Sojojin Yemen Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kataparen Jirgin Ruwan Yaki Mai Daukar Jirage Na kasar Amurka
Published: 2nd, April 2025 GMT
Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin cruise a hare-haren da suka kai kan kataparen jirgin yaki mai daukarjiragen saman yaki na kasar Amurka da suke cikin tekun maliya a karo na ukku a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar ta Yemen na fada a jiya Talata, kan cewa sun yi amfani da makamai masu linzami da kuma jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a wadan nan hare-hare kan USS Harry S.
Truman kuma saun sami bararsu kamar yadda aka tsara.
Labarun ya kara da cewa yakin yana ci gaba tsakanin bangarorin biyu. Kuma wadan nan hare hare sun zo ne saboda maida martanin hare-haren da jiragen yakin Amurka suke ci gaba da kaiwa a kan kasar ta Yemen.
Majiyar ta kara da cewa hare-hare da makamai masi linzami kan HKI ma zai ci gaba kamar yadda gwamnatin kasar ta tsara.
Gwamnatin Amurka dai ta shiga yaki da sojojin Yemen ne saboda kare HKI a kan kissan kiyashin da takewa mutanen Gaza, sannan da kuma hana shigowar abinci da bukatun mutanen yankin tun fiye da wata guda da ya gabata. Har’ila yau sojojin Yemen sun hana jiragen ruwa kasuwanci na HKI ko wadanda suke zuwa can wucewa ta tekun.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jaridar The Guardian Mafi Yawan ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Ne A Gidan Yarin Kasar Girka
Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan
Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari.
Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi.
Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka zarce ‘yan ciranin gargajiya na wasu kasashe kamar ‘yan Siriya da Falasdinawa.