’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista
Published: 18th, April 2025 GMT
Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki.
Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB) da nufin samar da wutar lantarki ga ‘yan Afirka miliyan 300 nan da shekarar 2030.
“Ƙa’idar ta tsara kyawawan manufofi don haɓaka hanyoyin samar da wutar lantarki, ƙara haɓaka makamashi da inganta hanyoyin magance matsalolin dafa abinci mai tsabta ga miliyoyin ‘yan Najeriya – wato Mission 300, kuma muna samun ci gaba mai kyau a kan wannan,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Ina mai farin cikin gaya muku cewa cikin ‘yan Afirka miliyan 300 da Bankin Duniya da AfDB ke son cimmawa, Najeriya na kan hanyar da za ta biya ƙasa da kashi 25 cikin 100, wanda ke nufin kusan ‘yan Najeriya miliyan 75. Da muka gabatar da yarjejeniyarmu, sun amince da mu.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya Adedayo Adelabu Wutar Lantarki wutar lantarki yan Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Sarkakiyar Dake Gaban Hadakar ADC — Atiku Ko Peter Obi
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
‘Yan Najeriya suna ci gaba da tafka muhawara a kan wanda jamiyyar hadaka ta ADC zata tsayar takarar Shugaban Kasa a zaben 2027.
Yayin da wasu suke ganin Atiku Abubakar yana da dimbin magoya baya, wasu kuwa gani suke yi shi ma Peter Obi ba kanwar lasa bane.
Ko me zai faru idan daya daga cikin su ya samu tikitin tsayawa takara a 2027?
NAJERIYA A YAU: Mene ne tasirin naɗin Mataimaka na Musamman a rayuwar jama’a? DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke HaifarwaShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wannan lamari.
Domin sauke shirin, latsa nan