2025-05-12@21:27:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 414

«kayan yaƙi»:

    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto suka yi musayar taya juna murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Inda shugaba Xi ya ce, yana dora matukar muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Indonesia, kuma a shirye yake ya yi...
    Al’ummar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yakin da ake yi a Gaza A karkashin taken “An rusa Gaza” kuma goyon bayan al’umma ga Falasdinawa abu ne da ya zama wajibi, ba zabi ba, mazauna birnin Nouakchott fadar mulkin kasar Mauritaniya sun gudanar da zanga-zanga domin jaddada bukatar musulmi a ko’ina a duniya...
    Sakamakon gazawar shugabanci, bayar da tallafi na neman zama wani bangare a tarihin dimokoradiyyar Nijeriya, inda gwamnatocin jihohi da ’yan majalisu da sauran ’yan siyasa suke amfani da shi wajen cusa wa ’yan kasa ra’ayinsu na siyasa. A duk lokacin da al’umma suka koka a kan wani mummunann yanayi da ya hada da matsin tattalin...
    Wata kotu a Amurka ta umurci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta ƙasar (FBI) da ta fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken badaƙalar miyagun ƙwayoyi da gwamnatin ƙasar ta yi a shekarun 1990. Jaridar Premium Times ta ruwaito Alƙalin kotun, Beryl Howell wanda ya ba da umarnin...
    Wannan gargadi da Sin da EU suka gabatar ga manyan kamfanonin shirya fina-finai da na fasaha na Amurka, na nuna cewa, gangancin da gwamnatin Amurka ke yi na kakaba haraji barkatai, zai ci gaba da illata kashin bayan fannoninta na cinikayya.   Hadin gwiwa tsakanin Sin da Sifaniya, ya kara bayyana yadda Sin ke fatan...
    Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar 18 ga watan Maris, yayin da al’amuran jin kai ke kara ta’azzara a Gaza. Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun bayan da Isra’ila...
    A Gabon, yau Asabar ne Jama’ar kasar suka kada kuri’a  domin zaben shugaban kasar, a karon farko bayan kifar da iyalan gidan Bongo daga mulkin kasar. Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya kifar da mulkin Ali Bongo na daga cikin ‘yan takarar dake fafatawa a zaben daga cikin ‘yan takara guda takwas. Sauran yan takarar...
      A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin...
    Daga karshe ta ce da farko ta samu turjiya daga wajen wasu mutane a kan kudurinta na fara harkar fim amma kuma ta yi biris dasu ta fara, amma kuma yanzu wadanda a baya ke hanata shiga fim su ne yanzu ke yi mata murnar samun nasara hakan ya matukar bata mamaki, duba da cewar...
    Jami’an tsaro sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Gwaska Ɗan Ƙarami da wasu mayaƙa 100 a Jihar Katsina. Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dokta Nasir Mu’azu ya bayyana matakin a matsayin wata gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga ake yi a jihar. An kama mutum 8 kan...
    Ministan harkokin wajen kasar Saudiya ya bayyana cewa shigo da kayakin agaji zuwa cikin zirin Gaza bai da wata dangantka da tsagaita bude wuta. Shafin yanar Gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ya nakalto Yerima Faisal bin Farhan yana fadar haka a jiya Jumma’a.. Ya kuma kara da cewa dole ne kasashen duniya...
    Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadaccen Abinci, Sanata Abubakar Kayri ne ya bayyana a haka, a cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar. “Mun samar da tsarin samar da wadataccen abinci a kasar nan, wanda kowanne dan kasar zai amfana da shi”, in ji Kyari. Daga cikin manyan abubuwan da suka hada da bashin...
    ’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin ya ɗirka wa ’yar cikinsa mai shekara 17 ciki a yankin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjiwa a Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya ce an kama mutumin mai shekaru 50 ne bayan samun ƙara cewa ya yi wa ’yar tasa fyaɗe fiye da...
    A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje. Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon...
    Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kasance mai fafutukar tabbatar da hadin kan ‘yan adawa, yana mai jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen kayar da Tinubu a zaben 2027. A ranar 8 ga watan Maris ne ya bayyana kokarinsa na hada kan ‘yan adawa da kafa kawancen korar jam’iyyar APC. Bayan sauya shekar El-Rufa’i daga jam’iyyar...
    Idan masu ajiya a Bnkin suka ajiye akalla Naira 10,000 a Asusun ajiya na Bankin ko kuma a cikin Lalitar ajiyarsu ta Bankin a kalla a cikin kwanuka 30, hakan ya nuna cewa, sun tsallake zamowa Zakarun samun damar lashe kyaututuka a wata daya, inda kuma za su shiga gasar zagaye ta karashe. Kazalika, a...
    Sojojin HKI suna ci gaba da yin kiyashi a sassa mabanbata na Gaza, da a bayan nan su ka yi wa mutane 30 kisan kiyashi a unguwar Shuja’iyya dake birnin Gaza.  Majiyar asibitin Falasdinawa ta ambaci cewa; Harin da sojojin HKI su ka kai da manyan bindigogi sun yi sanadiyyar shahadar mutane 17 a unguwar...
    Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani...
    Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani  kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke...
      Shugaban na kasar Sin ya kuma yi fatan alheri ga kasashe da jama’ar yankin na Latin Amurka da Caribbean wajen samun manyan nasarori a fannin ci gaba, da farfado da tattalin arziki, ta yadda za su ba da gagarumar gudummawa ga hadin kai da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa a duniya....
    Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a...
    Gwamnatin kasar China ta bada sanarwan kara kodaden fito kan kayakin Amurka wadanda suke shigowa kasa har na kasha 80% sannan a shirye take ta ci gaba da yakin kasuwanci da gwamnatin shugaba Trump har zuwa karshe. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’an gwamnatin kasar China na fadar haka a yau...
    Ta kuma ce har yanzu ƙasashe sama da 70 daga sassa daban-daban na duniya sun tuntuɓi Amurka domin a yi tattaunawa kan yadda sabbin harajin ke shafar kasuwanci a duniya. Mene ne Ma’anar Wannan Haraji? Wannan haraji na nufin idan ana shiga da kaya daga China zuwa Amurka, za a ƙara musu kuɗi sosai kafin...
    Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci dubu 16 sun fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata zuwa wasu ƙasashen duniya don ci gaba da aiki cikin ingantaccen yanayi. Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afrika da ya gudana...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da yiwuwar tattaunawa da Iran kai tsaye, inda ya yi karin haske kan matsayar Tehran, kamar yadda jaridar Washington Post ta kawo. Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yi tir da gwamnatin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, saboda dirar mikiyan da ta yi kan Falasdinawa a yankin wadanda suke zanga-zangar beman HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da ta yi a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran...
    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani shahararren mai sana’ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda yin likin da takardun Naira a lokacin bikin aurensa. Mai Shari’a S.M. Shu’aibu ya yanke wa Huseini Amuscap hukuncin ne bayan...
    Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas. Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu. Hundeyin ya...
    A safiyar jiya litinin an kashe wani dan jarida Bafalasdine da wani matashi tare da raunata wasu da dama a lokacin da jirgin Isra’ila ya kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida a kusa da rukunin likitocin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza. Wakilin Al Mayadeen ya ruwaito cewa dan jarida Hilmi...
    A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo...
    Ana fargabar cewa kimanin ’yan sa-kai 13 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka kai Jihar Kebbi a jiya Lahadi. Lamarin ya faru ne a yankin Morai na Ƙaramar Hukumar Augie — ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani....
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta hanyar yin watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu. Esmail Baghai ya bayyana haka ne a cikin wani sako a asusunsa na X, bayan ziyarar aiki da Netanyahu ya kai kasar...
    Ƙungiyar Take It Back ta ce zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba. Wannan dai na zuwa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shirin bautar ƙasa wanda aka kafa tun a shekarar 1973, an ƙirƙire shi da nufin haɗa kan matasa daga kowane lungu da saƙo na ƙasar nan, domin fahimtar juna da kawar da wariyar yanki da ƙabilanci. Amma a yau, bayan shekaru fiye da arba’in da biyar da fara...
    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Southampton ba za ta buga gasar Firimiya Lig na badi ba, bayan da su ka koma gasar yan dagaji ta kasar Ingila, Southampton ta yi rashin nasara a hannun Tottenham Hotspur wanda kuma shi ne ya yi sanadiyar da Southampton ta koma gasar Championship ta kasar Ingila. Hakan ya sa ta...
    Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wasu ƙauyuka na Ƙaramar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Ruwi, Manguna, Daffo, Josho da Hurti. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya...
    Jirgin da ke ɗauke da mutane sama da 200 daga Bali a ƙasar Indonesia zuwa Ostireliya, ya yi juyawar dole bayan wani fasinja ya yi yunƙurin buɗe ƙofarsa yayin da jirgin kamfanin Jetstar ke shawagi a tekun Indiya. “Mun samu wani jirgin sama ya koma Denpasar (filin jirgin sama na Bali) a daren Talata bayan...
    Jami’an tsaro sun jiran kayan ado na ’yan kunnayen zinare su wuce ta na’urar binciken fasinjan jirgin sama kafin a gano kayan da aka sace a hukumance. An kama wani mutum mai shekara 32, mai suna Jaythan Lawrence Glider bisa zargin satar ’yan kunne biyu na zinare na sama da Dala Amurka 769,000 kwatankwacin Naira...
    Hotunan faifan bidiyo da ke fallasa kisan da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi wa likitoci 15 a Rafah, ya tilastawa “Isra’ila” ja da baya kan labarin da ta kirkiro, tana mai cewa karyar da ta yi “ba da gangan ba ce”. An kara da’awar kuma daga baya an karyata ta ta hanyar shaidun bidiyo,...
    Yana kuma havaka sabon nau’in alakar kasa da kasa, ta hanyar kaddamar da shirin Raya Duniya, da shirin Tsaron Duniya, da shirin Wayewar Kai na Duniya dake aiki a matsayin ginshikan wannan tunanni. Haka ma hadin gwiwa mai inganci karkashin tsarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya mai amfani wajen aiwatar da wannan hangen nesa,...
    Yayin ziyararsa kasar Sin kwanan nan, babban mashawarcin gwammatin wucin-gadi ta kasar Bangladesh, Muhammad Yunus, ya tattauna da wakiliyar CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, inda a cewarsa, a matsayin kasa ta farko a kudancin nahiyar Asiya, wadda ta rattaba hannu tare da kasar Sin kan takardar bayanin hadin-gwiwa game...
    Direba da kwandastan motar bas sun tsere domin tsira da rayukansu, inda suka bar fasinjoji a ciki yayin da wata motar bas ta BRT ta kama wuta a Maryland da ke Jihar Legas da safiyar ranar Asabar. Majiyar Channels TV da ke wajen da lamarin ya faru, ta ce motar ta taso ne daga yankin...
    daukar Ciki: Wannan na nuna yadda wanda za a lura da ‘ya’yan da aka haifa. 3- A Ina Ya Fi Dacewa A Sayi Sa? Za a iya sayen Bijimin Sa, a wurare daban-daban da ake bukata, amma ana so kafin a saya, a yi taka-tsan-tsan. Ana kuma so a tunbubi kwararru a fannin ko kuma...
    Tsohon Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano kuma tsohon Mashawarci na Musamman ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, CP Muhammad Wakili (ritaya), ya jaddada cewa dole ne ’yan sanda su yi amfani da ikon da suke da shi cikin gaskiya da adalci, don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Da yake jawabi a wani...
    A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Nijeriya ta ce ana cigaba da farautar  ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Bello Turji wanda sojojin ƙasar suka daɗe suna nema ya kusa komawa ga mahalicci. Rundunar ta bayyana cewa kuma kwanakinsa sun kusa ƙarewa. Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta miƙa Janar Tsiga da wasu ga NSA Gobara ta...
    Shugaban kasar Burundi ya yi gargadin cewa Rwanda na da shirin kai wa kasarsa hari, bayan da sojojin Burundi suka taimakawa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) a yakin da take yi da ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda. Shugaban kasar ta Burundi Evariste Ndayishimiye ya bayyana cewa, ya samu “sahihan bayanan sirri” da...
    Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka...
    Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka...
    Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga. An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon Shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025. Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato...