukan da ya kamata ayi da kuma fara yin aikin gadan-gadan, inda aka ware dala bilyan daya, domin fara gyran Tashar Tincan Island, ta Apapa, ta...

Araqchi Ya Jaddada Cewa; Karfin Kariya Da Makamai Masu Linzamin Iran Ne Suka Tilastawa Makiya Neman Tsagaita Wuta
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin kariya da makamai masu linzami na Iran ne suka tilasta wa abokan gaba neman tsagaita wuta Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Karfin kariya da makamai masu linzami na Iran, sune suka tilasta wa makiya neman tsagaita wuta. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen kasar ta Iran Abbas Araqchi ya fitar a lokacin da ya ziyarci gidan tsohon kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci nak are tsaron sararin samaniyar Iran, Manjo Janar Amir Ali Hajizadeh, inda ya mika ta’aziyyarsa da taya shi murnar rabauta da shahada tare da nuna girmamawa ga daukakarsa. Araqchi ya yi ishara da irin kokarin...
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Siriya ta tattara bayanan mutuwar mutane 1,400 a loardin Sweida na Siriya Siriya, Faransa da Amurka sun sanar da wata taswirar hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a Siriya, bayan tattaunawar da ba a taba ganin irinta ba a birnin Paris na Faransa, wadda ta hada ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya na Siriya Asaad al-Sheibani, da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot da manzon Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack. Sanarwar ta hadin gwiwa da aka fitar bayan taron na bangarorin uku, ta tabbatar da goyon bayan shirin mika mulki ga gwamnatin kasar Siriya da karfafa hadin kan al’umma, musamman a birnin Sweida da ke arewa maso...
Ya zargi gwamnatin da cewa ba ta dauki kwararan matakai na kawo babban gyara a fannin wutar lantarki ba, sannan ta gaza wajen nuna wani hobbasa game da lamarin ballantana har kuma ta dauki matakin gaggawa a cikin shekaru biyu da ta kwashe tana mulki. “Mun wuce rabin lokacin wannan gwamnatin, kuma miliyoyin ‘yan Nijeriya na ci gaba da caji wayoyinsu a tashoshin caji na hannu, suna kashe dubban naira wajen sayen man fetur na janareta domin samun wutar lantarki. “Ina hasken wutan lantarkin da aka yi wa ‘yan Nijeriya al’kawari? Me ya faru da alkawarinku? Kuma har yaushe ‘yan Nijeriya za su ci gaba da zama cikin duhu?” Ya sake dawo wa da alkawarin Tinubu a lokacin yakin neman...

‘Yan Jarida Da Suka yi Shahada A Gaza Sun Kai 232, Yayin Da Wadanda Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Yunwa Suka Kai 122
‘Yan jarida akalla 232 suka yi shahada sannan wasu 122 sun rasa rayukansu sabaoda masifar yunwa a yankin Zirin Gaza! Yakin kisan kare dangi da ake yi a zirin Gaza yana ci gaba da lakume rayukan Falasdinawa da dama a kowace rana, manya da kanana…ta hanyar jefa bama-bamai, kisa, killace yankin da kakaba masifar yunwa. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu daruruwa, ciki har da masu neman agaji, sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar al-Rimal da gidaje da sansanonin ‘yan gudun hijira a yankunan al-Amal, al-Tuffah, da al-Nasr, dake gabashi, arewacin Gaza. Hakazalika an sha kai...
Shugaban kasar Ukraine ya nuna sha’awar ganawa da shugaban Rasha kan neman hanyar warware rikicin da kasashen biyu ke fama da shi Ana ci gaba da yakin Ukraine musamman ta hanyar kai hare-hare da jiragen sama marasa matuka coiki. Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuka ciki guda 105 na Ukraine da aka harba zuwa yankuna tara, a tekun Azov, da kuma cikin kasar Rasha a daren jiya. Shugaban kasar Ukraine Zelenskyy ya ce: Kasarsa tana da kudade don sarrafa tsarin makamai masu linzami na Patriot guda uku kuma yana neman samar da karin kudade don sarrafa wasu bakwai na daban, gami da taimakon abokan huldarsa na kasashen Turai. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya...
Mai magana da yawun jam’iyyar na wucin gadi ya ki janye ikirarinsa na cewa ADC na fuskantar manyan matsaloli a bangaren shari’a. “Muna da tabbaci kan doka a kowane mataki da muka dauka. Mun tabbatar mun rufe duk wata baraka da jam’iyya mai mulki za ta iya amfani da ita a kanmu,” ya kara da cewa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ikazoboh, ya ce ya jin daɗin samun wannan dama, kuma zai yi aiki tuƙuru don rage farashi da kuma amfani da makamashi mai tsafta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau Juma’a, 25 ga Yulin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karbi takardun nadi daga sabbin jakadun kasashe 16 da suka hada da Angola, da Benin, da Sudan ta Kudu, da Amurka, da Iran, da Chile da sauransu a Babban Zauren taruwar Jama’a dake nan birnin Beijing. Shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin tana darajanta dangantakar abota da al’ummomin duniya, kuma tana fatan kara hadin gwiwa a mabambantan bangarori, da kowace kasa bisa mutunta juna, da daidaito da samun moriyar juna. Ya ce Sin za ta ci gaba da fadada budadden tsarin tattalin arzikinta mai zurfi, tare da ba da damar yin amfani da babbar kasuwarta, ta yadda sabon ci gaban kasar zai zama dama ga kasashen duniya, kuma...
Wakilin dindindin na kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, Fu Cong, ya yi magana a wani taro na bude kofar Kwamitin Sulhu na MDD game da hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwar kasashen Musulmi (OIC), inda ya karyata batun da wakiliyar Amurka ta yi game da yankin Xinjiang na Sin. Fu Cong ya ce, Sin ta nuna adawa kwarai tare da kin amincewa da zargi mara tushe balle makama da wakiliyar Amurka ta yi game da Xinjiang. A halin yanzu jihar Xinjiang na cikin kwanciyar hankali, tana samun ci gaban tattalin arziki, al’umma suna rayuwa cikin kwanciyar hankali, kuma suna cikin mafi kyawun yanayin ci gaba a tarihi. Amma da gangan Amurka ke kokarin yayata batun Xinjiang da...
JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar Rasha mai suna Vostochiny Cosmodrome don isar da tauraron zawa inda take so a sararin samaniya, a yau Jumma’a 25 ga watan Yulin shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa kombon kasar Rasha a wannan cillawar ta isar da taurarin dan’adam da dama zuwa sararin samaniya. Banda tauraron dan’adam na kasar Iran ita ma kasar Rasha tana da taurarin dana dam guda biyu a cikin kumbon wato Ionosfera-M3 da M4, sannan da wasu 18 na wasu kasashe. Kafin haka dai wannan kumbon na kasar Rasha ya taba aika...
Namadi ya bayyana fatan cewa ayyukan hukumar ta Hisbah za su kawo kyakkyawan tsarin zamantakewa da tarbiyya a jihar. Ya kuma bukaci jami’an Hisba da su gudanar da ayyukansu cikin tsoron Allah, adalci, da sadaukarwa. Gwamnan ya kuma yaba wa ‘yan kwamitin kafa hukumar Hisbah bisa jajircewa, kwazon da suka yi, da sadaukarwa wajen gudanar da aikin da aka dora musu. “Kokarin da suka yi ya taka rawar gani wajen ganin an aiwatar da kudurin,” in ji shi. Ya kara da cewa, “Tare da sanya hannu kan wannan doka, a yanzu hukumar Hisbah ta samu cikakken ikon gudanar da ayyukanta a fadin Jihar Jigawa bisa aikinta na inganta kyawawan halaye, tabbatar da adalci ga al’umma, da kyautata rayuwar al’umma. “Kafa...
Kamfanin kera manyan motocin dakon kaya na kasar Sin Sinotruk ya kaddamar da motocinsa kirar H2 mai dakon kaya marasa nauyi da ta H3 ta dakon kaya masu matsakaicin nauyi a kasar Kenya, tare da kamfanin CFAO Mobility a matsayin mai rarraba motocin a cikin gida. Babban manajan kamfanin CFAO Mobility na Sinotruk Sarfraz Premji, ya shaida wa manema labarai a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, an kera samfuran motocin ne ne don kawo sauyi ga masana’antar sufuri saboda suna iya daukar kaya masu nauyi, sannan an sa musu manyan tankunan mai, inda hakan zai rage bukatar yawan zuwa shan mai da kuma ba da damar daukar dogon lokaci ana tafiya, kana wannan zai rage yawan kudin da ake...
Kwamitin ya nemi a mayar da sama da Naira miliyan 124, kusan dala 795,000 zuwa asusun gwamnatin tarayya, an kuma bayar da karin wasu kudade da suka hada da Naira miliyan 31.7 da dala 155,923.00, a matsayin wadanda aka kashe ba bisa ka’ida ba. An umarci ma’aikatar da ta kwato Naira miliyan 49.4 da aka biya, domin yin gyaran ba tare da bin ka’idojin sayen kayayyakin ba. Kazalika, an raba Naira miliyan 9.2 ga jami’an ofishin jakadancin, ba tare da cikakkiyar shaida ba. Haka nan kuma, an binciki bankin noma; kan basussuka kimanin Naira biliyan 75.6. Kwamitin ya umarci hukumar da ta buga jerin sunayen wadanda ake bi bashi a akalla a jaridu guda uku na wannan kasa tare da...
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023, ya karɓi ’yan APC zuwa jam’iyyar NNPP a Jihar Kano. Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta shafinsa na X, inda ya ce waɗanda suka sauya sheƙar ’yan jam’iyyar APC ne. An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo An kashe mata da yara a sabon harin Filato “Jiya rana ce mai muhimmanci,” in ji shi. “Na karɓi dubban mutane da suka bar jam’iyyar APC suka dawo NNPP.” Ya ce taron ya gudana ne a gidansa da ke Kano, inda ya yi wa sabbin mambobin maraba da kuma alƙawarin adalci da haɗin kai a cikin jam’iyyar. An wallafa hotunan taron a shafukan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sai dai Sanatoci sun yi watsi da bayanin, inda suka zargi Ojulari da yin watsi da Majalisar. Kwamitin yana binciken tambayoyin tantancewa daga shekarar 2017 zuwa 2023, wanda ya nuna sabanin da ya kai Naira tiriliyan 210, ciki har da bashin da ba a tabbatar da shi ba na Naira tiriliyan 103. ‘Yan majalisar sun firgita cewa Naira tiriliyan 3 zuwa 5 ne kawai aka rubuta a cikin asusun ribar da kamfanin ya samu a cikin shekaru shida. “Wannan gayyatar ba tilas bace,” in ji Wadada. Ya kara da cewa kwamitin ba yana zargin hukumar ta NNPC da laifin sata bane amma ya jaddada cewa girman sabanin ya bukaci a yi karin haske kai tsaye. Ya bayyana rashin bayyanar Ojulari...
“Sauran su ne Lawan Haruna, Opurum Patrick, Agbo James da Georgewill Onwubiko da sauransu. “Shugaban PSC ya ce su tuna cewa su abokai ne ga kowa, kuma ya kamata a kowane lokaci su yi daidai da abin da ‘yan Nijeriya ke bukata. Ya kuma ba su tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da yin iya kokarinta don ganin an inganta yanayin aikinsu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce tituna a Arewa sun lalace kuma gwamnati tana nuna rashin kulawa ga yankin. “Jiya da jirgi zan biyo na taho, amma aka ɗage jirgi daga ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare, sai na taho ta mota. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano abin takaici ne. Wannan aikin titi tun lokacin farkon hawa gwamnatin APC ake yinsa.” Kwankwaso ya kara da cewa ana gudanar da manyan ayyuka a Kudu cikin hanzari, amma an bar ayyuka masu mahimmanci a Arewa babu kulawa. “Muna jin ana gina titi daga Kudu zuwa Gabas. Muna maraba da ci gaba a ko’ina a Nijeriya. Amma gwamnati tana ɗaukar duk arzikin ƙasa ta zuba a ɓangare ɗaya kaɗai, ba ta yin aiki da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Babu shakka Iran za ta ci gaba da inganta sinadarn Uranium Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana a jiya Alhamis dangane da tattaunawar da Iran za ta yi da kungiyar kasashen Turai da za a yi a yau Juma’a a birnin Istanbul na Turkiyya cewa; Za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a cikin kasar Iran, kuma kasar ba za ta yi watsi da wannan hakkin na al’ummar Iran ba. A cikin bayanin da ya yi a gefen ziyarar da ya kai ga iyalan shahidan Laftanar Janar Baqiri, Araqchi ya kara da cewa; Ko da yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da shirinta...