Farfesa Bello ya ce gwamnatin jihar ta dage wajen bai wa ’yan mata masu tasowa ingantaccen ilimi da tallafa musu domin su zama masu amfani ga iyalansu da al’ummominsu.

 

Ya bayyana godiyarsa matuka bisa gudunmuwar da Bankin Duniya ke bayarwa, yana bayyana aikin AGILE a matsayin wani gagarumin sauyi wajen canja ra’ayin al’umma game da ilimin ’ya’ya mata.

 

“Kalma ba za ta isa ta bayyana yadda muke jin wannan taimako daga Bankin Duniya ba, musamman game da aikin AGILE. Kungiyar aikin a jihar, karkashin jagorancin Maryam Sani Dangaji, ta yi kokari sosai wajen fadakar da iyaye cewa AGILE yana kokarin taimaka wa yarinya ta gane cikakken kwarewarta,” in ji shi.

 

Farfesa Bello ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kuma kaddamar da wani sabon shiri mai suna “Reaching Out to Out-of-School Children” domin rage adadin yaran da ke waje da makaranta a fadin jihar.

 

Haka kuma ya bayyana cewa gwamnati ta ware dala miliyan goma sha shida ($16m) domin gina makaranta a ko wace tazarar kilomita daya a yankunan karkara domin karfafa shiga makaranta.

 

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Yankin na Bankin Duniya, Ousmane Diagana, ya jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna kan yadda take jajircewa wajen ganin aikin AGILE ya samu nasara.

 

Diagana ya jaddada muhimmancin ilmantar da ’yan mata, yana rokon dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da jajircewa duk da kalubale.

“Idan yarinya ta samu ilimi, gaba dayan al’umma ke amfana,” in ji shi, yana mai jaddada bukatar kawar da duk wani cikas da zai hana ‘yan mata cimma burinsu.

 

Aikin AGILE, wanda Bankin Duniya ke tallafawa, ya zuwa yanzu ya gyara makarantu 665, ya horas da malamai, tare da wayar da kan ‘yan mata game da sauyin yanayi da daukar matakin kare muhalli.

 

Da take zantawa da Radio Nigeria Kaduna, Daraktar Yanki da ke kula da kasashen Yammaci da Gabashin Afirka kan harkokin Ilimi, Lafiya, Kariya ta Zamani da Jinsin Mata, Trina Haque, ta ce Bankin Duniya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa dukkan ’yan mata masu tasowa sun samu ingantaccen ilimi karkashin aikin AGILE.

Ta kara da cewa Bankin Duniya na aiki kafada da kafada da gwamnonin jihohi da kwamishinonin ilimi domin cimma burin aikin.

 

Ita ma, Jami’ar Kula da Bin Diddigi na aikin AGILE a Kaduna, Yabai Ayis, ta bayyana nasarorin da aka samu a cikin shekaru hudu da suka gabata.

 

“AGILE ya gyara makarantu 550 tare da sake farfado da wasu makarantu 115, wanda ya kai jimillar makarantu 665 da suka amfana daga gyare-gyare daban-daban. Haka kuma, an horas da malamai domin inganta koyarwa a duk makarantu na gwamnati a Jihar Kaduna,” in ji Ayis.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da aikin, Success Eliminian, ta yaba wa AGILE bisa sauya dabi’u da al’adun al’umma tare da bunkasa ilimin ’yan mata.

“Aikin AGILE yana sauya tunanin al’umma da al’adunmu. Ya shafe mu ta hanyar ba mu ilmi da da yadda zamu kulada kanmu akan kowane irin kalubale,” In ji ta.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Ya ya AGILE Gwamnatin Duniya Hanyar Rayuwar Sauya Bankin Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC

Karin bayani na tafe

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest
  • Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudinta a Gaban Majalisa
  • Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa
  • Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro
  • Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
  • Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya
  • Ministan Makamashi: Iran Tana Da Sanayya Ta Ilimi Na Samar Da Hadari Domin Yin Ruwan Sama
  • Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC
  • Yara masara zuwa makaranta barazana ne ga kasa — Shettima
  • MِِِِDD:  Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya